Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da
wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da
aka yi musu gargaɗi (da shi).
Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna
mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku
zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani
ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa
masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga
kiransu?
Kõkuwã sunã cẽwa: "Yã ƙirƙira shi (Alƙur'ãni) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi
ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke
kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada
tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
Ka ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da
ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa
gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa."
Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma
kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida
a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã
Ya shiryar da mutãne azzãlumai."
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya
kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su
shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe."
Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma
rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a
harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra
ga mãsu kyautatãwa.
Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi
cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a
lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in,ya ce: "Ya
Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da
kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da
shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka,
kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)."
Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata,
kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan
wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi).
Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni
cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa
sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah
taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne."
Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko."
Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda
suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ,
sun kasance mãsu hasãra.
Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin
(Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su
ba.
Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã ( a ce musu): "Kun
tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin
dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka
kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin
da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi."
Kuma ka ambaci ɗan'uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan
Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare
shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku
azãbar yini mai girma."
Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo
mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni
da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya."
To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce:
"Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar
saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma
Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba,
kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da
ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya
wajaba a gare su.
To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi.wa baiko, gumaka,
ba su taimake su ba ? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da
abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren
Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da
aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.
Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn
Mũsã,mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da
kuma zuwa ga hanya madaidaiciya.
"Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa
ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata
bayyananna."
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa
kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na'am,
lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe,
wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!"
Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na
kãfirci."
Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi
haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin
(sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini.
Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne
fasiƙai.