Muhawara Hausa
 



RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 06
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Daga Sheikh Faisal Bn Ali Al- Ba'adani Fassarar:

RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 06

Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Mal. Aliyu Rufa'i Gusau.

RAYUWAR ANANBI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA TSAKANINSA DA UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN RAMALANA (2)

Babban abin da ya kamata musulmi ya lura da shi a cikin wadannan nassosa da suka gabata, shi ne kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na matuqar kwadayin jinkirta yin sahur da kuma gaggauta yin budin baki, tare da yin su da duk abin da ya sawwaqa gare shi Sallallahu Alaihi Wasallama komai qanqantarsa. Kamar yadda Anas Raliyallahu Anhu ke cewa: ''Ban taba ganin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi Sallar magariba kafin ya buda baki ba; ko da kuwa da kurbin ruwa guda ne sai ya yi.'' Haka kuma Abdullahi dan Amru Raliyallahu Anhu ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ''Ku yi qoqari ku yi sahur ko da da kurbin ruwa guda ne.'' Kaga kenan, ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi amfani ne da duk abin da ya tari gabansa, don ya tabbatar da ganin ya ba wa wannan ibada haqqinta, ba tare da ya tsaya wata inda-inda ba. Don ya qara samun fada ga Ubangijinsa mai girma da xaukaka.

Yin nazarin wadannan bayanai da suka gabata, na tabbatar wa mai karatu da cewa, abin da wasu musulmi ke yi yau, na yin ''tazarce,'' ko yin sahur tun talatainin dare bai dace ba, don ya saba wa koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, da abin da gaba dayan Sahabbansa ke a kai bayan sa. Kuma hakan na cutar da rayuwa matuqa. Amru dan Maimun ya bayar da labarin cewa: ''Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sun fi kowa gaggauta budin baki da jinkirta sahur.

Kuma hakan na qara tabbatar da cewa, abin da wasu mutanen ke yi a yau, na dibar girki da shan gara a yi maqil lokacin sahur ko budin baki, shi ma ya saba ma wannan koyarwa ta Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa irin haka na haifar da kasala da dibgewar jiki, ta yadda mutum ba zai sami sukunin yawaita ibada a wannan wata mai albarka ba. To, fita batun ma duk wannan matsala. Babban bala'i duk, bai fi irin wannan gara da ake shiryawa ta zama an shirya ta ne da dukiya ta haramun ba. Mutum yana ji yana gani ya yi sahur da haramiya ya kuma bude baki da ita, wal iyazu billahi. Allah shi kiyashe mu.

Abin na da matuqar ban mamaki, ganin irin yadda musulmi ke jefa kansa cikin halaka; yana ganin hanyar Aljanna ya kama ta Wuta. Maimakon ya dage a kan cin halaliya da yawaita ayyukan alheri da da'a a cikin wannan wata, sai ya buge ga abubuwan da za su kawai nisanta shi daga rahamar Allah; su tara masa zunubbai su kuma cika shi da rashin lafiya, irin wadda a qarshen rayuwarsa ba abin da zai yi sai nadama.

Da wannan muke kiran duk musulmi mai hankali, da ya yi qoqari ya ja lizzamin zuciyarsa, ya yi mata dabaibayi, ya rage kwadayi da zama kamar dabba. Ya tuna fa rayuwar duniya mai qarewa ce, kuma yau da gobe ba ta bar komai ba. Musulmi na gari kuwa shi ne wanda ya gudanar da rayuwarsa bisa koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama gwargwadon hali. Kuma kamar yadda muka fada a baya, ba abin da qawace- qawacen duniya da son jin dadi ke haifarwa baya ga rafkana. Saboda haka a rage kwadayi, a kuma riqe ayyukan da'a da alheri, tare da yawaita su, musamman a cikin watan Azumin Ramalana.

Wasu Sigogi:

Tsakanin sahur da budin baki kuma Azumin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na Ramalana ya qunshi wasu sigogi kamar haka:

i- Addu'a: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi addu'a a duk lokacin da zai yi budin baki. Dan Umar Raliyallahu Anhu ya ce: ''A duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi budin baki yakan ce:

''Qishirwa kuma sai ta gobe, ga kuma abinci za mu ci, Allah ka ba mu ladar da ke ciki.''

Amma abin takaici a yau, qanshin abinci ya sa mutane da yawa, musamman uwaye mata mantawa da su yi addu'a, a lokacin budin baki.

Alhali kuwa babu wata addu'a da musulmi zai yi a wannan lokaci face Allah Subhanahu Wa Ta'ala ya karbe ta. Muna fatar za a kula a gyara.

ii- Asawaki: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi asawaki a lokacin Azumi. An riwaiyo daga Amiru dan Rabi'ata Raliyallahu Anhu wanda ya ce: ''Na ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ban san iyaka ba yana asawaki, yana kuma dauke da Azumi.''

Ba mamaki ko kadan a kan haka.

Domin kuwa ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwadaitar da musulmi yin asawaki kusan kodayaushe, ta hanyar nuna masu falalarsa, yana mai cewa:

''Asawaki na tsaftace baki ya kuma sa mutum ya sami yardar Ubangiji.''

Sannan kuma shi ya ce: ''Haqiqa an umurce ni da yin asawaki, har na zaci sai an saukar mani da aya ko wani wahayi a kansa.''

Wadannan nassosa da suka gabata, da wadanda za su biyo baya, na nuna cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi asawaki a kowane lokaci a cikin yini, ba tare da kebancewa ba, balle ya qi yin sa da marece. Shi da kansa Sallallahu Alaihi Wasallama yana cewa: ''Ba don kada in tsananta wa al'ummata ba, da na umurce su da yin asawaki a lokacin kowace arwalla.'' Ya kuma ce a wani Hadisin: ''Ba don kada in tsananta wa muminai ba da na umurce su da yin asawaki a lokacin kowace Sallah.''

Malam Ibnu Abdilbarri ya ce:

''Wannnan Hadisi na nuna halaccin yin asawaki a kowane lokaci. Saboda cewa Annabi ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama, ''……a lokacin kowace arwalla da kowace Sallah.'' Sallah kuwa na iya kamawa a kowane lokaci, ko da safe ko da rana ko da marece.''

Shi kuwa Imamul-Buhari qarfafa wannan magana ya yi da cewa:

''Wannan halacci na yin asawaki a kowane lokaci, ya hada har da mai Azumi.'' Bayansa kuma Ibnu Huzaima ya qara da cewa: ''Hadissan na nuna cewa yin asawaki ga mai Azumi a lokacin kowace Sallah abu ne da ke da falala kamar yadda yake ga wanda ba mai Azumi ba.'' Saboda haka ya kamata kowane musulmi ya kiyaye wannan Sunnah ta Shugaban Manzanni Sallallahu Alaihi Wasallama, saboda lada da fai'da da ke cikinta ba su qidayuwa.

Hadisin da ya tabbata Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a cikinsa: ''Warin bakin mai Azumi ya fi soyuwa a wurin Allah, a kan qanshin turaren Almiski.'' ba zai tayar da wancan hukuncin ba. Domin kuwa ma'anar Hadisin ita ce bayyana cewa, wannan doyi na bakin mai Azumi, wanda mutane ke qyama, yana da irin wannan matsayi a wurin Allah Subhanahu Wa Ta'ala ta yadda har qanshinsa a wurinsa ya kere na almiski, turaren da ko a cikin mutane sai wane da wane. Kuma doyin bakin na mai Azumi ya sami wannan matsayi ne a wurin Allah Subhanahu Wa Ta'ala saboda kasancewarsa sakamakon biyayya ga umurninsa da neman kusanta gare shi. Ba wai shi kansa doyin ne ke da waccan daraja da daukaka ba, balle hakan ta sa mutum qoqarin samarwa da tabbatar da shi.

Iyakar abin da wannan Hadisi ke nufi ke nan. Allah kuma shi ne mafi sani.

Sannan kuma babu wani nassi ingantacce da ke nuna cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya banbanta danye da busasshen itace a cikin yin asawaki. Saboda haka da yawan su, suka dauki nau'o'an itacen daya, har Malam Ibnu Sirina ke cewa wani mutun: ''Babu laifi a cikin yin asawaki da danyen itace.'' Mutumin ya ce masa: ''Tsumagiyar dabino ce fa, kuma tana da dandano.'' Malamin ya karba masa da cewa: ''To, ai ruwa na da dandano amma kuma kake kurkura shi.'' Shi kuwa Malam Ibnu Ulayyata ya ce:'' Yin asawaki Sunnah ne ga mai Azumi, kamar yadda yake Sunnah ga wanda ba Azumin yake yi ba. Kuma danyen itace da busasshe duka daya ne a ciki.''

 Posted By Aka Sanya A Thursday, June 18 @ 05:13:51 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen



"RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 06" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com