Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ
wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah
Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa
gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta,
kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã
a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr.
Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda
Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã
su da wani mataimaki.
Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da
shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma
zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna.
(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku,
kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu
bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin
da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga
Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a
cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah
na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali
gare Shi, ga hanyarSa.
Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu
kuma bã dõmin wata kalma tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali
ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa
Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.
Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma
kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar
na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne
Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã
gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu,
kuma zuwa gare Shi makõma take."
Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa,
hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã
da wata azãba mai tsanani.
Waɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa
waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita
gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa,sunã a cikin
ɓata Mai nĩsa.
Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma
wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli
kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira.
Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game
da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba,
da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai
raɗaɗi.
Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi
abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata
ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin
Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma.
Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni
kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa,
fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã
Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya.
Kõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a
kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da
kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata.
Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai,
kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba
mai tsanani.
Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a
cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne
Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani.
Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan
bãyan tẽkun,Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai
gõdiya.
Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma
abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci,kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda
suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.
Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma
al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã
ciyarwa.
Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya
kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai.
lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã
ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai
raɗaɗi.
Kuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga
azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga
kõmãwa?"
Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã
hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne,
mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar
¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya.
Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu,
baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra.
To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da
ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum
wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta
sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin
kãfirci ne.
Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã
bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda
Yake so.
Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ
daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da
izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.
Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga
gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni,
kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da
wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã
shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya.