First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
ق ۚ وَالْقُرْآنِ الْمَجِيدِ
Hausa
ˇ̃ . Ină rantsuwa da Alƙur'ăni Mai girma.
|
Ayah 50:2 الأية
بَلْ عَجِبُوا أَن جَاءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ الْكَافِرُونَ هَٰذَا
شَيْءٌ عَجِيبٌ
Hausa
Ă'a, sun yi mămăki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yă zo musu, sai kăfirai suka
ce: "Wannan wani abu ne mai ban mămăki."
|
Ayah 50:3 الأية
أَإِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ۖ ذَٰلِكَ رَجْعٌ بَعِيدٌ
Hausa
"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓăya (ză a kőmo da mu)? Waccan kőmowa
ce mai nĩsa."
|
Ayah 50:4 الأية
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ الْأَرْضُ مِنْهُمْ ۖ وَعِندَنَا كِتَابٌ حَفِيظٌ
Hausa
Lalle ne Mun san abin da ƙasă ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani
littăfi mai tsarẽwa.
|
Ayah 50:5 الأية
بَلْ كَذَّبُوا بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُمْ فَهُمْ فِي أَمْرٍ مَّرِيجٍ
Hausa
Ă'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lőkacin da ta je musu, sabőda haka sună a
cikin wani al'amari mai raurawa.
|
Ayah 50:6 الأية
أَفَلَمْ يَنظُرُوا إِلَى السَّمَاءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَاهَا
وَزَيَّنَّاهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ
Hausa
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samă a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma
Muka ƙawăce ta, kuma bă ta da waɗansu tsăgogi?
|
Ayah 50:7 الأية
وَالْأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن
كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ
Hausa
Da ƙasă, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwătsu a cikinta, kuma Mun tsirar,
a cikinta daga kőwane ma'auri mai ban sha'awa?
|
Ayah 50:8 الأية
تَبْصِرَةً وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ
Hausa
Dőmin wăyar da ido da tunătarwa ga dukan băwa mai tawakkali?
|
Ayah 50:9 الأية
وَنَزَّلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً مُّبَارَكًا فَأَنبَتْنَا بِهِ جَنَّاتٍ
وَحَبَّ الْحَصِيدِ
Hausa
Kuma Mun sassakar, daga samă ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi
(ităcen) lambuna da ƙwăya abin girbẽwa.
|
Ayah 50:10 الأية
وَالنَّخْلَ بَاسِقَاتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ
Hausa
Da ităcen dabĩno dőgăye, sună da'ya'yan ităce gunda măsu hauhawar jũna.
|
Ayah 50:11 الأية
رِّزْقًا لِّلْعِبَادِ ۖ وَأَحْيَيْنَا بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ
الْخُرُوجُ
Hausa
Dőmin arziki ga băyi, kuma Muka răyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar
wannan ne fitar daga kabari kake.
|
Ayah 50:12 الأية
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَابُ الرَّسِّ وَثَمُودُ
Hausa
Mutănen Nũhu sun ƙaryata, a gabăninsu (mutănen yanzu) da ma'abũta Rassi, da
Samũdăwa.
|
Ayah 50:13 الأية
وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَانُ لُوطٍ
Hausa
Da Ădăwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
|
Ayah 50:14 الأية
وَأَصْحَابُ الْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ ۚ كُلٌّ كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ
وَعِيدِ
Hausa
Da ma'abũta ƙunci da mutănen Tubba'u, kőwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai
ƙyacẽwaTa ta tabbata.
|
Ayah 50:15 الأية
أَفَعَيِينَا بِالْخَلْقِ الْأَوَّلِ ۚ بَلْ هُمْ فِي لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ
Hausa
Shin, to, Mun kăsa ne game da halittar farko? Ă'a, su sună a cikin rikici daga
halitta săbuwa.
|
Ayah 50:16 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِ نَفْسُهُ ۖ
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ الْوَرِيدِ
Hausa
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswăsi
da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
|
Ayah 50:17 الأية
إِذْ يَتَلَقَّى الْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ قَعِيدٌ
Hausa
A lőkacin da măsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dăma, kuma daga hagu akwai wani
(mală'ika) zaunanne.
|
Ayah 50:18 الأية
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ
Hausa
Bă ya lafazi da wata magana făce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
|
Ayah 50:19 الأية
وَجَاءَتْ سَكْرَةُ الْمَوْتِ بِالْحَقِّ ۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ
Hausa
Kuma măyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare
shi kană bijirẽwa.
|
Ayah 50:20 الأية
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْوَعِيدِ
Hausa
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
|
Ayah 50:21 الأية
وَجَاءَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَائِقٌ وَشَهِيدٌ
Hausa
Kuma kőwane rai ya zo, tăre da shi akwai mai kőra da mai shaida.
|
Ayah 50:22 الأية
لَّقَدْ كُنتَ فِي غَفْلَةٍ مِّنْ هَٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَاءَكَ فَبَصَرُكَ
الْيَوْمَ حَدِيدٌ
Hausa
(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To,
Mun kuranye maka rufinka, sabőda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
|
Ayah 50:23 الأية
وَقَالَ قَرِينُهُ هَٰذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ
Hausa
Kuma abőkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tăre da ni halarce."
|
Ayah 50:24 الأية
أَلْقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ
Hausa
(A ce wa Mală'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kăfirci, mai
tsaurin rai."
|
Ayah 50:25 الأية
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ
Hausa
"Mai yawan hanăwa ga alhẽri, mai zălunci, mai shakka."
|
Ayah 50:26 الأية
الَّذِي جَعَلَ مَعَ اللَّهِ إِلَٰهًا آخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِي الْعَذَابِ
الشَّدِيدِ
Hausa
"Wanda ya sanya, tăre da Allah wani abin bautăwa na dabam, sabőda haka kujẽfa
shi a cikin azăba mai tsanani."
|
Ayah 50:27 الأية
قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَٰكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ
Hausa
Abőkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya
kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
|
Ayah 50:28 الأية
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا لَدَيَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِالْوَعِيدِ
Hausa
Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhăli Na gabătar da ƙyacewa zuwa gare ku."
|
Ayah 50:29 الأية
مَا يُبَدَّلُ الْقَوْلُ لَدَيَّ وَمَا أَنَا بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ
Hausa
"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zălunci ba ga băyiNa."
|
Ayah 50:30 الأية
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ امْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ
Hausa
Rănar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani
ƙări?"
|
Ayah 50:31 الأية
وَأُزْلِفَتِ الْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ
Hausa
Kuma a kusantar dă Aljanna ga măsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
|
Ayah 50:32 الأية
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ
Hausa
"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kőmawa ga
Allah, mai tsarewar (umurninSa).
|
Ayah 50:33 الأية
مَّنْ خَشِيَ الرَّحْمَٰنَ بِالْغَيْبِ وَجَاءَ بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ
Hausa
"Wanda ya ji tsőron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai
tawakkali."
|
Ayah 50:34 الأية
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُلُودِ
Hausa
(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rănar dawwama."
|
Ayah 50:35 الأية
لَهُم مَّا يَشَاءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ
Hausa
Sună da abin da suke so a cikinta, kuma tăre da Mũ akwai ƙărin ni'ima,
|
Ayah 50:36 الأية
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا
فَنَقَّبُوا فِي الْبِلَادِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ
Hausa
Kuma da yawa Muka halakar, a gabăninsu, (mutănen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi,
(waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a
cikin ƙasăshe: 'Kő akwai wurin tsĩra'? ( Babu).
|
Ayah 50:37 الأية
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى السَّمْعَ
وَهُوَ شَهِيدٌ
Hausa
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunătarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare
shi, kő kuwa ya jẽfa saurăro, alhăli kuwa yană halarce (da hankalinsa).
|
Ayah 50:38 الأية
وَلَقَدْ خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ
أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ
Hausa
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasă da abin da ke a tsakăninsu, a
cikin kwănaki shida, alhăli wata'yar wahala ba ta shăfe Mu ba.
|
Ayah 50:39 الأية
فَاصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ
الشَّمْسِ وَقَبْلَ الْغُرُوبِ
Hausa
Sabőda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadă, kuma ka yi tasĩhi game da
gődẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabănin fitőwar rănă da gabănin
ɓacẽwarta.
|
Ayah 50:40 الأية
وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَارَ السُّجُودِ
Hausa
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da băyan sujada.
|
Ayah 50:41 الأية
وَاسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ الْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ
Hausa
Kuma ka saurăra a rănar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
|
Ayah 50:42 الأية
يَوْمَ يَسْمَعُونَ الصَّيْحَةَ بِالْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُرُوجِ
Hausa
Rănar da suke saurăron tsăwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
|
Ayah 50:43 الأية
إِنَّا نَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا الْمَصِيرُ
Hausa
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke răyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu
kawai ne makőmar take.
|
Ayah 50:44 الأية
يَوْمَ تَشَقَّقُ الْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ۚ ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ
Hausa
Rănar da ƙasă ke tsattsăgẽwa daga gare su, sună măsu gaggăwa. Wancan tărăwar
mutăne ne, mai sauƙi a gare Mu.
|
Ayah 50:45 الأية
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ ۖ فَذَكِّرْ
بِالْقُرْآنِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
Hausa
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bă ză ka zama mai tĩlasta su ba.
Sabőda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsőron ƙyacewaTa.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|