Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 08
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Daga Sheikh Faisal Bn Ali Al- Ba'adani Fassarar:

RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 08

Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da Mal. Aliyu Rufa'i Gusau.

Har yanzu dai muna cikin darasin RAYUWAR ANANBI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA TSAKANINSA DA UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN RAMALANA (4)

Ya tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi saje/doren Azumi, wato doreri a lokacin watan Ramalana, don ya sada dare da rana a cikin halin ibada.

Anas Raliyallahu Anhu ya ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma su wata rana: ''Kada ku yi saje/dore.''

Sai wasu daga cikin Sahabbai suka ce ma sa: ''To, ba kai kakan yi ba?'' Sai ya karba mansu da cewa: ''To, ai ba daya nake da ku ba, don ni ana ciyar da ni ana shayar da ni, a lokacin da nake bacci.'' Haka kuma Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya ce: ''Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana yin saje/dore a Azumi. Sai wani mutum daga cikin musulmi ya ce ma sa; ''Ya Manzon Allah, to ai kai kana yi.'' Sai ya karba ma sa da cewa: ''Ai ba wanda kafadarsa take daidai da ta wa a cikin ku. Domin ni Ubangijina kan ciyar da ni, ya kuma shayar da ni a lokacin da nake bacci.'' Amma duk da haka ba su daina ba. Ganin haka sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwarara da su suna bin sa har tsawon kwana biyu suna saje/dore, sai wata ya tsaya. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, ya ce masu: ''Kun kuru, da wata bai tsaya ba, da sai na shaqe ku a sajen/ doren.'' Mai riwaya ya ce, ya yi masu haka ne Sallallahu Alaihi Wasallama don ya tarbiyantar da su.''

Wadannan nassosa da suka gabata na nuna cewa Shari'a ba ta yarda da saje/dore ga wanda ba Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Amma mutum ya samu ya qi buda baki har sai dare ya tsala. Saboda an riwaito Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: ''Kada ku yi saje/dore. Amma ba laifi ga wanda ke so daga cikinku, ya jinkirta budin baki, har sai dare ya tsala.'' To, amma ya kamata mu fahimci cewa, wannan dama da Manzon Allah ya bayar, ta halacci ce kawai ba mustahabbanci ba. Domin kuwa ya tabbata cewa ya yi matuqar kwadaitar da musulmi a kan gaggauta budin baki, kamar yadda Hadisin Sahalu dan Sa'adu yake nunawa, inda ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ''Mutane ba za su gushe cikin alheri ba, matuqar suna gaggauta budin baki.''

Cewar kuma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: ''Haqiqa Ubangijina na ciyar da ni ya kuma shayar da ni a lokacin da nake barci,''

Malamai sun qara wa junansu sani a kan wannan magana. Sashensu suka ce, lafuzzan da zancen na Ma'aiki ya qunsa na tabbatar da cewa tantagaryar abinci ne da sha, ake ciyarwa da shayar da shi. Babu kuma wani dalili da zai bayar da damar yin ta'awili wa maganar. Wasu kuma suka ce, a'a Allah Subhanahu Wa Ta'ala na tsatstsage Manzon Allah ne Sallallahu Alaihi Wasallama da sannai, ya kuma cika ruhinsa da mamakon dadin ganawa da yake yi da shi. Suka qara da cewa, da tantagaryar abinci da sha ne Allah ke cika Manzon nasa da su, hakan ba za ta zama mu'ujiza ba, kuma ba zai kasance mai Azumi ba, balle har ya yi saje. Maganar nan ta biyu ita ce mafi armashi. Ga Allah muke godiya.

Wata fa'ida kuma da musulmi ke iya qaruwa da ita a cikin wannan magana ita ce, a duk lokacin da mutum ya shagalta da yawan bauta da kusantar Ubangijinsa, to, hakan za ta kakkabe sha'awowin duniya, da suka shafi buqatun jiki da ruhi daga zuciyarsa.

Domin kuwa yawan ibada na qara wa mutum qarfin niyya da himma da azama ne, ta yadda ba yadda rundunar shedan za ta iya galaba a kansa.

Saboda haka ne sha'ria ta nada wa Azumi rawanin zama sarkin yaqi tsakanin mai yin sa da rundunar shaidan. Idan kuma muka koma ga saje da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi, a matsayinsa na wani abu da Shari'a ta halasta masa, sai mu ga cewa hakan na dada fitowa fili da irin sha'awar da yake da ita a kan ayyukan alheri, da irin kulawar da yake da ita ta ganin ya yaye zuciyarsa daga kwadayin shan nonon duniya, da koya mata wadatuwa da abu dan kadan, don kada nauyi ya niqe ta, har ta kasa samun isasshiyar dama ta yin bauta ga Ubangijinta. Musamman a cikin wannan wata na Azumi mai albarka da matsananciyar tsada.

Bayan wannan kuma, al'amarin na nuna mana girman Allah Subhanahu Wa Ta'ala da daukakar ikonsa, ta yadda yake iya tabbatar da wani abu da ya saba wa al'ada, ba tare da wani dalili na zahiri ba. A yayin da shi kuwa hana sahabbai yin saje/dore da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, alhali shi yana yi, ke nuna irin yadda yake qauna da tausaya wa al'ummarsa. Haka kuma su Sahabban a shirye suke su yi koyi da shi Sallallahu Alaihi Wasallama ta kowane hali, matuqar bai ce masu kul ba.

Allah shi ne mafi sani.

Azumi A Lokacin Tafiya:

Azumin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama lokacin da yake cikin halin tafiya ya dauki wani salo. Malam Dawusu ya riwaito daga Ibnu Abbas Raliyallahu Anhuma wanda ya ce:

''Wata rana a cikin Watan Azumi, tafiya ta kama Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kuma tafi da Azuminsa a baki, har sai da ya kai wani wuri da ake ce wa Usfan, inda ya nemi a kawo masa qwaryar ruwa, ya sha, rana da sauran mutane na kallonsa. Ya kuma ci gaba da cin abincinsa har ya isa Makka. Saboda haka ne ma Ibnu Abbas ke cewa: ''Manzon Allah ya yi Azumi ya kuma sha, a lokacin tafiya.

Saboda haka wanda ya ga dama ya sha, wanda kuma ya ga dama ya yi Azumi.''

Amma kuma idan muka bi diddigin tarihin tafiye-tafiyen Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Azumi, sai mu fahimci cewa, yin Azumi ga matafiyi shi ya fi, matuqar babu wata wahala da za ta afka ma sa. Saboda shi ma Annabi Sallallahu Alaihi WaSallama ya yi haka. Kamar yadda Hadisin Abuddarda'i Raliyallahu Anhu ke cewa: ''Mun fita wata rana saboda wata tafiya, tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin watan Azumi, ana kuma matsananciyar rana, da har wasu daga cikinmu ke dora hannu a ka saboda ita. Amma duk da haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne kawai da Abdullahi dan Rawahata ba su aje Azumi ba.'' Yin haka kuwa ko shakka babu, matuqar akwai dama shi ya fi, bisa ga a koma ranko.

Amma idan mai Azumi ya hangi wata matsala 'yar qanqanuwa da ba za ta cutar da shi ba, ko buqatar lalle sai ya aje Azumin ta kama, to abin da ya fi shi ne ya ajiye, saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:

''Haqiqa Allah na son a karbi rangwamensa kamar yadda yake qin a saba masa.'' Kai! ana ma iya cewa yin Azumi a cikin irin wannan hali makaruhi ne, saboda aje shi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a lokacin yaqe-yaqen da ya yi a cikin Ramalana, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Ibnu Abbas Raliyallahu Anhuma cewa:

''Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya dauki Azumi, har sai da aka kai wani wuri da ake ce wa Qudaid, sannan ya ci abinci. Kuma daga nan bai sake Azumi ba har watan ya qare.''

Haka kuma Anas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa: ''Mun Kasance tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wata rana a cikin watan Azumi, wanda ya fi mu samun inuwa shi ne wanda ya yi rumfa da bargonsa. Wadanda suka ci gaba da Azumi a cikin wannan hali, ba su sami tabuka komai ba. Su kuwa wadanda suka aje shi, sai suka ci gaba da ayyukan shirin yaqi. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ''Yau kam wadanda suka ajiye Azumi sun kwashe lada.'' Kaga da wannan ya gama tabbata cewa, matuqar al'amari ya tsananta ga mai Azumi, ko wata lalura ta faru, to aje Azumi ya wajaba a kansa. Dalili kuwa shi ne cewar da Manzon Allah ya yi a kan wadanda suka qi aje Azumi a irin wannan hali: ''Lalle sun saba! Lalle sun saba!!'' Haka kuma a lokacin da wasu mutane suka taru a kan wani mutum suna yi masa inuwa daga zafin rana, an riwaito cewa Ma'aiki ya ce masa: ''Ba nagarta ba ce yin Azumi a cikin halin tafiya; Allah ba ya son haka.''

Bayan wannan kuma an riwaito Abu Sa'idil-Khudri Raliyallahu Anhu na cewa: ''Wata rana tafiya ta kama mu tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa Makka, duk kuma muna dauke da Azumi. Muna ya da zango wani wuri, sai ya ce: ''To, haqiqa fa, kun kusa haduwa da abokan gaba, saboda haka ku aje Azumi shi ya fi. Allah ya yarde maku''.

Sai kuwa wasu suka aje, wasu kuma suka daure. Da kuma muka sake ya da zango a wani wurin, sai ya sake ce mana: ''To, gari na wayewa fa za ku gamu da abokan gaba. Saboda haka kada wanda ya dauki Azumi, haka shi ya fi gare ku. Sai kuwa muka aje Azumi gaba daya.'' Mai riwayar ya ce:

''Bayan haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai qara hana mu Azumi a lokacin tafiya ba, ko muna tare da shi.'' Allah shi ne mafi sani.

Malam Ibnul Qayyim ya qara da cewa:

''Ba Sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ce ba, kula da tsawon tafiya kafin a aje Azumi. Duk zantukan da ke cewa haka, ba su inganta cewa daga gare shi suke ba Sallalhu Alaihi Wasallam. Ya ma tabbata cewa Sahabbai ko Azumin ba su dauka da zarar sun qulla niyyar tafiya. Ba wai sai sun ba gidajensu baya ba. Sun kuma tabbatar wa duniya cewa haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi.

Idan muka koma ga abin da Malaman Fiqihu suka cirato daga bakunan ma'abuta ilmi, na qoqarin gane abin da ya fi tsakanin yin Azumi ko aje shi a lokacin tafiya. Sai a taras kawai suna tabbatar da cewa, yin Azumi ko aje shi duk halas ne, kuma Sunnah ce ta Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan kuma shi ne abin da ya kamata masu gaggawar suka ga masu aje Azumin ko daukar sa su lura. Domin kowannensu yana da hujja, tattare kuwa da cewa aje Azumin shi ya fi, ko a kame baki.

Allah shi ne mafi sani.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Thursday, June 18 @ 05:34:35 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI 08" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: