First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَوْفُوا بِالْعُقُودِ ۚ أُحِلَّتْ لَكُم بَهِيمَةُ
الْأَنْعَامِ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ غَيْرَ مُحِلِّي الصَّيْدِ وَأَنتُمْ
حُرُمٌ ۗ إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ مَا يُرِيدُ
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin
dăɗi făce abin da ake karantăwa a kanku, bă kună măsu halattar da farauta ba
alhăli kuwa kună măsu harama. Lalle ne, Allah Yană hukunta abin da yake nufi.
|
Ayah 5:2 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُحِلُّوا شَعَائِرَ اللَّهِ وَلَا الشَّهْرَ
الْحَرَامَ وَلَا الْهَدْيَ وَلَا الْقَلَائِدَ وَلَا آمِّينَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ
يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّن رَّبِّهِمْ وَرِضْوَانًا ۚ وَإِذَا حَلَلْتُمْ
فَاصْطَادُوا ۚ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ أَن صَدُّوكُمْ عَنِ
الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ أَن تَعْتَدُوا ۘ وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ
وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا
اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Hausa
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmăni! kada ku halattar da ayyukan ibădar Allah game da
hajji, kuma da wată mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rătayar raƙuman hadaya,
kuma da măsu nufin ¦ăki mai alfarma, sună neman falala daga Ubangijinsu da
yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu
mutăne ta ɗauke ku, dőmin sun kange ku daga Masallăci Mai alfarma, ga ku yi
zălunci. Kuma ku taimaki jună a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki
juna a kan zunubi da zălunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai
tsananin uƙũba ne.
|
Ayah 5:3 الأية
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنزِيرِ وَمَا أُهِلَّ
لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ
وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى
النُّصُبِ وَأَن تَسْتَقْسِمُوا بِالْأَزْلَامِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ الْيَوْمَ
يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ ۚ
الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي
وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا ۚ فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ
مُتَجَانِفٍ لِّإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hausa
An haramta muku mũshe da jini da năman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin
Allah a gare shi, da măƙararriya da jefaffiya da mai gangarőwa da sőkakkiya, da
abin da măsu dăgi suka ci, făce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan
gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na căca wannan
făsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kăfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabőda
haka kada ku ji tsőronsu kuma ku ji tsőroNa. A yau Nă kammală muku addininku,
Kuma Nă cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nă yarda da Musulunci ya zama addini a gare
ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bă yana mai karkata
zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 5:4 الأية
يَسْأَلُونَكَ مَاذَا أُحِلَّ لَهُمْ ۖ قُلْ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ ۙ وَمَا
عَلَّمْتُم مِّنَ الْجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ
اللَّهُ ۖ فَكُلُوا مِمَّا أَمْسَكْنَ عَلَيْكُمْ وَاذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ
عَلَيْهِ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ
Hausa
Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa
măsu dăɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga măsu yin mĩki, kună măsu sakinsu
daga hannuwanku, kună sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci
daga abin da suka kama sabőda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi
Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawă ne.
|
Ayah 5:5 الأية
الْيَوْمَ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ ۖ وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ
حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْ ۖ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ
وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ إِذَا
آتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِي
أَخْدَانٍ ۗ وَمَن يَكْفُرْ بِالْإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي
الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Hausa
A yau an halatta muku abũbuwa măsu dăɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littăfi
halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mătă măsu kămun kai
daga muminai da mătă 'yă'ya daga waɗanda aka bai wa Littăfi a gabăninku idan kun
je musu da sadăkőkinsu, kuna măsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bă măsu
riƙon abőkai ba. Kuma wanda ya kăfirta da ĩmăni to, lalle ne aikinsa yă ɓăci,
kuma shĩ, a cikin Lăhira, yană daga măsu hasăra.
|
Ayah 5:6 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا
وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ
وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ ۚ وَإِن كُنتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا ۚ وَإِن
كُنتُم مَّرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِّنكُم مِّنَ الْغَائِطِ
أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا
طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُم مِّنْهُ ۚ مَا يُرِيدُ اللَّهُ
لِيَجْعَلَ عَلَيْكُم مِّنْ حَرَجٍ وَلَٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ
نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni ! idan kun tăshi zuwa ga salla, to, ku wanke
fuskőkinku da hannuwanku zuwa ga magincirőri, kuma ku yi shăfa ga kănunku, kuma
ku (wanke) ƙafăfunku zuwa idănun săwu biyu. Kuma idan kun kasance măsu janaba,
to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kő kuwa a kan tafiya, kő kuwa
ɗaya daga gare ku ya zo daga kăshi, kő kuka yi shăfayyar jună da mătă, sa'an nan
ba ku sămi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shăfa ga
fuskőkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bă Ya nufi dőmin Ya sanya wani
ƙunci a kanku, kuma amma Yană nufi dőmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammăninku
kună gődewa.
|
Ayah 5:7 الأية
وَاذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَمِيثَاقَهُ الَّذِي وَاثَقَكُم بِهِ
إِذْ قُلْتُمْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ
بِذَاتِ الصُّدُورِ
Hausa
Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a
lőkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗă'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle
ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata."
|
Ayah 5:8 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ لِلَّهِ شُهَدَاءَ بِالْقِسْطِ
ۖ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلَىٰ أَلَّا تَعْدِلُوا ۚ اعْدِلُوا هُوَ
أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا
تَعْمَلُونَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku kasance măsu tsayin daka dőmin Allah măsu shaida
da ădalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bă ză ku yi ădalci
ba. Ku yi ădalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle
Allah Masani ne ga abin da kuke aikatăwa.
|
Ayah 5:9 الأية
وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ۙ لَهُم مَّغْفِرَةٌ
وَأَجْرٌ عَظِيمٌ
Hausa
Allah Yă yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai.
Sună da wata găfara da lăda mai girma.
|
Ayah 5:10 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta, kuma suka ƙaryată, game da ăyőyinMu, waɗannan su ne
abőkan wuta.
|
Ayah 5:11 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ هَمَّ
قَوْمٌ أَن يَبْسُطُوا إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ فَكَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ ۖ
وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ
Hausa
Yă kũ waɗanda suka yi ĩmăni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lőkacin da wasu
mutăne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange
hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara
ga Allah kawai.
|
Ayah 5:12 الأية
وَلَقَدْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَبَعَثْنَا مِنْهُمُ اثْنَيْ
عَشَرَ نَقِيبًا ۖ وَقَالَ اللَّهُ إِنِّي مَعَكُمْ ۖ لَئِنْ أَقَمْتُمُ الصَّلَاةَ
وَآتَيْتُمُ الزَّكَاةَ وَآمَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرْتُمُوهُمْ وَأَقْرَضْتُمُ
اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ
وَلَأُدْخِلَنَّكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۚ فَمَن كَفَرَ
بَعْدَ ذَٰلِكَ مِنكُمْ فَقَدْ ضَلَّ سَوَاءَ السَّبِيلِ
Hausa
Kuma lalle Allah Yă riƙi alkawarin Banĩ lsră' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gőma
shă biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Ină tăre da ku, haƙĩƙa,
idan kun tsayar da salla, kuma kun băyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da
manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa,
Ină kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Ină shigar da ku gidăjen
Aljanna (waɗanda) ƙőramu sană gudăna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kăfirta a
băyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yă ɓace daga tsakar hanya."
|
Ayah 5:13 الأية
فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَاقَهُمْ لَعَنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً ۖ
يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ ۙ وَنَسُوا حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا بِهِ
ۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَائِنَةٍ مِّنْهُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۖ
فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Hausa
To, sabőda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukătansu
ƙeƙasassu, sună karkatar da magana daga wurărenta, kuma suka manta da wani yanki
daga abin da aka tunătar da su da shi, kuma bă ză ka gushe ba kana tsinkăyar
yaudara daga gare su făce kaɗan daga gare su. To, ka yăfe laifi daga gare su,
kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yană son măsu kyautatăwa.
