Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
[ Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc ]

·Musulmi da farfagandar makiya
·Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)
·Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)
·Giba da illolinta (1)
·Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)
·Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)
·Tukuici ga mai azumi (4)
·Tukuici ga mai azumi (3)
·Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 07
 
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga Salihu Is'hak Makera

Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 07

Daga wannan za mu fahimci cewa addinin Musulunci yana ba ran dan Adam kariya fiye da kowane addini ko tsarin rayuwa na dan Adam.

Kuma babbar mai tsare rayuka a kowane lokaci ita ce hukuma ko gwamnati. Idan ta ce ita ballagaza ce babu ruwanta da tsare addinin mutane, ko kowa ya je ya yi addinin da yake so, ko ya ma ki bin addinin gaba daya, to komai ballagazancinta ba za ta ce, alhakin tsare rayuka ya fadi daga kanta, kowa ya je ya kashe wanda yake so ba. Duk duniya babu inda aka taba samun haka. Don haka muna nasiha ga Musulmin da ke cikin wannan gwamnati, ya alla a bangaren mulki ne ko tsaro, su sani zubar da jinin jama'a da ake yi a kasar nan alhakin yana wuyansu ne su da sauran shugabannin gwamnatin da ba Musulmi ba. Kada su dauka Shugaban kasa ne kawai alhakin ke wuyansa, su ma suna da kaso, abin da zai hana su samun zunubi shi ne idan suka bayar da shawarar yadda za a magance wannan zubar da jini, amma suka lura an ki daukar shawarar saboda dalili na siyasa ko wata manufa, sai su yi murabus daga gwamnatin. Wallahi, ba uzuri ba ne da za su tunkari Allah da shi gobe kiyama cewa ba su ne shugabanni na kololuwa ba, shi ya sa suka kasa yin komai. 

Alkur'ani ya nuna mana cewa ko da muguwar magana ko ta banza ko wadda za ta cutar ake yi, idan mutum bai iya hanawa, ya tashi daga wurin. To ina ga zubar da jinin bayin Allah da ake yi, amma hukuma tana rikon sakainar kashi da lamarin? Idan sojojinmu za su ja kasashen waje kwantar da yaki su samu nasara, me zai hana su iya kwantar da yakin da ke gudana a jihohi biyu na kasar nan?

Kwanaki wani soja ya fito a gidan rediyon Muryar Amurka yana kukan cewa akwai lauje cikin nadi dangane da yaki da masu daukar makami a yankin Arewa maso Gabas, amma maimakon mu ji hukumomin tsaro sun dauki matakin bincikar zargin, sai suka ce, wai soja mai da'a ba zai yi haka ba. Sojan nan ya jero zarge-zarge kan kwamandan sojojin Bama, amma ba wani abu daga bangaren gwamnati na a binciki zargin nan. Kuma ga shi kullum kashe mutane ake yi a yankin fiye da kowane yanki. 

Ran mumini daya yana da tsada a wurin Ubangiji, shi ya sa a wasu Hadisai Manzon Allah (SAW) yake cewa: ''Wallahi, gushewar duniya ya fi sauki a wurin Allah da kashe mumini ba tare da hakki ba.'' A wani Hadisin kuma ya ce: ''Rusa dakin Ka'aba ya fi sauki a wurin Allah da kashe mumini ba tare da hakki ba.'' 

Na uku: Kyautata tsare hankali:

1. An sanya hankali sharadi na takalifanci:

Al-Amadiy ya ce: ''Ma'abuta hankali sun hadu kan cewa daga cikin sharadin takalifanci (dora wa mutum hukunci) ya kasance mai hankali. Kuma shi ne mafi muhimmanci ga takalifanci, domin takalifi magana ce, kuma magana da wanda ba ya da hankali kuma ba ya fahimta abu ne korarre, kamar yin magana da dutse ko dabbobi, domin asalin maganar da ake nufi shi ne umarni da hani da suke iya jawo samun lada ko ukuba. Wanda yake umarnin shi ne Allah Madaukaki kuma shi ne ya wajabta da'a, kuma kasancewar wanda ake umarni da yin kaza da kaza kamar mahaukaci da yaron da bai mallaki hankali ba, ana kallonsa kamar dutse ne ko itace da dabba… don haka ake yi masa uzuri kan takalifanci.'' (Al-Ihkamul fi Usulil Ahkam, mujalladi na 1 shafi na 138-139).

Saboda haka idan hankali sharadi ne na yin takalifanci a shari'ar Musulunci, to kiyaye shi lalura ne da ba makawa, kuma rayuwar mutane ba za ta daidaitu ba ba tare da shi ba.'' (Makasidus Shari'a wa Alakatiha bi Adillatis Shari'a, shafi na 112).

2. Haramta abin da zai bata hankali:

Daga cikin abin da yake nuna kular shari'ar Musulunci wajen tsare hankali akwai cewa ta haramta duk wani abin da zai iya batawa ko gusar da hankali da jawo masa matsala. Kuma wadannan abubuwa masu bata hankali sun kashi gida biyu:

a. Masu bata hankali na zahiri:

Su ne wadanda suke jawo matsala ga hankali ta yadda mutum zai wayi gari kamar mahakuaci, wanda ba zai iya gane masoyi daga makiyi ba, ba zai iya bambance alheri da sharri ba, ya zamo maganganunsa ba su da kan gado, yana mai watsa sirrinsa da ya kamata ya boye. Wadannan masu bata hankali sun hada da giya da kwaya da hodar Iblis da sauran kayayyakin gusar da hankali:

''Ya ku wadanda suka yi imani! Abin sani kawai, giya da caca da refu da kiban kuri'a, kazanta ne daga cikin aikin Shaidan, sai ku nisance shi, wa la'alla ku ci nasara. Abin sani kawai, Shaidan yana nufin aukar da adawa da keta a tsakaninku a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga Sallah. To shin ku masu hanuwa ne?'' (k:5:90-91).

Sayyid kutub ya ce: ''Lallai maye da kowane irin abin maye yana kore fadaka a da'iman da Musulunci ya farlanta a kan zuciyar Musulmi domin ya kasance sadarwa a tsakaninsa da Allah ba ta yankewa a kowace lahaza tana mai kiyaye dokokin Allah a kowane motsi. Kuma sa'annan ya kasance da wannan fadaka yana mai aiki na wajibci domin inganta rayuwa da kyautata tad a kare ta daga yin rauni ko fasadi, ya yi amfani da aiki da ita wajen kare ransa da dukiyarsa da mutuncinsa da tsare zaman lafiyar jama'ar Musulmi da shari'arta da dokokin zamantakewarta daga dukkan wata ta'adda. Musulmi a tilonsa ba a bar shi ga dabarar kansa ko jin dadin kansa ba, a kansa akwai takalifofi da suke wajabta masa kasancewa a fadake, akwai takalifofi na Ubangijinsa akwai takalifofi na kashin kansa, akwai takalifofi na iyalansa, akwai takalifofi na jama'ar Musulmin da yake raye a cikinta da kuma takalifofi na Musulunci dukkansu na yin kira zuwa gare su da bayar da su. Ana bukatar ya kasance a fadake koyaushe domin ya sauke wadannan takalifofi. Kai hatta a lokacin da yake jin dadi da abubuwa tsarkaka, Musulunci ya bukaci ya kasance a fadake a cikin wannan jin dadi, domin kada ya zamo bawa ga sha'awoyinsa ko wannan dadi. Ya zamo da'iman ya fi karfin kwadayinsa ya tankwara shi ya zamo mai bin umarninsa ba shi ya zamo mai bi ga kwadayinsa ba. To idan maye ya kama mutum ba zai iya kiyaye komai daga cikin wadannan abubuwa ba.'' (Fi Zilalil kur'an, mujalladi na 2, shafi na 977). 

Ya ci gaba da cewa: ''Sa'annan wannan bacewar hankali a hakikaninta ba komai ba ce face guduwa daga hakikanin rayuwa a wani lokaci daga cikin lokuta da rusuna ga wasu surori da suke mamaye tunanin mutum. Kuma Musulunci yana kin wannan hanya ga Musulmi. Yana nufin mutane su rika ganin hakikanin al'amura su fuskance su yadda ya kamata, su rayu a cikin duniya suna masu gudanar da rayuwarsu gwargwadon yadda ya kamata, kuma irin wannan rayuwa ba za ta samu a bisa wahami da rudu ba… Kuma fuskantar hakikanin al'amura ita ce ginshiki mai girma da karfin ikon gudanar da rayuwa. Amma guje mata zuwa ga wahamomi wata hanya ce ta aukawa ga rudu da rauni da ruguzawa. A cikin kyawun Musulunci da'iman yana sanya tarbiyyar manufa a gaba da kubutar da ita daga daurin al'adu masu tilasta karkacewa da gushewar hankali, wannan buguwa da gushewar hankali ana daukarsa shi kadai a matsayin wani aikin Shaidan da ke iya lalata rayuwar mutum.'' (Fi Zilalil kur'an, mujalladi na 2, shafi na 977).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Thursday, June 18 @ 05:30:42 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al'umma 07" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: