Muhawara Hausa
 



KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) 35
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa
 
 KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) 35
 
 KARANTARWAR SHEHU USMAN DAN FODIYO A KAN BIN SUNNAH (2)
 
 Ci gaba ...
 
 4. An yi tambaya, shin ko ya halatta ga wanda ya riga ya kama wata mazhaba ayyananniya ya fita daga gare ta? A wajen jawabi an ce, ''Na'am,'' zai iya fita yanke.
 
 Rafi'i shi ne ya inganta wannan ra'ayi. Ko da yake wani qaulin an ce ba zai iya fita yanke ba, domin ya riga ya daure kansa. A qauli na uku kuwa aka ce bai halatta ya fita da wadansu mas'alolin mazhaba ba, sannan ya ci gaba da riqo da wasu mas'alolin.
 
 5. Duk Mujtahidi da ya sava wa nassin Alqur'ani da Hadisi ko Ijma'i, ba za a bi shi ga wannan magana ba.
 
 6. Duk abin da almajiran mujtahidi suka fahimta daga maganar mujtahidin nan ba za a lissafa da shi ba a cikin mazhabarsa. Amma daga baya, sakacin mutane ya yi yawa har suka riqa jingina ra'ayoyin masu wallafar littafi da masu yi wa littafi sharhi ga mazhabar wadanda suke koyi da shi, suka mai da su kamar ra'ayoyin mujtahidin nan na asali.
 
 Sai daga qarshe al'amari ya koma ga su almajiran suna koyi da ratayawa da junansu. Ta haka har ya zama kowane littafi ya kai Juz'i ashirin, alhali kuwa ainihin maganar mujtahidin a cikinsa idan an tara ba za ta kai Juz'i daya ba.

Wajibi ne a kan kowane Musulmi mukallafi ya qudurta cewa dukkan Imaman Musulmi a kan shiriya ta Ubangijinsu su ke. (Wato ba sa cikin bata). Wato su Imamu Abu Hanifa, Maliki, Shafi'i da Imamu Ahmad bin Hambal.
 
 8. Wajibi ne a kan kowane Musulmi Mukallafi kada ya yi qyamar aiki da maganganunsu (Mujtahidan). Wadansu mutane a yau sun kasance idan waninsu ya yi amfani da maganar da ba ta Imaminsa ba, sai ya ce, ''Bari in yi koyi da shi don larura.'' Watau ya yi aiki da hukuncin a kan hukuncin larura wadda take halartar da abin da aka hana. Sai ya ga kamar dai ya afka ne a cikin zunubi. To ya sani cewa wannan aiki nasa da ya yi na qyamar hukuncin Mujtahidin nan, shi ne babban zunubi wanda ya wajaba ya tuba saboda aikata shi, kuma ya nemi gafara a wurin Allah. Domin da su irin wadannan mutane sun yar da cewa dukkan Imaman Musuluunci a kan shiriya su ke, da ba su yi qyamar aiki da magabatansu ba, domin shiriya ba a qyamar ta matuqar dai an tabbata ita ce.
 
 9. Duk wanda ya bar aikin da aka yi sabani a kan zamowarsa wajibi, ko kuwa ya aikata abin da aka yi sabani a kan zamowarsa haram, to ba za a yi masa inkari ba, idan har ya dogara da qaulin malami. Sai fa idan ya dogara ga maganganunsa wadanda suka saba wa nassin Alqur'ani da Sunnah ko Ijma'i.
 
 Amma matuqar aikinsa ya yi daidai da wata maganar Mujtahidi na Alhalus-Sunnah, to ba za a yi masa musu ba. Amma da a ce an yi musu shi ne a ce abin da wannan mutum ya yi haram ne.
 
 Amma da a ce an yi musu ne da nufin shiryarwa ko don yi masa nasiha, to shi wannan ba za a kira shi inkari ba. Amma a wajen babin fatawa, malamin da ke yi wa mutane fatawa da wani qauli manisanci ga hankali, ko kuma mai raunin hujja, ya bar mashahuriyar magana mai qarfin hujja, to za a iya yi masa inkari domin bai halatta a yi fatawa ba sai da mashahuriyar magana mai qarfi.
 
 10. Mutum wanda za a yi wa inkari na hukunci, shi ne wanda ya sava wa nassin Alqur'ani da Sunnah ko na Ijma'i.
 
 Wannan bayani na Shehu Usmanu dan Fodiyo ya nuna mana irin tsarin karantarwar Shehun Malamin. Sannan za mu fahimci cewa riqo da mazhaba guda daya ba tilas ba ne cikin addinin Islama.
 
 Haka kuma riqo da mazhabar ba laifi ba ne, sai dai in ka yi watsi da maganar Manzon Allah (S.A.W.)
 
 ingantacciya don riqo ko bin jagoran mazhabar, to a nan kam an kauce wa karantarwar Annabi (S.A.W.) da Sahabbai da sauran magabata na qwarai har da shi jagoran Mazhabar da kake bi din.
 
 Domin dukkansu sun ce in an ga Hadisi ingantacce ya sana da fatawa ko karantarwarsu to a ajiye maganarsu a dauki ta Manzon Allah (S.A.W.) ita ta fi daidai (Wallahu A'alamu).

 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 20 @ 18:40:57 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi



"KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA KWARAI (Manhajus Salafis Salih) 35" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com