|
Ayah 5:14 الأية
وَمِنَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّا نَصَارَىٰ أَخَذْنَا مِيثَاقَهُمْ فَنَسُوا حَظًّا
مِّمَّا ذُكِّرُوا بِهِ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ
إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ ۚ وَسَوْفَ يُنَبِّئُهُمُ اللَّهُ بِمَا كَانُوا
يَصْنَعُونَ
Hausa
Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasăra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai
suka manta da wani yanki daga abin da aka tunătar da su da shi, sai Muka
shushuta adăwa da ƙeta a tsakăninsu har ya zuwa ga Rănar ˇiyăma. Kuma Allah zai
bă su lăbari da abin da suka kasance sună sană'antawa.
|
Ayah 5:15 الأية
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيرًا
مِّمَّا كُنتُمْ تُخْفُونَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَعْفُو عَن كَثِيرٍ ۚ قَدْ جَاءَكُم
مِّنَ اللَّهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُّبِينٌ
Hausa
Yă Mutănen littăfi! Lalle ne, ManzonMu yă je muku, yană bayyana muku abu mai
yawa daga abin da kuka kasance kună ɓőyewa daga Littăfi, kuma yană rangwame daga
abu mai yawa. Haƙĩƙa,wani haske da wani Littafi mai bayyanăwa yă je muku daga
Allah.
|
Ayah 5:16 الأية
يَهْدِي بِهِ اللَّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلَامِ وَيُخْرِجُهُم
مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَىٰ صِرَاطٍ
مُّسْتَقِيمٍ
Hausa
Dashĩ, Allah Yană shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyőyin aminci, kuma
Yană fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yană shiryar da su
zuwa ga hanya madaidaiciya.
|
Ayah 5:17 الأية
لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ ۚ
قُلْ فَمَن يَمْلِكُ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا إِنْ أَرَادَ أَن يُهْلِكَ الْمَسِيحَ
ابْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُ وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ۗ وَلِلَّهِ مُلْكُ
السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ
عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun
kăfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yă nufi
Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabă ɗaya?"
Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakăninsu, Yană
halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kőme, Mai ĩkon yi ne.
|
Ayah 5:18 الأية
وَقَالَتِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَىٰ نَحْنُ أَبْنَاءُ اللَّهِ وَأَحِبَّاؤُهُ ۚ
قُلْ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُم ۖ بَلْ أَنتُم بَشَرٌ مِّمَّنْ خَلَقَ ۚ
يَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ ۚ وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ
وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ
Hausa
Kuma Yahudu da Nasăra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masőyansa." Ka ce: "To,
don me Yake yi muku azăba da zunubanku? Ă'a ku mutăne ne daga waɗanda Ya
halitta, Yană găfartăwa ga wanda Yake so, kuma Yană azabta wanda Yake so. Kuma
Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakăninsu kuma zuwa gare shi
makomă take."
|
Ayah 5:19 الأية
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلَىٰ فَتْرَةٍ
مِّنَ الرُّسُلِ أَن تَقُولُوا مَا جَاءَنَا مِن بَشِيرٍ وَلَا نَذِيرٍ ۖ فَقَدْ
جَاءَكُم بَشِيرٌ وَنَذِيرٌ ۗ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
Yă Mutănen Littăfi! Lalle ManzonMu yă je muku yană bayyana muku, a kan lőkacin
fatara daga manzanni, dőmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushăra bai zo mana
ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai băyar da bushăra da
mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kőme, Mai ĩkon yi.
|
Ayah 5:20 الأية
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ يَا قَوْمِ اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ
إِذْ جَعَلَ فِيكُمْ أَنبِيَاءَ وَجَعَلَكُم مُّلُوكًا وَآتَاكُم مَّا لَمْ يُؤْتِ
أَحَدًا مِّنَ الْعَالَمِينَ
Hausa
Kuma a lőkacin da Musa ya ce wa mutănensa: "Yă ku mutănena! Ku tuna ni'imar
Allah a kanku; dőmin Yă sanya annabăwa a cikinku, kuma Yă sanya ku sarăkuna,
kuma Yă bă ku abin da bai bai wa kőwa ba daga tălikai."
|
Ayah 5:21 الأية
يَا قَوْمِ ادْخُلُوا الْأَرْضَ الْمُقَدَّسَةَ الَّتِي كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ
وَلَا تَرْتَدُّوا عَلَىٰ أَدْبَارِكُمْ فَتَنقَلِبُوا خَاسِرِينَ
Hausa
"Yă mutănena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabőda
ku, kuma kada ku kőma da băya, har ku juya kună măsu hasara."
|
Ayah 5:22 الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِنَّ فِيهَا قَوْمًا جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا
حَتَّىٰ يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِن يَخْرُجُوا مِنْهَا فَإِنَّا دَاخِلُونَ
Hausa
Suka ce: "Ya Musă! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutăne măsu ƙarfi kuma lalle
ne bă ză mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare
ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."
|
Ayah 5:23 الأية
قَالَ رَجُلَانِ مِنَ الَّذِينَ يَخَافُونَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمَا ادْخُلُوا
عَلَيْهِمُ الْبَابَ فَإِذَا دَخَلْتُمُوهُ فَإِنَّكُمْ غَالِبُونَ ۚ وَعَلَى
اللَّهِ فَتَوَكَّلُوا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa
Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsőron Allah, Allah Yă yi ni'ima a kansu, suka
ce: "Ku shiga gare su, daga ƙőfar, dőmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku,
măsu rinjăya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."
|
Ayah 5:24 الأية
قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا أَبَدًا مَّا دَامُوا فِيهَا ۖ
فَاذْهَبْ أَنتَ وَرَبُّكَ فَقَاتِلَا إِنَّا هَاهُنَا قَاعِدُونَ
Hausa
Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bă za mu shige ta ba har abada matuƙar sun
dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dőmin ku yi yăƙi. Lalle ne mu,
mună a nan zaune."
|
Ayah 5:25 الأية
قَالَ رَبِّ إِنِّي لَا أَمْلِكُ إِلَّا نَفْسِي وَأَخِي ۖ فَافْرُقْ بَيْنَنَا
وَبَيْنَ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ
Hausa
Ya ce: "Yă Ubangijina! Lalle ne nĩ, bă ni mallakar kőwa făce kaina da ɗan'uwăna,
sai Ka rarrabe a tsakăninmu da tsakănin mutăne făsiƙai."
|
Ayah 5:26 الأية
قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيْهِمْ ۛ أَرْبَعِينَ سَنَةً ۛ يَتِيهُونَ فِي
الْأَرْضِ ۚ فَلَا تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ
Hausa
(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtăwa ce a gare su, shekara arba'in,
sună yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabőda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutăne
făsiƙai."
|
Ayah 5:27 الأية
وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ابْنَيْ آدَمَ بِالْحَقِّ إِذْ قَرَّبَا قُرْبَانًا
فَتُقُبِّلَ مِنْ أَحَدِهِمَا وَلَمْ يُتَقَبَّلْ مِنَ الْآخَرِ قَالَ
لَأَقْتُلَنَّكَ ۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللَّهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ
Hausa
Kuma karantă musu lăbărin ɗiya biyu na Ădamu, da gaskiya, a lőkacin da suka
băyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce:
"Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓă
daga măsu taƙawa ne."
|
Ayah 5:28 الأية
لَئِن بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقْتُلَنِي مَا أَنَا بِبَاسِطٍ يَدِيَ إِلَيْكَ
لِأَقْتُلَكَ ۖ إِنِّي أَخَافُ اللَّهَ رَبَّ الْعَالَمِينَ
Hausa
"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dőmin ka kashe ni, ban zama mai
shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dőmin in kashe ka. Lalle ne nĩ ină tsőron Allah
Ubangijin tălikai.
