Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Ku karbi gaskiya ko daga wa ta fito (1)
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi Daga Imam Murtada Muhammad Gusau

Ku karbi gaskiya ko daga wa ta fito (1)

Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya ce a cikin littafinSa Mai girma cewa: ''An la'ani wadanda suka kafirta daga Bani Isra'il a kan harshen Dawuda da Isa dan Maryama. Wannan kuwa saboda sabon (zunubi) da suke yi, kuma sun kasance suna ta'adi (ketare iyaka), sun kasance ba sa hana juna aikata mummunan aiki, wanda suka aikata. Hakika, abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.'' (Ma'ida:78-79).

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), wanda ya fada a ingantaccen Hadisinsa, cewa: ''Ka taimaki dan uwanka, azzalumi ko wanda ake zalunta. Sai sahabbai suka ce: ''Ya Manzon Allah, idan an zalunci dan uwanmu mun san ta yadda za mu taimake shi (mu kwato masa hakkinsa), to yaya za mu taimake shi idan shi ne azzalumi?'' Sai Annabi (SAW) ya ce: ''Ku hana shi zaluncin, shi ne kun taimake shi.''

'Yan uwa Musulmi! Al'amarin umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki, alama ce mai girma daga cikin alamonin Musulunci. Kuma turke ne mai karfi daga turakun al'ummar da ke kan gaskiya. Nassosi masu yawa sun tabbatar da haka, tarihi ya tabbatar da haka, kuma halin da muka tsinci kawunanmu a ciki a yau a kasar nan ya tabbatar da cewa lallai wannan aiki wajibi ne a cikin al'umma.

Al'umma a yau tana bukatar rayar da wannan tafarki na umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummuna, tare da karfafa shi. Domin ta wannan ne kadai za a iya karkade kurar da ta lullube wannan al'umma, kuma ta yi mummunan tasiri a kanta. Sanadiyyar haka sai aka wayi gari ana yi wa wannan al'umma makirci iri-iri, ciki da wajenta. Alhali duk mai hankali ya san cewa ba wani abu ne ya jefa mu cikin wannan hali ba, illa nisan da muka yi daga tafarkin Allah da addininSa.

Umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, shi ne tsantsar aikin Annabawa da Manzannin Allah. Kai, shi ne ma madarar tafarkinsu. Allah bai aiko Annabawa da Manzanni ba, face su umarci mutane su aikata kyakkyawan aiki, kuma su hana su aikata mummuna. Hadisi ya tabbata (ingantacce) daga Abdullahi dan Mas'ud (Allah Ya kara yardarSa a gare shi), ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Farkon abin da ya fara jawo wa Bani Isra'ila kaskanci shi ne: ''Mutum zai kasance dan uwansa yana aikata ba daidai ba, yana yin abu maras kyau, idan sun hadu zai yi masa nasiha wane ka ji tsoron Allah ka bar wannan abin ba ya da kyau, haramun ne, shi kuma sai ya ki dainawa. Gobe idan sun hadu, wannan mutum da ya yi masa nasiha zai zauna da shi su ci abinci tare su sha tare, sai Allah Ya jefa kiyayyar juna a zukatansu.'' Sannan sai Annabi (SAW) ya ce: ''Wallahi ko dai ku yi umarni da kyakkyawa, ku yi hani daga mummuna, ku kama hannun azzalumi ku hana shi zaluncin, ku dora shi a kan gaskiya, ko ku ga abin da ba ku so.''

Duk al'ummar da ta bar wannan aiki na umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, to ta halaka. A duk lokacin da mutane saboda kwadayi ko tsoro ko kabilanci ko bangaranci ko bambancin addini ya sa suka yi watsi da gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da adalci a bayan kasa, to, wallahi sun gama yawo, sai wasu ba su ba, kuma sai buzunsu. 

Saboda haka dole ne mu tashi tsaye don ganin cewa al'umma ta koma kan gaskiya, karama da izza sun dawo ga wannan al'umma, daukaka da kwarjini sun dawo ga wannan al'umma. Jagoranci da shugabanci nagari sun dawo ga wannan al'umma, adalci da hadin kai sun dawo ga wannan al'umma, domin samun ci gaba da zaman lafiya a ko'ina. Wannan ba zai taba samuwa ba, dole sai an yi gwagwarmaya domin tabbatar da shugabanci nagari da zai rungumi kowa da kowa bisa daidaito da adalci. Duk yadda ake son al'umma ta gyaru, wallahi idan babu shugabanci nagari ba zai yiwuwa ba.

Ranar 2 ga watan Disamba da muke ciki, tsohon Shugaban kasar na mulkin soja da farar hula, kuma tsohon shugaban Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar PDP, Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wata wasika mai tarihi zuwa ga Shugaban kasa mai ci, wato Dokta Goodluck Ebele Jonathan inda ya zargi Jonathan da abubuwa masu yawa da suka hada da nuna sakaci kan harkar tsaro da goyon bayan ta'addanci da 'yan ta'adda da rusa tattalin arziki da bata ci gaban kasa da hadin kan ta da raba kan al'umma da rashin iya mulki da cin hanci da rashawa da nuna kabilanci da kasa cika alkawuran da yayi wa 'yan Najeriya da hada husuma a tsakanin Musulmi da Kirista da sauransu. 
Wannan wasika mai shafi 18, kuma tana dauke da kalmomi dubu bakwai da 584. Kuma kafofin watsa labarai na yanar gizo da jaridu da mujallu na gida da waje duk sun buga kwafin wannan wasika ta Obasanjo.

A takaice dai bayan bayyanar wannan wasika, maganganu da rubuce-rubuce sun biyo baya. Kama daga masu goyon baya zuwa masu sukar tsohon Shugaban kasa Obasanjo. Masu goyon bayansa suna yaba masa domin jarunta da gwarzontaka da jajirewarsa a kan fada wa Jonathan gaskiya game da abin da ke tafiya a gwamnatinsa, wanda wannan abu ne a fili da duk dan Najeriya ya san da shi, kuma yake shaida a kansa. Marasa tsoron Allah ne kawai za su yi musu a kan wannan. Wadanda ke sukar Olusegun Obasanjo kuwa, suna ganin bai yi daidai ba da ya bayyana wasikar a kafafen watsa labarai. Sun manta cewa Obasanjo ya bayyana wa duniya cewa, ya rubuta wasika da dama kuma ba alamun gyara. Sannan suna cewa yaushe Obasanjo ya zama mutumin kirki da har zai bayyana laifin wani, ko ya yi wa wani nasiha? Wasu kuwa cewa suke yi, ai duk abin da Jonathan ya yi ba laifin kowa ba ne illa Obansanjo, domin shi ne ya kawo shi. 

Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus'ab)
Shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
08038289761
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, May 31 @ 23:38:05 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"Ku karbi gaskiya ko daga wa ta fito (1)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: