First Ayah 1 الأية الأوليبِسْم ِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
هَلْ أَتَىٰ عَلَى الْإِنسَانِ حِينٌ مِّنَ الدَّهْرِ لَمْ يَكُن شَيْئًا
مَّذْكُورًا
Hausa
Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake
ambata.
|
Ayah 76:2 الأية
إِنَّا خَلَقْنَا الْإِنسَانَ مِن نُّطْفَةٍ أَمْشَاجٍ نَّبْتَلِيهِ فَجَعَلْنَاهُ
سَمِيعًا بَصِيرًا
Hausa
Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi,
sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
|
Ayah 76:3 الأية
إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا
Hausa
Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma
ko ya zama mai kãfirci.
|
Ayah 76:4 الأية
إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ سَلَاسِلَ وَأَغْلَالًا وَسَعِيرًا
Hausa
Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
|
Ayah 76:5 الأية
إِنَّ الْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِن كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا
Hausa
Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance
kãfur ne.
|
Ayah 76:6 الأية
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا
Hausa
Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi
ɓuɓɓugarwa.
|
Ayah 76:7 الأية
يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا
Hausa
Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda
sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
|
Ayah 76:8 الأية
وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا
Hausa
Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da
kãmamme.
|
Ayah 76:9 الأية
إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمْ جَزَاءً وَلَا
شُكُورًا
Hausa
(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin
sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
|
Ayah 76:10 الأية
إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوْمًا عَبُوسًا قَمْطَرِيرًا
Hausa
"Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai
murtukẽwa."
|
Ayah 76:11 الأية
فَوَقَاهُمُ اللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ الْيَوْمِ وَلَقَّاهُمْ نَضْرَةً وَسُرُورًا
Hausa
Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin
huska da farin ciki,
|
Ayah 76:12 الأية
وَجَزَاهُم بِمَا صَبَرُوا جَنَّةً وَحَرِيرًا
Hausa
Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
|
Ayah 76:13 الأية
مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ ۖ لَا يَرَوْنَ فِيهَا شَمْسًا وَلَا
زَمْهَرِيرًا
Hausa
Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta,
kuma bã su ganin jaura.
|
Ayah 76:14 الأية
وَدَانِيَةً عَلَيْهِمْ ظِلَالُهَا وَذُلِّلَتْ قُطُوفُهَا تَذْلِيلًا
Hausa
Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
|
Ayah 76:15 الأية
وَيُطَافُ عَلَيْهِم بِآنِيَةٍ مِّن فِضَّةٍ وَأَكْوَابٍ كَانَتْ قَوَارِيرَا
Hausa
Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance
na ƙarau.
|
Ayah 76:16 الأية
قَوَارِيرَ مِن فِضَّةٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرًا
Hausa
¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
|
Ayah 76:17 الأية
وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا
Hausa
Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance
zanjabil ne.
|
Ayah 76:18 الأية
عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا
Hausa
Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
|
Ayah 76:19 الأية
وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيْتَهُمْ حَسِبْتَهُمْ
لُؤْلُؤًا مَّنثُورًا
Hausa
Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka
zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
|
Ayah 76:20 الأية
وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا
Hausa
Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
|
Ayah 76:21 الأية
عَالِيَهُمْ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضْرٌ وَإِسْتَبْرَقٌ ۖ وَحُلُّوا أَسَاوِرَ مِن
فِضَّةٍ وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا
Hausa
Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da
mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai
tsarkakẽwar (ciki).
|
Ayah 76:22 الأية
إِنَّ هَٰذَا كَانَ لَكُمْ جَزَاءً وَكَانَ سَعْيُكُم مَّشْكُورًا
Hausa
(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya
kasance abin gõdewa."
|
Ayah 76:23 الأية
إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ تَنزِيلًا
Hausa
Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
|
Ayah 76:24 الأية
فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعْ مِنْهُمْ آثِمًا أَوْ كَفُورًا
Hausa
Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu,
mai zunubi ko mai kãfirci.
|
Ayah 76:25 الأية
وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّكَ بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Hausa
Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
|
Ayah 76:26 الأية
وَمِنَ اللَّيْلِ فَاسْجُدْ لَهُ وَسَبِّحْهُ لَيْلًا طَوِيلًا
Hausa
Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
|
Ayah 76:27 الأية
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ يُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَاءَهُمْ يَوْمًا
ثَقِيلًا
Hausa
Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani
yini mai nauyi.
|
Ayah 76:28 الأية
نَّحْنُ خَلَقْنَاهُمْ وَشَدَدْنَا أَسْرَهُمْ ۖ وَإِذَا شِئْنَا بَدَّلْنَا
أَمْثَالَهُمْ تَبْدِيلًا
Hausa
Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu
musany su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
|
Ayah 76:29 الأية
إِنَّ هَٰذِهِ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ سَبِيلًا
Hausa
Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa
ga Ubangijinsa.
|
Ayah 76:30 الأية
وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا
حَكِيمًا
Hausa
Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai
hikima.
|
Ayah 76:31 الأية
يُدْخِلُ مَن يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ ۚ وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا
أَلِيمًا
Hausa
Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu
tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
|
©
EsinIslam.Com Designed & produced by The Awqaf London. Please pray for us
|