Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (3)
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi Daga Salihu Makera

Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (3)

dan Gwamna mai alfahari:

Wata rana Amirul Muminina Umar dan Khaddabi yana zaune a masallaci, sai wani mutumin Masar ya shiga ya yi masa sallama kamar yadda aka saba: ‘Assalamu alaikum' ya ce: Umar (RA) ya amsa ‘Wa alaikumus salam.' Sai bakon nan ya nemi wuri ya zauna kusa da Umar (RA) sannan ya ce: ''Idan na gabatar da kukana gabanka, ina da tabbacin samun adalci da kuma kariya?'' Umar (Allah Ya kara masa yarda) ya ce: ''kwarai kuwa na yi maka alkawarin samun adalci da kuma ba ka kariya. Amma ka gaya min, me yake damunka?''

Sai mutumin Masar din nan ya ce: Gwamnanka a Masar Amru bin Al-As yana da wata dabi' a ta shirya gasar tseren dawaki. Kuma ka san yadda muke son dawaki a Masar kamar yadda lamarin yake a kasashen Larabawa, da damanmu muna da dawaki masu kyau. Kowa yana son a ce ya shiga gasar nan, kuma akan dauki kwanaki ana shirye-shirye don wannan gasa ta musamman mai muhimmanci. To ni ma ina da wani doki mai kyau da karfi, kuma ina da kyakkyawar fata in lashe gasar nan.''

Wannan mutumin Masar ya ci gaba da bayyana wa Amirul Muminina Umar dan Khaddabi abin da ya gudana kamar haka: ''Muhammad (dan Gwamnan Masar) Amru ya shiga gasar tseren dawakin. To da aka fara gasar duk lokacin da dawakan suka kewayo ta gabanmu sai mu rika lekawa mu ga wanda ke gaba. Sai na hango dokina wanda aka bari a baya a farkon gasar yana kara gudu yana kamo sauran yana kokarin wuce su musamman da aka shiga zagaye na biyu. Lokacin da aka shiga zagaye na uku lokacin da dawaki suka kusato inda Muhammad yake zaune sai na ji yana fadi da babbar murya ''Dokina ne a kan gaba! Dokina ne zai lashe gasar!''

Bamisire ya ci gaba da cewa: ''Jimawa kadan suka iso wurina sai na ga ba dokin Muhammad ne a gaba ba, dokina ne ke kokarin lashe gasar. Kada ka ji irin murnar da na ji. Na daka tsalle na fara murna ina zuga dokina ya kara gudu na ce: Na rantse da Ubangijin Ka'aba wannan dokina ne a kan gaba. Kwatsam sai Muhammad ba tare da wata sanarwa bay a iso gare ne da bulala ya rika zane ni iyakar karfinsa yana cewa: ''Karbi wannan dan talakawa karbi wannan. Kada ka manta ni dan babban mutum ne kai kuwa ba komai ba ne wofin banza.''

Ya kara da cewa ''Abin mamaki ko ka san abin da ya faru da ni a bayan haka ya Amirul Muminina? Sai aka jefa ni kurkuku… kuma ba don komai ba, sai domin Amru ya samu labarin abin da ya faru, don haka nake jin tsoro na zo gare ka domin neman kariya da mika kukana kan wannan aika-aika na dansa. A can an jefa ni a kurkuku ba domin taimakon wani daga cikin masu tsaron kurkukun ba da ya ji abin da ya faru ba zan iya zuwa nan na nemi taimakonka ba.''

Da Umar (RA) ya ji wannan labara sai ya yi kasake kamar ruwa ya ci shi. Can sai ya ce: ''Zauna dan uwana. Ka zauna tare da mu.'' Sannan Umar (RA) ya rubuta takarda zuwa ga Gwamnan Masar yana umartarsa ya zo Madina maza-maza tare da dansa Muhammad. Shi kuma mutumin Masar din aka ce ya zauna har sai sun zo.

Lokacin da Amru ya karbi wannan wasika sai ya damu. Ya kira dansa ya tambaye shi me ya aikata. ''Ko ka yi wani laifi ne?'' Ya tambaye shi. ''A'a na rantse ban yi komai ba,'' inji saurayin.

''In haka ne me zai sa Umar (RA) ya neme mu ni da kai? Babu shakka akwai abin da ka aikata,'' inji Amru yana nuna dansa da yatsa yana ja masa kunne.

Sai Amru da dansa Muhammad suka kama hanyar Madina, bayan doguwar tafiya suka isa Masallacin Annabi (SAW) a Madina. Jama'a ta taru lokacin da aka ji labarin Amru yana kan hanya, kuma mutane da dama suka rika jinjina ga babban janar a lokacin da yake wucewa ta wurinsu, shi kuma yana amsa gaisuwarsu. Yana sanye da tufafinsa masu tsada kamar yadda ya saba, kuma dansa mai alfaharin nan yana biye da shi.

Yana zuwa ba tare da bata lokaci ba Umar (RA) ya ce ''Ina danka?'' Nan da nan Muhammad ya leko ta bayan mahaifinsa Amru. Sai ya ce: ''Ina mutumin Masar din nan?'' Ya ce: ''Ga ni ya Amirul Muminina!''

Sai Umar ya mika masa bulala ya ce: Doki wannan saurayi dan babban mutum kamar yadda ya doke ka.''

Sai mutumin Masar ya dauki bulala ya rika tsala masa, Umar yana kada kai alamar jin dadi, yana cewa, ''Ya yi kyau… doki dan babban mutum.''

Bayan wanin lokaci Bamisire ya tsaya da kansa.

Sannan Umar ya waiwaya wajen Amru ya ce: ''Yaushe kuka mayar da mutane bayi, bayan Allah Ya halicce su 'ya'ya?'' Ya yi masa gargadi mai tsanani, sannan ya sallame su.

Daga wadannan labarai biyu da suka gabata, za mu fahimci wani babban al'amari da ya bambanta Musulunci da sauran addinai da tsare-tsare na dan Adam wajen tabbatar da adalci da kuma barin kofar shugabannin a bude ga talakawa domin su isa gare su, su isar da kuka ko korafi game da shugabannin na kasa da su.

Misali a labarin farko, jingina kalmar munafunci Gwamna Amru ya yi ga talakansa, kuma wannan talakan ya ga an yi masa iyakar cin mutunci, sannan saboda tabbacin zai samu adalci ya garzaya har Madina daga Masar ya kai kuka kuma aka yi wa Gwamnan hukunci kamar yadda Musulunci ya tanada na ya yi wa Gwamnan nan bulala 40 da kansa na yi masa kazafi da bata suna. Kuma cin kaskanci Gwamnan nan ya rusuna a gaban wannan talaka ga dubban jama'a suna kallo ya cire rawaninsa ya mika wa wannan talaka bulala ya ce ya zartar da wannan hukunci! Shin wane addini ko tsari ne yake da irin wannan koyarwa? Sannan a labari na biyu dan wannan Gwamna ne ya yi bulala ga wani dan talakawa da dokinsa ya tsere na dan Gwamna a lokacin gasar sukuwar dawaki, nan ma wannan talaka ya garzaya har Madina don neman adalci, kuma a karshe ya samu adalcin. Musamman Amirul Muminina Umar dan Khaddabi (RA) ya kira Gwamnan da dansa har Madina sannan ya hukunta dan a gaban mahaifinsa kuma ya ja masa kunne.

Mu tsaya mu tambayi kawunanmu a matsayinmu na Musulmi da muke son shiga Aljanna tare da wadancan magabata, shugabanninmu na yanzu suna yin irin wannan adalci a tsakanin mabiyansu? Shin daga kansila zuwa Shugaban kasa daga mai unguwa zuwa sarki daga lebura zuwa heluma daga masinja zuwa kan shugaban ma'aikata, wane ne cikinsu zai fadi wata mummunar magana ga na kasa da shi a ce an iya zuwa gaba an samu adalcin da na kasa zai ji cewa shi mutum ne? Shin kofofin shugabanninmu na yanzu a bude suke ga na kasa ya isar da kukansa? Shin idan dan ‘babban mutum' ya aikata laifi hukunta shi ake yi ko kokarin kubutar da shi? Me muka lura da shi a labarin farko na fiyayyen halitta (SAW) cewa da Fatima za ta yi sata zai sa a yanke mata hannu!
 
 
 Posted By Aka Sanya A Monday, June 01 @ 01:22:59 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (3)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: