Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 02
 
 
Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
Daga Dr. Mansur

NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 02

Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad Al-Kadhibi –

Wani malami dan kasar Bahrain da Allah ya ganar da shi gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi'a.

KARAMOMIN SHI'A

Bayan cikawar babban marji'inmu kuma shugaban Hauza ta Najaf Ayatullahi Al-Khu'i, an yi wani jerin gwano a garinmu dauke da makara don suranta jana'izarsa.

Ba mu watse daga wannan jerin gwano ba sai ga labari ya yadu cewa, a unguwar Al- Makhariqa an ga hotonsa a cikin wata. Kuma duk da yake a cikinmu babu wanda ya ga haka da idonsa amma kusan kowa ya gaskata kuma mutanen garin Manama duk sun ba da gaskiya ga wannan karama musamman dai mata.

Wani abokina da nake kusa da shi a taron ya ce min, wai kuwa kai ka ga wani abu? Na daga kai na kalli sama na ce ma sa ni kam ban ga kome ba. Sai ya ce ko ni ma haka. Sai na ce to, me ya sa kake ba da himma wajen yada wannan labari kamar ka gani da idonka? Sai ya ce, ba ka ganin yadda kowa ya raja'a ga wannan batu? Ko dukan ka za su iya yi fa idan ka musanta! Sai muka bushe da dariya. Ba zan manta ba wani daga cikin mazauna Manama da shi ma jita-jitar ba ta gamsar da shi ba cewa ya yi, to ai ko manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam da ya cika ba mu ji ya bayyana a cikin wata ba!
 
 ME YA RABA NI DA ADDININ SHI'A?


Ba zai yiwu in yi ma kaina shedar zama na kirki ba. Amma kuma akwai wasu ababen da rayuwata ba ta iya natsuwa da su ba ko dadai.

Abubuwa guda uku ne na dade ina samun qaiqayi a cikin zuciyata game da su a addinin Shi'a.

Wadannan abubuwa sun haxa da: zagin sahabbai da cin mutuncinsu da auren wucin gadi sannan da kiran wanin Allah don neman kusanci ko neman agaji da biyan buqata.

Wadannan abubuwa sun dade suna damu na a cikin rayuwata har kafin Allah ya yi min gamon katar da gane gaskiya in koma ma aqidar Ahlussunna wadanda aka tashe mu a kan tsananin adawa da gaba da su.

1. Zagin Sahabbai da Cin Zarafin su; Kamar ko wane dan Shi'a na tashi ina qyamar su da ganin laifin su bisa irin tatsuniyoyin da malamanmu suke shara mana a kan su.

Amma fa ban taba zagin su irin yadda na ji mutane suna yi ba. Wannan tun da farko na tsane shi domin a gani na zagi ba ya cikin ayyukan alheri. Hankalina ya kasa yarda cewa, a cikin addini da kuma ayyukan lada akwai zagi da dibar albarka ko da kuwa a wurin najasa kamar yadda fitaccen malamin nan Muhammad At-Tusirkani yake cewa a cikin littafinsa La'alil Akhbar:

Ka sani mafi dacewar lokaci da wuri da yanayin da za a la'ance su shi ne lokacin kama ruwa.

Idan ka zo fitsari ko bahaya da kuma wurin kawar da najasa ka yi ta fadi kana maimaitawa ba tare da qyaqqyaftawa ba, kana cewa:

''Ya Allah ka la'anci Umar sannan Abubakar da Umar, sannan Umar da Usman sannan Umar da Mu'awiyah. Ya Allah! Ka la'anci A'isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam da duk wanda ya yarda da aikinsu har ranar tashin qiyama.''

Daga nan ne na fara samun damuwa a cikin wannan addini. Littattafanmu na da da na yanzu a maqare suke da zancen kafircin sahabbai da cewa sun yi ridda bayan cikawar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam.

Daga nan kuma sai aka gina la'antar su da barranta daga gare su. Dubi abin da ya zo a cikin Rijal As-Kasshi daga Hanan dan Sudair daga babansa daga Abu Ja'afar Alaihis Salam cewa: ''Mutane duk sun yi ridda bayan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam in ban da mutane uku. Sai na ce ma sa su wane ne ukun? Ya ce, Miqdad dan Aswad da Abu Dhar Al-Ghifari da Salman Al- Farisi.''

Waxannan su ne wadanda suka ki yarda su yi ma Abubakar mubaya'a har sai da aka zo da Imam Ali aka tilasta shi yin mubaya'ar. Wasu ruwayoyi sun qara mutane hudu a cikin wadanda suka tsayu a kan musulunci ba su yi ridda ba, sai adadin ya kai bakwai, amma bai wuce hakan ba. Wannan shi ne abin da ruwayoyin suke kawowa.

An karbo daga Al-Haris dan Mughira An-Nasri ya ce, na ji Abdulmalik dan A'ayan yana tambayar baban Abdullahi Alaihis Salam, yana ta tambayar sa a kan wannan har sai da ya ce, kenan dai mutane duk sun halaka gaba daya?

Ya ce, eh wallahi dan A'yan. Mutane sun halaka ga baki daya. Ya ce ma sa na gabas da na yamma? Ya ce, ai duk sun afka cikin bata, sun halaka sai mutane uku kawai. Sa'ann nan daga baya Abu Sasana ya riske su. Addu'ar da ake kira

''Du'a'u Sanamai Quraish''; Addu'ar gumakan Quraishawa biyu da ire-irenta wadanda suke cike da la'antar muqarraban manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam Abubakar da Umar duk sakamakon wancan tunanin ne da aka gina shi a kan wadancan rubabbun ruwayoyi da suka ci karo da Alqur'ani. Akwai wani lokaci da na tsaya kurum na nazarci ayar Alqur'ani in da Allah Tabaraka Wa Ta'ala yake cewa:

''Kuma da wadanda suka yi gabaci na farko daga muhajirai da ansarai da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi, kuma ya yi ma su tanadin gidajen aljanna wadanda qoramu ke gudana a qarqashin su, suna madawwama a cikin su har abada, wannan shi ne rabo babba''. Suratut Taubah:100

Sai na ga cewa fa wannan aya ta bayyana qarara yadda Allah Tabaraka Wa Ta'ala ya nuna amincewarsa ga magabatan musulmi da suka hada da muhajirai da ansarai, cikin su kuwa har da irin su Abubakar da Umar da Usman da Dalhatu da Zubairu da Sa'adu dan Abu Waqqas da Abdullahi dan Mas'ud da Sa'adu dan Mu'azu da duk wanda ka ga damar ka qirga a cikin su wadanda a yanzu haka 'yan Shi'a suke debe ma albarka.

A nan ne na tambayi kaina cewa, ya za ayi sahabban annabi su zalunci Ali Radhiyallahu Anhu su qwace ma sa haqqen shugabanci ga su kuwa su ne Allah ya shelanta ya yarda da su har ya yi ma su tanadin gidajen aljanna?!

Idan dai har manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wasallam ya cika yana mai amince mu su, kuma Alqur'ani ya sanar da yardar Allah madaukakin sarki a gare su, to, ta ya ya za su ja da baya su lalace; su fada cikin fitina kai tsaye bayan cikawar maigidansu?!

Ya kuma za ayi wadannan su canja littafin Allah, su yi ma hukunce- hukuncen addini gyaran fuska?!

To, wai kam tun farko Allah ya san za su canja ne su ja da baya ko kuwa ya ya?

Domin kuwa duk musulmi ya yarda cewa, Allah ya san jiya da yau da gobe, ba abin da yake boyuwa a gare shi. To, idan kuwa Allah ya sani mene ne matsayin ayoyin yabo da ya saukar a kan su?

Idan har malaman Shi'a ba suna son su ce madaukakin sarki ya cuci musulmi ba ne da ya saukar da ayoyin yarda a gare su kuma ya sanya surukuta a tsakanin su da manzonsa suka aurar da 'ya'yansu gare shi suka kuma auri nasa 'ya'yan alhalin ya san cewa munafukai ne, da zasu yi ridda. Idan ba haka malamn Shi'a nufi ba to, mene ne manufarsu?

Me ya sa Allah mafaukakin sarki bai fadi gaskiyar lamarinsu ba in haka ne don a sani?

Rashin samun gamsasshiyar amsa ga wadannan tambayoyi ya ja ni zuwa fahimtar cewa, Allah ya amince ma su amincewa ta har abada kuma ba zai bari su ja da baya ba tun da ya furta kalmar amincewa a gare su. Kuma ya sani – a cikin iliminsa na azaliyya – cewa, za su ci gaba da bin tafarkin da fiyayyen halitta ya dora su a kan sa ila yaumil qiyamati.

In ba haka ba da babu yadda za ayi ya rubuta a mafi tsarkin littafinsa cewa ya yarda da su.

Kamar yadda ya fada a wata ayar:

''Haqiqa, Allah ya yarda da mummunai a lokacin da suke yi ma ka caffa a qarqashin bishiyar nan, sai Allah ya kalli abin da ke cikin zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a gare su, ya saka ma su da budi na kurkusa. Suratul Fathi:18

''Wadanda kuwa Allah ya ba mu labarin ya kalli abin da ke cikin zukatansu, a sakamakon haka har ya saukar da natsuwa akan su, ba ya halalta wani ya sa shakku cikin lamarinsu.'' Cigaba a darasi na uku
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, September 20 @ 19:32:13 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin:
Wace Irin Mace Shari`a Ta Kwadaitar Da Namiji Ya Aura; Kuma Wane Irin Namiji Sha


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin

"NURUN ALA NUR ''BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMA SAHABBAI'' 02" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: