Muhawara Hausa
 



DA’AWAR TAUHIDI ABIN ZAGI DA SUKA DA KUSHEWA
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
Daga Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

DA’AWAR TAUHIDI ABIN ZAGI DA SUKA DA KUSHEWA

Babu wani Annabin Allah da ya zo yana da’awar tauhidi face sai ya koyar da mutane cewar su bautawa Allah shi kadai kuma su nisanci dagutu.

Amsar mushirikai da kafirai da masu addinin gargajiya suke ba dukkan wani Annabi ciki har da Annabi Muhammad (SAW) shi ne ya na zagin Iyayensu da aibantashi.

Babu wani mutum da zai yi da’awar kiyaye tauhidi ta wurin kadaita Allah shi kadai face sai an zage shi, kalaman da ake fadawa wadancan Annabawa shi ma irin shi a ke fada musu, domin daman kafirci hanya daya ce.

Duk mutumin da zai ce a kadaita Allah shi kadai, farkon abin da zaka ji an ce shi ne ya raina su wane, ya zagi iyayenmu, ya kafirta malamanmu.

Babu wanda zai kira sunan wani musulmi ya ce shi kafiri ne.



Manzon Allah ya hana haka, ya ce ma duk wanda ya jifi wani da kafirci to dole zata fada kan daya.

Amma kuma shi manzon Allah SAW shi da kansa ya fada mana cewar musulmi zai iya yin aiki da zai fitar da shi daga musulunci. To irin wadancan ayyukan su ake cewar mai yin su yana aikin kafirci.

To yana da kyau ka tambayi kanka ko da kana da’awar Sunnah, shin ayyukan da nake yi akwai wanda manzon Allah ya ce mai yinsu kafiri ne, ko kuma ya kafirtaIdan babu sai ka godewa Allah idan kuma akwai kada ka ce kana jiran wani ko shawarar wani ka yi maza ka tuba tun rana bata fito daga yamma ba. (An rufe kofar tubaba ko kuma ka jika a cikin kabari)

Mu yi addinin Musulunci da akida da Ilimi da Hujja da koyarwar magabata na farko. Ba ra’ayi ba, ba don kaga wani aboki ko uba ko dan’uwa yana yi ba, ko kuma don a garinku aka fito da wannan akidar ba, ko dan garinku shine shugaba a wannan tafiya, ko kuma kana yinta ne domin ka baiwa wane haushi, ko domin ka sami kudi, ko dan kin ga mijinki yana yi, dukkan wata akida da za mu yi mu dauki littafai mu karanta bango zuwa bango, mu ji ya wannan akida take, me take kokarin koyar da mu, tana koyar da mu girmana wadansu mutane ne ko kuma tana kokari karantar da mu yadda zamu bautawa Allah shi kadai ne.

Ka da ka shagalu da yawan alkawarin aljanna ko karama da wasu su ke yiwa mabiyansu, domin karshen karama shi Manzon Allah, amma kuma kullum Sahabbai na tare da shi a Masallaci wurin Sallah, ba su dai na dukkan wata ibada da ya koyar da su ba har sai da suka koma gurin mahaliccinsu.

Hasalima ba su karbi wani zikiri ba da da idan suna yin shi ba sai sun yi sallah ba, ba su kuma karbi wani zikiri ba da idan suka yi shi zai rika cin ladaddakinsu Kada wani ya rude ka cewar akwai wani abu da idan ka yi shi zai baka darajar Annabawa da Sahabban Manzon Allah, da hakan gaskiya ne, da Sahabbai da Tabi’ai sun shagalu da wannan ibada.

Idan kai Musulmin gaskiya ne babban abin da zaka fi damuwa da shi shine 1) YA MANZON ALLAH YAYI KA ZA, 2) YA SAHABBANSA SUKA YI WANNAN IBADA, 3) YA MUTANEN NAN WADANDA YACE AYI KOYI DA SU SUKA 4) YI YA KUMA WADANDA SHI MANZON YA CE LOKACINSU YA FI KOWANE LOKACI ALBARKA SUNA YI.

Ina muku rantsuwa da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Allah babu wanda zai yi ibada da wannan matakai guda hudu face ya tsira ya samu babban rabo.

Allah ka tsarkake mana niyyar m


 Posted By Aka Sanya A Thursday, November 07 @ 18:04:03 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai



"DA’AWAR TAUHIDI ABIN ZAGI DA SUKA DA KUSHEWA" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam ReligiĆ³n del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам ReligiĆ£o do IslĆ£ イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com