Muhawara Hausa
 



WAYE BAYA SON SAMUN RABO NA ALHERI..?
 
Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar Daga Sheikh Aliyu Said GamawaWAYE BAYA SON SAMUN RABO NA ALHERI..?Allah ya dora mana yin azumi a cikin dukkan watan Ramadan don mu samu rabo mai yawa na lada da kuma samun a kankare mana zunubbai da ‘yantuwa daga wuta, da sauran rabo na alheri mai yawa.Hakika barin ci da sha a cikin wunin watan Ramadan tsoron Allah ne da komawa gareshi, kuma aka kwadaidar da mu sallolin nafila na tarawihi, da yawaita sadaka da kyauta, da kokarin tilawar kur’ani, ga halartan tarukan karatu. Lallai cikin wannan akwai neman lada da kusaci ga Allah mai yawa.Hakanan aka umarce mu da nisantar miyagun aiyuka, rufe bakunan mu daga zagin wani ko aibata wassu ko jin waqe waqe da kade kade, da ashar ko amfanin da harshe ko gabobi a sabawa Allah.

Kuma yana daga cikin rabo mai yawa na lada da ake samu a watan Ramadan wajen nunka kyautatawa iyaye, iyalai, ‘yan uwa dangi, makwabta da sauran al’ummar da ke kusa da kai. Kuma ana son kowa ya sanya dukiyar sa a wannan wata cikin tallafawa mabukata, marayu, marasa gata da duk wani mai rauni mabukaci.Shugabanni kuna da dama mai yawa ta samun lada a wannan wata mai albarka na kusanto sauki da alheri ga alummar ku. Hakanan malamai ku kwadaitar da al’umma falalar sadaukar da kai wajen taimakawa jama’a a wannan wata mai albarka.Duk matakin da kake ciki mazan mu da matan mu pls mu himmatu wajen isar da alheri ga junan mu, ko da ta hanyar hada kai mu tara wani abu na gudumawa mu ciyar, mu tufatar da junan mu a wannan wata. Mu yawaita abin buda baki a masallatan mu, mu ciyar da masu rauni da abin sahur da buda baki.Shin wannan dama ta alheri mai yawa na ibada, da kyautatawa pls waye baya son ya samu!!!?

 Posted By Aka Sanya A Monday, September 30 @ 21:33:17 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar:
Ko Kasan Daga Ina Aka Gano Maukibi?


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar



"WAYE BAYA SON SAMUN RABO NA ALHERI..?" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com