|
Ayah 5:29 الأية
إِنِّي أُرِيدُ أَن تَبُوءَ بِإِثْمِي وَإِثْمِكَ فَتَكُونَ مِنْ أَصْحَابِ
النَّارِ ۚ وَذَٰلِكَ جَزَاءُ الظَّالِمِينَ
Hausa
"Lalle ne nĩ ină nufin ka kőma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance
daga abőkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzălumai."
|
Ayah 5:30 الأية
فَطَوَّعَتْ لَهُ نَفْسُهُ قَتْلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُ فَأَصْبَحَ مِنَ
الْخَاسِرِينَ
Hausa
Sai ransa ya ƙawătar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan
ya wayi gari daga măsu hasăra.
|
Ayah 5:31 الأية
فَبَعَثَ اللَّهُ غُرَابًا يَبْحَثُ فِي الْأَرْضِ لِيُرِيَهُ كَيْفَ يُوَارِي
سَوْءَةَ أَخِيهِ ۚ قَالَ يَا وَيْلَتَا أَعَجَزْتُ أَنْ أَكُونَ مِثْلَ هَٰذَا
الْغُرَابِ فَأُوَارِيَ سَوْءَةَ أَخِي ۖ فَأَصْبَحَ مِنَ النَّادِمِينَ
Hausa
Sai Allah Ya aiki wani hankăka, yană tőno a cikin ƙasa dőmin ya nuna masa yadda
zai turbuɗe găwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitőna! Nă kăsa in kasance kamar wannan
hankăka dőmin in turbuɗe găwar ɗan'uwana?" Sai ya wăyi gari daga măsu nadămă.
|
Ayah 5:32 الأية
مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ
نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ
جَمِيعًا وَمَنْ أَحْيَاهَا فَكَأَنَّمَا أَحْيَا النَّاسَ جَمِيعًا ۚ وَلَقَدْ
جَاءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِالْبَيِّنَاتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم بَعْدَ
ذَٰلِكَ فِي الْأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ
Hausa
Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsră'ĩla cewa, lalle ne wanda ya
kashe rai bă da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yă kashe mutăne
duka ne, kuma wanda ya răya rai, to, kamar yă răyar da mutăne ne gabă ɗaya. Kuma
lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjőji bayyanannu, sa'an nan kuma
lalle ne, măsu yawa daga gare su, a băyan wannan, haƙĩƙa, măsuɓarna ne a cikin
ƙasa.
|
Ayah 5:33 الأية
إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي
الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ
وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ ۚ ذَٰلِكَ لَهُمْ خِزْيٌ
فِي الدُّنْيَا ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Hausa
Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yăƙin Allah da Manzonsa, kuma sună aiki a
cikin ƙasa dőmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kő kuwa a kakkătse
hannuwansu da ƙafăfunsu daga săɓăni, ko kuwa a kőre su daga ƙasa. Sannan gare su
wulakanci ne a cikin răyuwar duniya, kuma a Lăhira sună da wata azăba mai girma.
|
Ayah 5:34 الأية
إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا مِن قَبْلِ أَن تَقْدِرُوا عَلَيْهِمْ ۖ فَاعْلَمُوا
أَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hausa
Făce fa waɗanda suka tuba tun a gabănin ku sămi ĩko akansu, to, ku sani cewa
lalle ne, Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 5:35 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ
الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare
shi, kuma ku yi jihădi a cikin hanyarsa, tsammăninku, za ku ci nasara.
|
Ayah 5:36 الأية
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُ
مَعَهُ لِيَفْتَدُوا بِهِ مِنْ عَذَابِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنْهُمْ
ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
Lalle ne waɗanda suka kăfirta, lalle dă sună da abin da ke a cikin ƙasa gabă
ɗaya da misălinsa tăre da shi, dőmin su yi fansa da shi daga azăbar Rănar
ˇiyăma, bă a karɓarsa daga gare su, kuma sună da azăba mai raɗadi.
|
Ayah 5:37 الأية
يُرِيدُونَ أَن يَخْرُجُوا مِنَ النَّارِ وَمَا هُم بِخَارِجِينَ مِنْهَا ۖ
وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ
Hausa
Sună nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama măsu fita daga gare ta ba, kuma
sună da azăba zaunanniya.
|
Ayah 5:38 الأية
وَالسَّارِقُ وَالسَّارِقَةُ فَاقْطَعُوا أَيْدِيَهُمَا جَزَاءً بِمَا كَسَبَا
نَكَالًا مِّنَ اللَّهِ ۗ وَاللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Hausa
Kuma ɓarăwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka
tsirfanta, a kan azăba daga Allah. Kuma Allah Mabuwăyi ne, Mai hikima.
|
Ayah 5:39 الأية
فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ
إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hausa
To, wanda ya tuba a băyan zăluncinsa, kuma ya gyăra (halinsa), to, lalle ne
Allah Yană karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai găfara ne, Mai jin ƙai.
|
Ayah 5:40 الأية
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يُعَذِّبُ
مَن يَشَاءُ وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ ۗ وَاللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
Hausa
Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yană
azăbtar da wanda Yake so, kuma Yană yin găfara ga wanda yake so, kuma Allah a
dukkan kőme, Mai ĩkon yi ne?
|
Ayah 5:41 الأية
يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ لَا يَحْزُنكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ مِنَ
الَّذِينَ قَالُوا آمَنَّا بِأَفْوَاهِهِمْ وَلَمْ تُؤْمِن قُلُوبُهُمْ ۛ وَمِنَ
الَّذِينَ هَادُوا ۛ سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ سَمَّاعُونَ لِقَوْمٍ آخَرِينَ لَمْ
يَأْتُوكَ ۖ يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ مِن بَعْدِ مَوَاضِعِهِ ۖ يَقُولُونَ إِنْ
أُوتِيتُمْ هَٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمْ تُؤْتَوْهُ فَاحْذَرُوا ۚ وَمَن يُرِدِ
اللَّهُ فِتْنَتَهُ فَلَن تَمْلِكَ لَهُ مِنَ اللَّهِ شَيْئًا ۚ أُولَٰئِكَ
الَّذِينَ لَمْ يُرِدِ اللَّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمْ ۚ لَهُمْ فِي الدُّنْيَا
خِزْيٌ ۖ وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Hausa
Yă kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kăfirci su ɓăta maka rai,
daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmăni" da băkunansu, alhăli zukatansu ba su yi
ĩmănin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) măsu yawan saurare ga wasu
mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sună karkatar da zance daga băyan
wurarensa, sună cewa: "Idan an bă ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bă ku
shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bă ză ka
mallaka masa kőme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya
tsarkake zukătansu ba. Sună da kunya a cikin duniya, kuma sună da wata azăba mai
girma a cikin 1ăhira.
|
Ayah 5:42 الأية
سَمَّاعُونَ لِلْكَذِبِ أَكَّالُونَ لِلسُّحْتِ ۚ فَإِن جَاءُوكَ فَاحْكُم
بَيْنَهُمْ أَوْ أَعْرِضْ عَنْهُمْ ۖ وَإِن تُعْرِضْ عَنْهُمْ فَلَن يَضُرُّوكَ
شَيْئًا ۖ وَإِنْ حَكَمْتَ فَاحْكُم بَيْنَهُم بِالْقِسْطِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ
الْمُقْسِطِينَ
Hausa
Măsu yawan saurăre ga ƙarya ne, măsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka,
sai ka yi hukunci a tsakăninsu kő ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira
daga gare su, to, bă ză su cuce ka da kőme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai
ka hukunta a tsakăninsu da ădalci. Lalle ne, Allah Yană son măsu ădalci.
|
Ayah 5:43 الأية
وَكَيْفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ التَّوْرَاةُ فِيهَا حُكْمُ اللَّهِ ثُمَّ
يَتَوَلَّوْنَ مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا أُولَٰئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ
Hausa
Kuma yăya suke gabătar da kai ga hukunci, alhăli a wurinsu akwai Attaura, a
cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sună karkacewa a băyan wannan?
waɗannan bă muminai ba ne!
|
Ayah 5:44 الأية
إِنَّا أَنزَلْنَا التَّوْرَاةَ فِيهَا هُدًى وَنُورٌ ۚ يَحْكُمُ بِهَا
النَّبِيُّونَ الَّذِينَ أَسْلَمُوا لِلَّذِينَ هَادُوا وَالرَّبَّانِيُّونَ
وَالْأَحْبَارُ بِمَا اسْتُحْفِظُوا مِن كِتَابِ اللَّهِ وَكَانُوا عَلَيْهِ
شُهَدَاءَ ۚ فَلَا تَخْشَوُا النَّاسَ وَاخْشَوْنِ وَلَا تَشْتَرُوا بِآيَاتِي
ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ
الْكَافِرُونَ
Hausa
Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabăwa
waɗanda suke sun sallamă, sună yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu),
da mălaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga
Littăfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, măsu bă da shaida. To, kada ku ji
tsőron mutăne kuma ku ji tsőroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ăyoyiNa.
wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.
|
Ayah 5:45 الأية
وَكَتَبْنَا عَلَيْهِمْ فِيهَا أَنَّ النَّفْسَ بِالنَّفْسِ وَالْعَيْنَ
بِالْعَيْنِ وَالْأَنفَ بِالْأَنفِ وَالْأُذُنَ بِالْأُذُنِ وَالسِّنَّ بِالسِّنِّ
وَالْجُرُوحَ قِصَاصٌ ۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِ فَهُوَ كَفَّارَةٌ لَّهُ ۚ وَمَن
لَّمْ يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ
Hausa
Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (ană kashe) rai sabőda rai, kuma
(ană ɗebe) idő sabőda idő, kuma (ana katse) hanci sabőda hanci, kuma kunne
sabőda kunne kuma haƙori sabőda haƙőri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya
yi sadaka da shi, to, shi kaffăra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da
abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzălumai.
|
Ayah 5:46 الأية
وَقَفَّيْنَا عَلَىٰ آثَارِهِم بِعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ
يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ ۖ وَآتَيْنَاهُ الْإِنجِيلَ فِيهِ هُدًى وَنُورٌ
وَمُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْرَاةِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةً
لِّلْمُتَّقِينَ
Hausa
Kuma Muka biyar a kan gurăbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yănă mai gaskatăwa ga abin
da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bă shi Injĩla a cikinsa akwai
shiriya da haske, yană mai gaskatăwa ga abin da yake a gaba gare shi daga
Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga măsu taƙawa.
|
Ayah 5:47 الأية
وَلْيَحْكُمْ أَهْلُ الْإِنجِيلِ بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ فِيهِ ۚ وَمَن لَّمْ
يَحْكُم بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
Hausa
Kuma sai mutănen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma
wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne făsiƙai.
|
Ayah 5:48 الأية
وَأَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ
مِنَ الْكِتَابِ وَمُهَيْمِنًا عَلَيْهِ ۖ فَاحْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ
اللَّهُ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ عَمَّا جَاءَكَ مِنَ الْحَقِّ ۚ لِكُلٍّ
جَعَلْنَا مِنكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجًا ۚ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَكُمْ
أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَٰكِن لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُمْ ۖ فَاسْتَبِقُوا
الْخَيْرَاتِ ۚ إِلَى اللَّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ
فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
Hausa
Kuma Mun saukar da Littăfi zuwa gare ka da gaskiya, yană mai gaskatăwa ga abin
da yake a gaba gare shi daga Littăfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartăwa a
kansa. sai ka yi hukunci a tsakăninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka
bĩbiyi son zũciyőyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya . Ga kőwanne daga
gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dă Allah Yă so, dă Yă sanya
ku al'umma guda, kuma amma dőmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bă ku. Sai ku
yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makőmarku take gabă ɗaya. Sa'an nan Ya
bă ku lăbări ga abin da kuka kasance kună săɓăwa a cikinsa.
|
Ayah 5:49 الأية
وَأَنِ احْكُم بَيْنَهُم بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ
وَاحْذَرْهُمْ أَن يَفْتِنُوكَ عَن بَعْضِ مَا أَنزَلَ اللَّهُ إِلَيْكَ ۖ فَإِن
تَوَلَّوْا فَاعْلَمْ أَنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعْضِ
ذُنُوبِهِمْ ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ لَفَاسِقُونَ
Hausa
Kuma ka yi hukunci a tsakăninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi
son zũciyőyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga săshen abin da Allah Ya
saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya băya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana
nufin Ya săme su da masĩfa ne sabőda săshen zunubansu. Kuma lalle ne, măsu yawa
daga mutăne, haƙĩƙa, făsiƙai ne.
|
Ayah 5:50 الأية
أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ ۚ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ حُكْمًا
لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ
Hausa
Shin, hukuncin Jăhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah
sabőda mutăne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmăni)?
|
Ayah 5:51 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْيَهُودَ وَالنَّصَارَىٰ
أَوْلِيَاءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ
فَإِنَّهُ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasăra majiɓinta. Săshensu
majiɓinci ne ga săshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ,
yană daga gare su. Lalle Allah bă Ya shiryar da mutăne azzălumai.
|
Ayah 5:52 الأية
فَتَرَى الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يُسَارِعُونَ فِيهِمْ يَقُولُونَ
نَخْشَىٰ أَن تُصِيبَنَا دَائِرَةٌ ۚ فَعَسَى اللَّهُ أَن يَأْتِيَ بِالْفَتْحِ
أَوْ أَمْرٍ مِّنْ عِندِهِ فَيُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا أَسَرُّوا فِي أَنفُسِهِمْ
نَادِمِينَ
Hausa
Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sună tseren gaugawa a cikinsu,
sună cewa: "Mună tsőron kada wata masĩfa ta săme mu." To, akwai tsammănin Allah
Ya zo da buɗi, kő kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wăyi gari a kan abin da
suka ɓőye a cikin zukatansu, sună măsu nadămă.
|
Ayah 5:53 الأية
وَيَقُولُ الَّذِينَ آمَنُوا أَهَٰؤُلَاءِ الَّذِينَ أَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ
أَيْمَانِهِمْ ۙ إِنَّهُمْ لَمَعَكُمْ ۚ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فَأَصْبَحُوا
خَاسِرِينَ
Hausa
Kuma waɗanda suka yi ĩmăni sună cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi
rantsuwa da Allah iyăkar rantsuwőyinsu, cewa su, lalle sună tăre da ku?"
Ayyukansu sun ɓăci, sabőda haka suka wăyi gari sună măsu hasăra.
|
Ayah 5:54 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا مَن يَرْتَدَّ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَسَوْفَ
يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى
الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ يُجَاهِدُونَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ
وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَائِمٍ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ
ۚ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to,
Allah zai zo da wasu mutăne, Yană son su kuma sună son Sa, măsu tawălu'i a kan
muminai măsu izza a kan kăfurai. Sună yin, jihădi a cikin hanyar Allah, kuma bă
su tsőron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yană băyar da ita ga
wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.
|
Ayah 5:55 الأية
إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُوا الَّذِينَ
يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ
Hausa
Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi
ĩmăni,waɗanda suke sună tsayar da salla kuma sună băyar da zakka kuma sună
ruku'i,
|
Ayah 5:56 الأية
وَمَن يَتَوَلَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آمَنُوا فَإِنَّ حِزْبَ اللَّهِ
هُمُ الْغَالِبُونَ
Hausa
Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmăni, to, ƙungiyar
Allah sune măsu rinjăya.
|
Ayah 5:57 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الَّذِينَ اتَّخَذُوا دِينَكُمْ
هُزُوًا وَلَعِبًا مِّنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ
وَالْكُفَّارَ أَوْلِيَاءَ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa
izgili da wăsa, daga waɗanda aka bai wa Littăfi daga gabăninku da kăfirai,
masőya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.
|
Ayah 5:58 الأية
وَإِذَا نَادَيْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ اتَّخَذُوهَا هُزُوًا وَلَعِبًا ۚ ذَٰلِكَ
بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْقِلُونَ
Hausa
Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wăsa. Wannan
dőmin lalle ne su, mutăne ne (waɗanda) bă su hankalta.
|
Ayah 5:59 الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ هَلْ تَنقِمُونَ مِنَّا إِلَّا أَنْ آمَنَّا بِاللَّهِ
وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلُ وَأَنَّ أَكْثَرَكُمْ فَاسِقُونَ
Hausa
Ka ce: "Ya Mutănen Littăfi! Shin, kună ganin wani laifi daga gare mu? Făce dai
dőmin mun yi ĩmăni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka
saukar daga gabăni, kuma dőmin mafi yawanku făsiƙai ne."
|
Ayah 5:60 الأية
قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ اللَّهِ ۚ مَن
لَّعَنَهُ اللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ الْقِرَدَةَ
وَالْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ الطَّاغُوتَ ۚ أُولَٰئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ عَن
سَوَاءِ السَّبِيلِ
Hausa
Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dőmin sakamako daga wurin
Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga
gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ăguta. Waɗannan ne mafiya sharrin
wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
|
Ayah 5:61 الأية
وَإِذَا جَاءُوكُمْ قَالُوا آمَنَّا وَقَد دَّخَلُوا بِالْكُفْرِ وَهُمْ قَدْ
خَرَجُوا بِهِ ۚ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا كَانُوا يَكْتُمُونَ
Hausa
Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmăni." Alhăli kuwa haƙĩƙa, sun shigo
da kăfirci,kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da
suka kasance sună ɓőyewa.
|
Ayah 5:62 الأية
وَتَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يُسَارِعُونَ فِي الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ
وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
Hausa
Kuma kana ganin măsu yawa daga gare su, sună tseren gaugawa a cikin zunubi da
zălunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatăwa.
|
Ayah 5:63 الأية
لَوْلَا يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ عَن قَوْلِهِمُ الْإِثْمَ
وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَصْنَعُونَ
Hausa
Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hană su daga faɗarsu
ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sună
sană'antăwa.
|
Ayah 5:64 الأية
وَقَالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللَّهِ مَغْلُولَةٌ ۚ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُوا
بِمَا قَالُوا ۘ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَاءُ ۚ
وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَانًا
وَكُفْرًا ۚ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَىٰ يَوْمِ
الْقِيَامَةِ ۚ كُلَّمَا أَوْقَدُوا نَارًا لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا اللَّهُ ۚ
وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا ۚ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ
Hausa
Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a
cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabőda abin da suka faɗa. Ă'a, hannuwanSa biyu
shimfiɗaɗɗu ne, Yană ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar
zuwa gare ka yană ƙăra wa măsu yawa daga gare su, girman kai da kăfirci. Kuma
Mun jefa a tsakăninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rănar ˇiyăma, kő da yaushe suka
hura wata wuta dőmin yăƙi, sai Allah Ya bice ta. Sună aiki a cikin ƙasa dőmin
ɓarna, alhăli kuwa Allah bă Ya son măsu fasădi.
|
Ayah 5:65 الأية
وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْكِتَابِ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَكَفَّرْنَا عَنْهُمْ
سَيِّئَاتِهِمْ وَلَأَدْخَلْنَاهُمْ جَنَّاتِ النَّعِيمِ
Hausa
Kuma dă dai lalle Mutănen Littăfi sun yi ĩmăni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dă
Mun kankare miyăgun ayyukansu daga gare su, kuma dă Mun shigar da su gidăjen
Aljannar Ni'ima.
|
Ayah 5:66 الأية
وَلَوْ أَنَّهُمْ أَقَامُوا التَّوْرَاةَ وَالْإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِم
مِّن رَّبِّهِمْ لَأَكَلُوا مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِم ۚ مِّنْهُمْ
أُمَّةٌ مُّقْتَصِدَةٌ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ سَاءَ مَا يَعْمَلُونَ
Hausa
Kuma dă dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa
gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dă sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin
ƙafăfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaităwa kuma măsu yawa daga
gare su, abin da suke aikatawa yă munana.
|
Ayah 5:67 الأية
يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ۖ وَإِن لَّمْ
تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ ۚ وَاللَّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ النَّاسِ ۗ
إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْكَافِرِينَ
Hausa
Yă kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma
idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yană
tsare ka daga mutăne. Lalle ne, Allah bă Ya shiryar da mutăne kăfirai.
|
Ayah 5:68 الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَسْتُمْ عَلَىٰ شَيْءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُوا التَّوْرَاةَ
وَالْإِنجِيلَ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ ۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا
مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَانًا وَكُفْرًا ۖ فَلَا تَأْسَ
عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ
Hausa
Ka ce: "Yă ku Mutănen Littăfi! Ba ku zama a kan kőme ba, sai kun tsayar da
Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma
lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yană ƙara wa măsu
yawa daga gare su girman kai da kăfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutăne
kăfirai.
|
Ayah 5:69 الأية
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئُونَ وَالنَّصَارَىٰ مَنْ
آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ
وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Hausa
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmăni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da
Nasăra, wanda ya yi ĩmăni da Allahda Rănar Lăhira, kuma ya aikata aiki na
ƙwarai, to, băbu tsőro a kansu, kuma bă su zamo sună baƙin ciki ba.
|
Ayah 5:70 الأية
لَقَدْ أَخَذْنَا مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ وَأَرْسَلْنَا إِلَيْهِمْ رُسُلًا ۖ
كُلَّمَا جَاءَهُمْ رَسُولٌ بِمَا لَا تَهْوَىٰ أَنفُسُهُمْ فَرِيقًا كَذَّبُوا
وَفَرِيقًا يَقْتُلُونَ
Hausa
Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isră'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa
gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da răyukansu bă su so, wani
ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sună kashewa,
|
Ayah 5:71 الأية
وَحَسِبُوا أَلَّا تَكُونَ فِتْنَةٌ فَعَمُوا وَصَمُّوا ثُمَّ تَابَ اللَّهُ
عَلَيْهِمْ ثُمَّ عَمُوا وَصَمُّوا كَثِيرٌ مِّنْهُمْ ۚ وَاللَّهُ بَصِيرٌ بِمَا
يَعْمَلُونَ
Hausa
Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bă ză ta kasance ba sai Suka makanta, kuma
suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta
kuma suka kurunta măsu yawa daga gare su, alhăli Allah Mai gani ne ga abin da
suke aikatăwa.
|
Ayah 5:72 الأية
لَقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ هُوَ الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ ۖ
وَقَالَ الْمَسِيحُ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ اعْبُدُوا اللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمْ ۖ
إِنَّهُ مَن يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ
وَمَأْوَاهُ النَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ
Hausa
Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama,"
sun kăfirta. Alhăli kuwa Masĩhu yă ce: "Yă Banĩ Isră'ĩla! Ku bauta wa Allah
Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to,
lalle ne, Allah Yă haramta masa Aljanna. Kuma băbu wasu mataimaka ga azzălumai.
|
Ayah 5:73 الأية
لَّقَدْ كَفَرَ الَّذِينَ قَالُوا إِنَّ اللَّهَ ثَالِثُ ثَلَاثَةٍ ۘ وَمَا مِنْ
إِلَٰهٍ إِلَّا إِلَٰهٌ وَاحِدٌ ۚ وَإِن لَّمْ يَنتَهُوا عَمَّا يَقُولُونَ
لَيَمَسَّنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kăfirta, kuma
babu wani abin bautăwa făce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke
faɗa ba, haƙĩƙa, wata azăba mai raɗaɗi tănă shăfar waɗanda suka kăfirta daga
gare su.
|
Ayah 5:74 الأية
أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى اللَّهِ وَيَسْتَغْفِرُونَهُ ۚ وَاللَّهُ غَفُورٌ
رَّحِيمٌ
Hausa
shin fă, bă su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi găfara, alhăli kuwa Allah
Mai găfara ne, Mai jin ƙai?
|
Ayah 5:75 الأية
مَّا الْمَسِيحُ ابْنُ مَرْيَمَ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ
وَأُمُّهُ صِدِّيقَةٌ ۖ كَانَا يَأْكُلَانِ الطَّعَامَ ۗ انظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ
لَهُمُ الْآيَاتِ ثُمَّ انظُرْ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Hausa
Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba făce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige
dage gabăninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sună cin abinci. Ka duba
yadda Muke bayyana musu ăyőyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.
|
Ayah 5:76 الأية
قُلْ أَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا
نَفْعًا ۚ وَاللَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
Hausa
Ka ce: "Ashe kună bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta
sabőda ku kuma haka wani amfani alhăli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"
|
Ayah 5:77 الأية
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ غَيْرَ الْحَقِّ وَلَا
تَتَّبِعُوا أَهْوَاءَ قَوْمٍ قَدْ ضَلُّوا مِن قَبْلُ وَأَضَلُّوا كَثِيرًا
وَضَلُّوا عَن سَوَاءِ السَّبِيلِ
Hausa
Ka ce: "Yă ku Mutanen Littăfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bă
gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyőyin waɗansu mutăne waɗanda suka riga
suka ɓace a gabăni, kuma suka ɓatar da wasu măsu yawa, kuma suka ɓace daga
tsakar hanya."
|
Ayah 5:78 الأية
لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِن بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُودَ
وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَوا وَّكَانُوا يَعْتَدُونَ
Hausa
An la'ani waɗanda suka kăfirta daga Banĩ Isră'ĩla a kan harshen Dăwuda da Ĩsa
ɗan Maryama. wannan kuwa sabőda săɓăwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna
ta'addi .
|
Ayah 5:79 الأية
كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَن مُّنكَرٍ فَعَلُوهُ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا
يَفْعَلُونَ
Hausa
Sun kasance bă su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka
kasancesună aikatăwa yă munana.
|
Ayah 5:80 الأية
تَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يَتَوَلَّوْنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ لَبِئْسَ مَا
قَدَّمَتْ لَهُمْ أَنفُسُهُمْ أَن سَخِطَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَفِي الْعَذَابِ هُمْ
خَالِدُونَ
Hausa
Kana ganin măsu yawa daga gare su, sună jiɓintar waɗanda suka kăfirta. Haƙĩƙa
tir da abin da răyukansu suka gabătar sabőda su, watau Allah Yă yi fushi da su,
kuma a cikin azăba su măsu dawwama ne
|
Ayah 5:81 الأية
وَلَوْ كَانُوا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالنَّبِيِّ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مَا
اتَّخَذُوهُمْ أَوْلِيَاءَ وَلَٰكِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُمْ فَاسِقُونَ
Hausa
Kuma dă sun kasance sună ĩmăni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa
gare shi, dă ba su riƙe su masőya ba. Kuma amma măsu yawa daga gare su, făsiƙai
ne.
|
Ayah 5:82 الأية
لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ النَّاسِ عَدَاوَةً لِّلَّذِينَ آمَنُوا الْيَهُودَ
وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا ۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقْرَبَهُم مَّوَدَّةً لِّلَّذِينَ
آمَنُوا الَّذِينَ قَالُوا إِنَّا نَصَارَىٰ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنْهُمْ
قِسِّيسِينَ وَرُهْبَانًا وَأَنَّهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
Hausa
Lalle ne kana sămun mafiya tsananin mutăne a adăwa ga waɗanda suka yi
ĩmăni,Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kană sămun mafiya
kusantarsu a sőyayya ga waɗanda suka yi ĩmăni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu
ne Nasăra." Wancan kuwa sabőda akwai ˇissawa da ruhubănăwa daga cikinsu. Kuma
lalle ne su, bă su yin girman kai.
|
Ayah 5:83 الأية
وَإِذَا سَمِعُوا مَا أُنزِلَ إِلَى الرَّسُولِ تَرَىٰ أَعْيُنَهُمْ تَفِيضُ مِنَ
الدَّمْعِ مِمَّا عَرَفُوا مِنَ الْحَقِّ ۖ يَقُولُونَ رَبَّنَا آمَنَّا
فَاكْتُبْنَا مَعَ الشَّاهِدِينَ
Hausa
Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kană ganin idanunsu sună
zubar da hawăye, sabőda abin da suka sani daga gaskiya, sună cewa: "Yă
Ubangijinmu! Mun yi ĩmăni,sai ka rubuta mu tăre da măsu shaida.
|
Ayah 5:84 الأية
وَمَا لَنَا لَا نُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَمَا جَاءَنَا مِنَ الْحَقِّ وَنَطْمَعُ أَن
يُدْخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ الْقَوْمِ الصَّالِحِينَ
Hausa
"Kuma mene ne yake gare mu, bă ză mu yi ĩmăni daAllah ba, da kuma abin da ya zo
mana daga gaskiya, kuma mună gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tăre da mutăne
sălihai?"
|
Ayah 5:85 الأية
فَأَثَابَهُمُ اللَّهُ بِمَا قَالُوا جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ
خَالِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ جَزَاءُ الْمُحْسِنِينَ
Hausa
Sabőda haka, Allah Yă săkă musu, dőmin abin da suka faɗa da gidăjen Aljanna
(waɗanda) ƙőramu sună gudăna a ƙarƙashinsu, sună madawwama a cikinsu, kuma
wannan ne sakamakon măsu kyautatăwa.
|
Ayah 5:86 الأية
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Hausa
Kuma waɗanda suka kăfirta kuma suka ƙaryata game da ăyőyinMu, waɗancan ne abőkan
Wuta.
|
Ayah 5:87 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُحَرِّمُوا طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللَّهُ
لَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوا ۚ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku haramta abubuwa măsu dăɗi da Allah Ya
halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bă Ya son măsu ƙetare
haddi.
|
Ayah 5:88 الأية
وَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ حَلَالًا طَيِّبًا ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ
الَّذِي أَنتُم بِهِ مُؤْمِنُونَ
Hausa
Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da
taƙawa, wanda yake ku, măsu ĩmăni ne da shi.
|
Ayah 5:89 الأية
لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم
بِمَا عَقَّدتُّمُ الْأَيْمَانَ ۖ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ
مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ
رَقَبَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ
أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ
اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Hausa
Allah bă Ya kămă ku sabőda yăsassa a cikin rantsuwőyinku, kuma amma Yană kămă ku
da abin da kuka ƙudurta rantsuwőyi (a kansa). To, kaffărarsa ita ce ciyar da
miskĩni gőma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyălanku, kő kuwa tufătar da
su, kő kuwa 'yantăwar wuya. Sa'an nan wanda bai sămu ba, sai azumin kwăna uku.
wannan ne kaffărar rantsuwőyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyăye rantsuwoyinku.
Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ăyoyinsa, tsammăninku kună gődewa.
|
Ayah 5:90 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنصَابُ
وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ
تُفْلِحُونَ
Hausa
Ya ku waɗanda suka yi ĩmăni! Abin sani kawai, giya da căca da refu da kiban
ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci
nasara.
|
Ayah 5:91 الأية
إِنَّمَا يُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُوقِعَ بَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ
فِي الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَن ذِكْرِ اللَّهِ وَعَنِ الصَّلَاةِ ۖ
فَهَلْ أَنتُم مُّنتَهُونَ
Hausa
Abin sani kawaĩ Shaiɗan yană nufin ya aukar da adăwa da ƙeta a tsakăninku, a
cikin giya da căca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To,
shin, ku măsu hanuwa ne?
|
Ayah 5:92 الأية
وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَاحْذَرُوا ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ
فَاعْلَمُوا أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ
Hausa
Ku yi ɗă'a ga Allah, kuma ku yi ɗă'a ga Manzo, kuma ku kiyăye. To, idan kun
jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.
|
Ayah 5:93 الأية
لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوا
إِذَا مَا اتَّقَوا وَّآمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ثُمَّ اتَّقَوا وَّآمَنُوا
ثُمَّ اتَّقَوا وَّأَحْسَنُوا ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ
Hausa
Băbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin
abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmăni, kuma suka aikata ayyukan
ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmăni,sa'an nan kuma suka yi
taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son măsu kyautatăwa.
|
Ayah 5:94 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَيَبْلُوَنَّكُمُ اللَّهُ بِشَيْءٍ مِّنَ
الصَّيْدِ تَنَالُهُ أَيْدِيكُمْ وَرِمَاحُكُمْ لِيَعْلَمَ اللَّهُ مَن يَخَافُهُ
بِالْغَيْبِ ۚ فَمَنِ اعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga
farauta, hannuwanku da măsunku sună sămun sa dőmin Allah Ya san wanda yake
tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a băyan wannan, to, yană da azăba mai
raɗaɗi.
|
Ayah 5:95 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْتُلُوا الصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۚ وَمَن
قَتَلَهُ مِنكُم مُّتَعَمِّدًا فَجَزَاءٌ مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ النَّعَمِ
يَحْكُمُ بِهِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْيًا بَالِغَ الْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّارَةٌ
طَعَامُ مَسَاكِينَ أَوْ عَدْلُ ذَٰلِكَ صِيَامًا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِ ۗ
عَفَا اللَّهُ عَمَّا سَلَفَ ۚ وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ اللَّهُ مِنْهُ ۗ
وَاللَّهُ عَزِيزٌ ذُو انتِقَامٍ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku kashe farauta alhăli kună măsu harama. Kuma
wanda ya kashe shi daga gare ku, yană mai ganganci, sai sakamako misălin abin da
ya kashe, daga dabbőbin ni'ima, ma'abuta ădalci biyu daga cikinku sună yin
hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffăra da abincin
miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dőmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa.
Allah Yă yafe laifi daga abin da ya gabăta. Kuma wanda ya kőma, to, Allah zai yi
azăbar rămuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwăyi ne, ma'abũcin azabăr rămuwa.
|
Ayah 5:96 الأية
أُحِلَّ لَكُمْ صَيْدُ الْبَحْرِ وَطَعَامُهُ مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِلسَّيَّارَةِ ۖ
وَحُرِّمَ عَلَيْكُمْ صَيْدُ الْبَرِّ مَا دُمْتُمْ حُرُمًا ۗ وَاتَّقُوا اللَّهَ
الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Hausa
An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dőmin jin dăɗi a gare ku, kuma dőmin
matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama măsu
harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tăra ku.
|
Ayah 5:97 الأية
جَعَلَ اللَّهُ الْكَعْبَةَ الْبَيْتَ الْحَرَامَ قِيَامًا لِّلنَّاسِ وَالشَّهْرَ
الْحَرَامَ وَالْهَدْيَ وَالْقَلَائِدَ ۚ ذَٰلِكَ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ
يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَأَنَّ اللَّهَ بِكُلِّ
شَيْءٍ عَلِيمٌ
Hausa
Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yă sanya
wată Mai alfarma da hadaya da rătayőyin Allah Yă san abin da yake a cikin sammai
da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kőme, Masani ne.
|
Ayah 5:98 الأية
اعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ وَأَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Hausa
Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai găfara ne,
Mai jin ƙai.
|
Ayah 5:99 الأية
مَّا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا
تَكْتُمُونَ
Hausa
Băbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yană sanin abin da kuke
bayyanăwa da abin da kuke ɓőyewa.
|
Ayah 5:100 الأية
قُل لَّا يَسْتَوِي الْخَبِيثُ وَالطَّيِّبُ وَلَوْ أَعْجَبَكَ كَثْرَةُ الْخَبِيثِ
ۚ فَاتَّقُوا اللَّهَ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Hausa
Ka ce: "Mummuna da mai kyau bă su daidaita, kuma kő dă yawan mummuan yă bă ka
sha'awa. Sabőda haka ku bi Allah da taƙawa, yă ma'abuta hankula ko la'alla ză ku
ci nasara."
|
Ayah 5:101 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَسْأَلُوا عَنْ أَشْيَاءَ إِن تُبْدَ لَكُمْ
تَسُؤْكُمْ وَإِن تَسْأَلُوا عَنْهَا حِينَ يُنَزَّلُ الْقُرْآنُ تُبْدَ لَكُمْ
عَفَا اللَّهُ عَنْهَا ۗ وَاللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku
(hukuncinsu) su ɓăta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lőkacin da
ake saukar da Alƙur'ăni, ză a bayyana maku. Allah Yă yăfe laifi daga gare su,
Allah Mai găfara ne, Mai haƙuri.
|
Ayah 5:102 الأية
قَدْ سَأَلَهَا قَوْمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ثُمَّ أَصْبَحُوا بِهَا كَافِرِينَ
Hausa
Lalle ne wasu mutăne sun tambaye su daga gabăninku, sa'an nan kuma suka wăyi
gari da su sană kăfirai.
|
Ayah 5:103 الأية
مَا جَعَلَ اللَّهُ مِن بَحِيرَةٍ وَلَا سَائِبَةٍ وَلَا وَصِيلَةٍ وَلَا حَامٍ ۙ
وَلَٰكِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يَفْتَرُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ ۖ
وَأَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ
Hausa
Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka să'iba, kuma haka wasĩla, kuma
haka hămi, amma waɗanda suka kăfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi
yawansu bă su hankalta.
|
Ayah 5:104 الأية
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا إِلَىٰ مَا أَنزَلَ اللَّهُ وَإِلَى الرَّسُولِ
قَالُوا حَسْبُنَا مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا ۚ أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ
لَا يَعْلَمُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ
Hausa
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga
Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa."
Shin, kuma kő dă ubanninsu sun kasance bă su sanin kőme kuma bă su shiryuwa?
|
Ayah 5:105 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا عَلَيْكُمْ أَنفُسَكُمْ ۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن
ضَلَّ إِذَا اهْتَدَيْتُمْ ۚ إِلَى اللَّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم
بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Ku lazimci răyukanku, wanda ya ɓace bă zai cuce ku
ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makőmarku take gabă ɗaya. Sa'an nan Ya bă ku
lăbari ga abin da kuka kasance kună aikatăwa.
|
Ayah 5:106 الأية
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا شَهَادَةُ بَيْنِكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ
الْمَوْتُ حِينَ الْوَصِيَّةِ اثْنَانِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ أَوْ آخَرَانِ مِنْ
غَيْرِكُمْ إِنْ أَنتُمْ ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَأَصَابَتْكُم مُّصِيبَةُ
الْمَوْتِ ۚ تَحْبِسُونَهُمَا مِن بَعْدِ الصَّلَاةِ فَيُقْسِمَانِ بِاللَّهِ إِنِ
ارْتَبْتُمْ لَا نَشْتَرِي بِهِ ثَمَنًا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ ۙ وَلَا
نَكْتُمُ شَهَادَةَ اللَّهِ إِنَّا إِذًا لَّمِنَ الْآثِمِينَ
Hausa
Yă ku waɗanda suka yi ĩmăni! Shaidar tsakăninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku,
a lőkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ădalci daga gare ku, kő kuwa wasu biyu
daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta săme ku. Kună
tsare su daga băyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bă
mu sayen kuɗi da shi, kő dă ya kasance ma'abucin zumunta kuma bă mu ɓőye shaidar
Allah. Lalle ne mu, a lőkacin, haƙĩƙa, mună daga măsu zunubi."
|
Ayah 5:107 الأية
فَإِنْ عُثِرَ عَلَىٰ أَنَّهُمَا اسْتَحَقَّا إِثْمًا فَآخَرَانِ يَقُومَانِ
مَقَامَهُمَا مِنَ الَّذِينَ اسْتَحَقَّ عَلَيْهِمُ الْأَوْلَيَانِ فَيُقْسِمَانِ
بِاللَّهِ لَشَهَادَتُنَا أَحَقُّ مِن شَهَادَتِهِمَا وَمَا اعْتَدَيْنَا إِنَّا
إِذًا لَّمِنَ الظَّالِمِينَ
Hausa
To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu
matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutăne biyu mafiya cancanta,
sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga
shaidarsu, kuma ba mu yi zălunci ba. Lalle mu, a lőkacin haƙĩƙa, mună daga
azzălumai."
|
Ayah 5:108 الأية
ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يَأْتُوا بِالشَّهَادَةِ عَلَىٰ وَجْهِهَا أَوْ يَخَافُوا أَن
تُرَدَّ أَيْمَانٌ بَعْدَ أَيْمَانِهِمْ ۗ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاسْمَعُوا ۗ
وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Hausa
Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kő kuwa su yi tsőron a
tũre rantsuwőyi a băyan rantsuwőyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku
saurara, kuma Allah bă Ya shiryar da mutăne făsiƙai.
|
Ayah 5:109 الأية
يَوْمَ يَجْمَعُ اللَّهُ الرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَا أُجِبْتُمْ ۖ قَالُوا لَا
عِلْمَ لَنَا ۖ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Hausa
A ranar da Allah Yake tăra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?"
(ză) su ce: "Băbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."
|
Ayah 5:110 الأية
إِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ اذْكُرْ نِعْمَتِي عَلَيْكَ وَعَلَىٰ
وَالِدَتِكَ إِذْ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ الْقُدُسِ تُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ
وَكَهْلًا ۖ وَإِذْ عَلَّمْتُكَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ
وَالْإِنجِيلَ ۖ وَإِذْ تَخْلُقُ مِنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ بِإِذْنِي
فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيْرًا بِإِذْنِي ۖ وَتُبْرِئُ الْأَكْمَهَ
وَالْأَبْرَصَ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ تُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ بِإِذْنِي ۖ وَإِذْ
كَفَفْتُ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَنكَ إِذْ جِئْتَهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالَ
الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Hausa
A lőkacin da Allah Ya ce: "Yă Ĩsă ɗan Maryama!Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a
kan mahaifiyarka, a lőkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ˇudusi,kană yiwa mutăne
magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kană dattijo. Kuma a lőkacin da Na
sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lőkacin da kake yin
halitta daga lăkă kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta
sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kană warkar da haifaffen makaho da kuturu,
da izinĩNa, kuma a lőkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lőkacin
da Na kange Banĩ Isră'ĩla daga gare ka, a lőkacin da ka je musu da hujjőji
bayyanannu, sai waɗanda suka kăfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bă kőme ba
ne, făce sihiri bayyananne.'
|
Ayah 5:111 الأية
وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى الْحَوَارِيِّينَ أَنْ آمِنُوا بِي وَبِرَسُولِي قَالُوا
آمَنَّا وَاشْهَدْ بِأَنَّنَا مُسْلِمُونَ
Hausa
"Kuma a lőkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawăriyăwa cewa ku yi ĩmăni da Ni, kuma
da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmăni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, măsu
sallamăwa ne."
|
Ayah 5:112 الأية
إِذْ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ هَلْ يَسْتَطِيعُ رَبُّكَ
أَن يُنَزِّلَ عَلَيْنَا مَائِدَةً مِّنَ السَّمَاءِ ۖ قَالَ اتَّقُوا اللَّهَ إِن
كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa
A lőkacin da Hawarăyăwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yană
iyăwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samă?" (Ĩsă) Ya ce: "Ku bi Allah da
taƙawa idan kun kasance muminai."
|
Ayah 5:113 الأية
قَالُوا نُرِيدُ أَن نَّأْكُلَ مِنْهَا وَتَطْمَئِنَّ قُلُوبُنَا وَنَعْلَمَ أَن
قَدْ صَدَقْتَنَا وَنَكُونَ عَلَيْهَا مِنَ الشَّاهِدِينَ
Hausa
Suka ce: "Mună nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukătanmu su natsu kuma mu san
cewa lalle ne, kă yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga măsu shaida a kansa."
|
Ayah 5:114 الأية
قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ اللَّهُمَّ رَبَّنَا أَنزِلْ عَلَيْنَا مَائِدَةً
مِّنَ السَّمَاءِ تَكُونُ لَنَا عِيدًا لِّأَوَّلِنَا وَآخِرِنَا وَآيَةً مِّنكَ ۖ
وَارْزُقْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Hausa
Ĩsă ɗan Maryam ya ce: "Yă Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga
sama dőmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ăyă daga
gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin măsu azurtawa."
|
Ayah 5:115 الأية
قَالَ اللَّهُ إِنِّي مُنَزِّلُهَا عَلَيْكُمْ ۖ فَمَن يَكْفُرْ بَعْدُ مِنكُمْ
فَإِنِّي أُعَذِّبُهُ عَذَابًا لَّا أُعَذِّبُهُ أَحَدًا مِّنَ الْعَالَمِينَ
Hausa
Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya
kăfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Ină azabta shi, da wata azăba wadda bă Ni
azabta ta ga kőwa daga tălikai."
|
Ayah 5:116 الأية
وَإِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ
اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيْنِ مِن دُونِ اللَّهِ ۖ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا
يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ ۚ إِن كُنتُ قُلْتُهُ فَقَدْ
عَلِمْتَهُ ۚ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلَا أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ ۚ إِنَّكَ
أَنتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ
Hausa
Kuma a lőkacin da Allah Ya ce: "Yă Ĩsă ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa
mutăne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautăwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsă) Ya
ce: "Tsarkinka yă tabbata! Bă ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da băbu wani
hakki a gare ni. Idan nă kasance nă faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kană sanin
abin da ke a cikin raina, kuma bă ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne
Kai Masanin abubuwan fake ne."
|
Ayah 5:117 الأية
مَا قُلْتُ لَهُمْ إِلَّا مَا أَمَرْتَنِي بِهِ أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ رَبِّي
وَرَبَّكُمْ ۚ وَكُنتُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا مَّا دُمْتُ فِيهِمْ ۖ فَلَمَّا
تَوَفَّيْتَنِي كُنتَ أَنتَ الرَّقِيبَ عَلَيْهِمْ ۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ
شَهِيدٌ
Hausa
"Ban faɗa musu ba făce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah
Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nă kasance mai shaida a kansu matuƙar nă
dawwama a cikinsu, sa'an nan a lőkacin da Ka karɓi raina Kă kasance Kai ne mai
tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kőme, Halartacce ne.
|
|