Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah.
Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon
yi ne.
Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke
bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin
ƙirãza.
Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji
bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka
kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah
wadãtacce ne, Gõdadde.
Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã
rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle
anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi
ne."
A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma
wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa
mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga
ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai
girma.
Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da
Allah,Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi
a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma
kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma
ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar
ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.