Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Al'Adun Musulmi Da Darajoji
[ Al'Adun Musulmi Da Darajoji ]

·Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
·Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
·Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
·Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
·Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Jami’an Tsaro Suka Kashe Sheikh Albani —Zakzaky (Leadership Hausa)
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
Daga Jibwis Ta Nigeria

Jami’an Tsaro Suka Kashe Sheikh Albani —Zakzaky (Leadership Hausa)


Mako guda bayan wasu mahara da ba a san ko su waye ba, sun harbe Malamin addinin Musuluncin nan da ke Zariya, Shaikh Awwal Albani, matarsa da dansa, sai kuma ga shi, ’yan Shi’a, sun yi zargin ana yunkurin harbe Shugabansu, Shaikh Ibraheem Yakoub Zakzaky.A cikin wani jawabi da ya gabatar ga almajiransa a wajen karatun da ya saba gabatarwa kowace ranar Litinin a cibiyarsu da ake kira Husainiyya Bakiyyatullah da ke Sokoto Road Sabon Garin Zariya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya yi zargin an tura jami’an tsaron ne don su kai masa hari a gida da yake kwana ranar Asabar.“Waccan Asabar din kun yi kisan kai a wajen Gaskiya, kuma wanna Asabar din an gan ku a Gyallesu. Wa kuka zo kashewa ke nan? Ai ma ba sai an ba ka bayani ba, da ganin su a Gyallesu ka san sun zo kashe wani ne”, in ji Shaikh Zakzaky a jawabinsa nasa.A daren ranar Asabar ne aka ga wani gungun jami’an tsaro sun kakkafa shingayen suna binciken ababen hawa a daidai hanyar shiga Gyallesu, Zariya, Unguwar da Shaikh Zakzaky ke zama da iyalansa. Nan take almajiransa suka hallara a wajen.Wasu da muka zanta da su a wajen sun yi zargin jami’an tsaron sun je wajen da wata manufa. Yayin da wasu suka yi zargin jami’an tsaron sun zo binne makamai ne, wadanda za a nunawa duniya a ce da su aka kashe Shaikh Awwal Albani, wasu kuwa cewa suka yi an zo kamawa ko kuma kashe Shaikh Zakzaky ne.“Ba mu san abin da ya kawo su a daidai wannan lokacin ba, shi ya sa muka kasance a nan domin duk abin da za a yi ya zama a kan idonmu aka yi shi”, in ji daya daga cikin daliban Malamin a lokacin yake zantawa da Wakilinmu ta wayar GSM.Wata majiya mai tushe da ke da alaka da jami’an tsaro ta tsegunta mana cewa an kawo su Unguwar Gyallesu a daidai wannan lokacin ne, saboda wani rahoton sirri da suke da shi na yunkurin kai wa Madugun na ’yan Shi’a hari da ake tsammanin wasu gungun mutane za su yi.A cikin jawabin nasa, Shaikh Zakzaky ya nanata cewa suna da masaniyya game da shirin da ake da shi na kai masu hari a ranar Litinin ko Laraba; ranakun da ya saba fita don gabatar da Tafsiri da kuma karantun littafin Nahjul Balagha. “Sun dai ce za su yi Litinin, idan ba su yi ba ko wata rana idan an tashi karatu daga Husainiyyah, ko in za a zo Husainiyya za su bude wuta”, In ji shi

Wannan dai ba shi ne karon farko da almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka yi zargin ana yunkurin kashe Malamin nasu ba. Wata majiya ta shaida wa Wakilinmu cewa wannan shi ne karo na 24 a cikin shekaru uku da aka yi yunkurin kashe shi.

Sun yi zargin cewa hatta tarurrukan Maulidin Manzon Allah (SWA) da suka gabatar a garuruwan Kano da Zariya, sai da aka shirya auka masu. Kuma da suka yi Tattaki a lokacin juyayin kwanaki 40 Ashura da suka yi a watanni biyu da suka gabata sun zargin an shirya auka masu.“Saboda haka wannan ma da suka ce za su zo su zuba makamai a Gyallesu ba don mun gan su ba, ba za mu fada ba (don ba magana ba ne). To amma sai suka yi yunkurin yi. Sun sha yin 'attempt’, kuma mukan wuce, kuma ba ma fada. Ko a wani 'Usulubil Wahda’ wata ranar Juma’a lallai sun ajiye masu harbi, kuma mun zo ko magana ma ba mu yi ba”, in ji shi.Shaikh Zakzaky, wanda ya nisanta kansu daga duk wani zargi da wasu suke yi masu na hannu a kan kashe Shaikh Awwal Albani, ya tabbatar da cewa a iya saninsu babu wata rashin jituwa da ta taba shiga a tsakaninsu da Marigayin har zuwa lokacin da wasu maharan da ba a san ko su waye ba suka kashe shi; “Iyakar saninmu Albani har suka kashe shi bai taba kashe kazarmu ba, ko ya fasa kwanmu ba. Ko kuna da labarin ya taba kashe mana kaza? To ga wanda suka bude mana wuta rana tsaka mun san su, wa muka kashe a cikin su?”

Acewarsa, almajiran Albani sun san wadanda suka yi kisan, amma saboda tsoro ba za su iya fitowa fili su fada ba, don haka “ba tare da tsoron duk wani mahaluki ba, mun fadi cewa gwamnat ce ta kashe Albani”. In ji shi.

Ya jaddada cewa su ba sa rike kowa a zuciya don ya yi masu wani abu da ba daidai ba; “To inda mu masu kisan kai ne ai da mun kashe wadanda suka bude mana wuta rana tsaka, amma har muna hannu da su, wadanda suka ba da umurnin aka bude wuta a kanmu rana tsaka mun san su, sun san mun sani, amma har muna hannu da su”.Shaikh Ibraheem Zakzaky ya nesanta Shi’a daga duk wani nau’i na ayyukan ta’addanci domin a cewarsa, su Shi’a suna da ka’ida kafin su yi duk wani abu “a wajen Shi’a babu yadda za a yi ka mari mutum ba da sai izinin Mujtahidi (Ayatullahi) ba, balle kuma ka auka wa mutane da yaki. Saboda haka, horo wanda za a ji zafi 'ittifakan’ ba a yi sai da izinin Mujtahidi, ballantana kisa. Horo wanda za a ji zafi ko da duka ne, mutum ba zai yi ba sai da izinin Mujtahidi, wannan a duk duniyar Shi’a haka yake ba a sabani, babu ra’ayi na biyu”.A baya dai garin Zariya ya kasance mai zaman lafiya da aminci ga bako ga dan gari, inda ya kasance Cibiyar ilimi ta Nijeriya, amma yanzu bisa ga dukkanin alamu an jefa tsoro da razani a zukatan mazaunansa; inda jama’a daban-daban ke tambayar cewa “ko wane ne zai iya bugan kirji ya ce zai amfana da wannan rashin tabbas da wasu ke neman jefa garin a ciki?”.

 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, April 27 @ 05:58:28 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Jami’an Tsaro Suka Kashe Sheikh Albani —Zakzaky (Leadership Hausa)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: