« Prev

44. Surah Ad-Dukhân سورة الدّخان

Next »



First Ayah   1   الأية الأولي
بِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
حم
Hausa
 
Ḥ. M̃.

Ayah   44:2   الأية
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ
Hausa
 
Ină rantsuwa da Littăfi Mabayyani.

Ayah   44:3   الأية
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
Hausa
 
Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Măsu yin gargaɗi.

Ayah   44:4   الأية
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ
Hausa
 
A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kőwane umurui bayyananne.

Ayah   44:5   الأية
أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
Hausa
 
Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMăsu aikăwă.

Ayah   44:6   الأية
رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Hausa
 
Sabőda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Măsani.

Ayah   44:7   الأية
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Hausa
 
(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu, idan kun kasance măsu yaƙĩni (za ku găne haka).

Ayah   44:8   الأية
لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ
Hausa
 
Babu abin bautăwa făce Shi. Yana răyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

Ayah   44:9   الأية
بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ
Hausa
 
A'a sũ, sună wăsă a cikin shakka.

Ayah   44:10   الأية
فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
Sabőda haka, ka dakata rănar da sama ză tă zo da hayăƙi bayyananne.

Ayah   44:11   الأية
يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
 
Yană rufe mutăne. Wannan wata azăba ce mai raɗaɗi.

Ayah   44:12   الأية
رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ
Hausa
 
Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azăba. Lalle Mũ, măsu ĩmăni ne.

Ayah   44:13   الأية
أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ
Hausa
 
Ină tunăwa take a gare su, alhăli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanăwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azăbar, ba su karɓa ba)?

Ayah   44:14   الأية
ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ
Hausa
 
Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayăwa ne, mahaukaci."

Ayah   44:15   الأية
إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ
Hausa
 
Lalle Mũ, Măsu kuranyẽwar azăba ne, a ɗan lőkaci kaɗan, lalle kũ, măsu kőmăwa ne (ga laifin).

Ayah   44:16   الأية
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
Hausa
 
Rănar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ măsu azăbar rămuwa ne.

Ayah   44:17   الأية
وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ
Hausa
 
Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutănen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

Ayah   44:18   الأية
أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa
 
(Mazon ya ce): "Ku kăwo mini (ĩmăninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

Ayah   44:19   الأية
وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
Hausa
 
"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

Ayah   44:20   الأية
وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ
Hausa
 
"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dőmin kada ku jẽfe ni."

Ayah   44:21   الأية
وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ
Hausa
 
"Kuma idan ba ku yi ĩmăni sabőda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

Ayah   44:22   الأية
فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ
Hausa
 
Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutănene măsu laifi.

Ayah   44:23   الأية
فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Hausa
 
(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dőmin a kăma ku.)"

Ayah   44:24   الأية
وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ
Hausa
 
"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

Ayah   44:25   الأية
كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Hausa
 
Da yawa suka bar gőnaki da marẽmari.

Ayah   44:26   الأية
وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
Hausa
 
Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

Ayah   44:27   الأية
وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ
Hausa
 
Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sună măsu hutu.

Ayah   44:28   الأية
كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ
Hausa
 
Kamar haka! Kuma Muka gădar da ita ga waɗansu mutăne na dabam.

Ayah   44:29   الأية
فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ
Hausa
 
Sa'an nan samă da ƙasă ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

Ayah   44:30   الأية
وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ
Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isră'ĩla daga, azăba mai wulăkantăwa.

Ayah   44:31   الأية
مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ
Hausa
 
Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin măsu ɓarna.

Ayah   44:32   الأية
وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ
Hausa
 
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zăɓe su sabőda wani ilmi (na Taurata) a kan mutăne.

Ayah   44:33   الأية
وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌ
Hausa
 
Kuma Muka bă su, daga ăyőyin mu'ujizőji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

Ayah   44:34   الأية
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ
Hausa
 
Lalle waɗannan mutăne , haƙĩka, sună cẽwa,

Ayah   44:35   الأية
إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ
Hausa
 
"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tăyarwa ba."

Ayah   44:36   الأية
فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
Hausa
 
"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance măsu gaskiya."

Ayah   44:37   الأية
أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ
Hausa
 
shin, sũ ne mafĩfĩta kő kuwa mutănen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabăninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance măsu laifi.

Ayah   44:38   الأية
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ
Hausa
 
Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu ba, alhăli kuwa Mună măsu wăsă.

Ayah   44:39   الأية
مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Hausa
 
Ba Mu halitta su ba făce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

Ayah   44:40   الأية
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa
 
Lalle rănar rarrabẽwa, ita ce lőkacin wa'adinsu gabă ɗaya.

Ayah   44:41   الأية
يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
Hausa
 
Rănar da wani zumu bă ya amfănin wani zumu da kőme kuma ba su zama ană taimakon su ba.

Ayah   44:42   الأية
إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
Hausa
 
făce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwăyi, Mai jin ƙai.

Ayah   44:43   الأية
إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ
Hausa
 
Lalle ităciyar zaƙƙũm (ɗanyen wută),

Ayah   44:44   الأية
طَعَامُ الْأَثِيمِ
Hausa
 
Ita ce abincin mai laifi.

Ayah   44:45   الأية
كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ
Hausa
 
Kamar narkakken kwalta yană tafasa a cikin cikunna.

Ayah   44:46   الأية
كَغَلْيِ الْحَمِيمِ
Hausa
 
Kamar tafasar ruwan zăfi.

Ayah   44:47   الأية
خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ
Hausa
 
(A cẽ wa mală'ikun wută), "Ku kămă shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

Ayah   44:48   الأية
ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ
Hausa
 
"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azăbar ruwan zăfi."

Ayah   44:49   الأية
ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ
Hausa
 
(A ce masă), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwăyi mai girma!"

Ayah   44:50   الأية
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ
Hausa
 
"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kună shakka game da shi."

Ayah   44:51   الأية
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ
Hausa
 
Lalle măsu taƙawa sună cikin matsayi amintacce.

Ayah   44:52   الأية
فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
Hausa
 
A cikin gidăjen Aljanna da marẽmari.

Ayah   44:53   الأية
يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ
Hausa
 
Sună tufanta daga tufăfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sună măsu zaman fuskantar jũna.

Ayah   44:54   الأية
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ
Hausa
 
Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mătă măsu kyaun idănu, măsu girmansu.

Ayah   44:55   الأية
يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ
Hausa
 
Sună kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan ităcen marmari, sună amintattu (daga dukan abin tsőro).

Ayah   44:56   الأية
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
Hausa
 
Bă su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, făce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azăbar Jahĩm.

Ayah   44:57   الأية
فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Hausa
 
Sabőda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

Ayah   44:58   الأية
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
Hausa
 
Dőmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ăni) da harshenka, tsammăninsu, su riƙa tunăwa.

Ayah   44:59   الأية
فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ
Hausa
 
Sai ka yi jira. Lalle sũ, măsu jira ne.
 


© EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us