Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 01
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Yaseen Bi-Asbi'i

Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 01

Masallaci: Ba a fada ba

Huduba ta farko

Godiya da taslimi:

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa. A kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita. Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.'' (k: 25:62).

Ya ku muminai! Mun shigo watan Sha'aban, mai rabo ya samu rabo a watan Rajab, ta wajen ayyukan da'a da kusanci ga Allah. To ga shi mun shigo watan Sha'aban me muka shirya aikatawa a cikinsa? Wannan huduba kan wannan wata za ta nazarci darussa da wasu abubuwa da suka shafi falala da hukunce-hukuncensa. Za mu nazarci rayuwar Manzonmu (SAW) a cikinsa domin yin koyi da shi. Me ya zo mana dangane da falalarsa? Me ya zo a cikinsa na hukunce-hukuncensa? Me Annabi (SAW) yake yi idan watan Sha'aban ya shigo?

An kira shi da watan Sha'aban ne saboda Larabawa suna watsuwa a cikinsa domin neman ruwa. Wasu sun ce, ana kiransa haka ne saboda watsuwarsu wajen kai hare-haren yaki bayan fita daga watan Rajab Mai alfarma. Wasu kuma suka ce an kira shi da haka ne saboda wata ne da ke bayyana a tsakanin Rajab da Ramadan.

Amma falalarsa da abin da ake so a rika yi a cikinsa, hakika ya zo daga Ahmad da wasu, kuma Ibnu Khuzaima ya inganta shi, sannan Albani ya kyautata shi daga Usama bin Zaid, ya ce: ''Na ce: ''Ya Manzon Allah! Ban gan ka kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha'aban ba! Sai ya ce: ''Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan. Shi ne watan da ake daukaka ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai. Don haka nake son a daukaka aikina ina cikin azumi.''

Ya ku Musulmi! Ba ku ganin yadda mutane suke gafala a yau daga watan Sha'aban? Suna gafala daga ayyukan da'a da neman kusanci ga Allah. Suna nutso a cikin sha'awoyi da ayyukan jin dadi. Suna gafala daga Sha'aban alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance yana raya shi da ayyukan da'a da azumi, ya ce da Usama: ''Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan.''

Mutane suna gafala ne daga Sha'aban saboda yana tsakanin watanni biyu masu girma wato Rajab Mai alfarma da Ramadan Mai albarka. Mutane sun fi shagala da su biyun don haka sai aka shagaltar da su daga Sha'aban. Ta kai wasu mutane suna ganin azumin watan Rajab (azumin tsofi inji Hausawa), ya fi azumin Sha'aban, saboda shi Rajab wata ne Mai alfarma. Wannan ba daidai ba ne, azumin Sha'aban ya fi na Rajab falala saboda fadin Annabi (SAW): ''Ana daukaka ayyuka a cikinsa, kuma ina son a daukaka aikina ina azumi.''

Hakika malamai (Rahimahumullahu) sun ce: ''A cikin wannan Hadisi akwai dalili cewa mustahabbi ne a raya lokutan da mutane suka gafala daga ayyukan da'a, kuma hakan abin so ne a wurin Allah Mabuwayi.''

Don haka ku koma ga Allah ya ku bayin Allah! Ku sallama ga abin da Yake yarda da shi, domin lada da ijara suna kara martaba idan aka yi su a lokacin da mutane suka gafala, fa'idojin raya shi da da'a ita ce mafi girma. Kuma wadannan fa'idoji za a same su ne idan aka yi ayyukan da'ar a asirce. Sirrantan aikin da'a daya ne daga cikin manya sabubban karbar aiki. Akwai bukatar aiki ya kasance don Allah, a nesanta shi daga jiyarwa da riya.

Ku sani aikin da'a a lokacin gafalar mutane yana da wahala a tsakanin mutane. Kuma mafiya falalan ayyuka, su ne wadanda suka fi wahala ga mutane matukar sun dace da Sunnar Annabi (SAW). Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''Ladar aiki ya dogara ne da irin wahalar da aka sha.''

Ya bayin Allah! Lallai ana daukaka ayyukan shekara zuwa ga Allah Madaukaki a watan Sha'aban. Ayyukan bayi suna bijirowa ga Allah bijirowa a kowane yini da dare, sannan ayyukan mako su bijiro gare shi a kowace Litinin da Alhamis, sannan a bijiro da ayyukan shekara a Sha'aban. Ga kowace bijirowa akwai hikima, Allah Yana bayyana su ga wanda Ya so daga cikin halittunsa, ko Ya asirta shi a wurinSa, tare da cewa babu abin da Yake boyuwa ga Allah Madaukaki daga ayyukan bayinSa.

Ya ku muminai, a yayin da Sha'aban ya zama kamar zagi ga watan Ramadan-kuma ba makawa ga tattalin bakon da ke zuwa- sai aka shari'anta yin azumi da sauran ayyukan da'a a cikinsa domin kusantar Allah ta yadda za a yi tattalin zuwan Ramadan, a tare shi cikin annashuwa da shauki da sabo wajen da'a ga Mai rahama. Don haka ne Annabi (SAW) yake yawaita azumi a cikinsa, yake cin ganimar lokacin gafalar mutane duk da matsayinsa, shi ne Manzon Allah (SAW), shi ne wanda aka gafarta masa abin da ya gabatar da wanda ya jinkintar na zunubinsa. Don haka magabatan kwarai suke kara kokari a Sha'aban suke tattalin zuwan Ramadan.

Ya kai bawan Allah! Me ka kintsa a cikin wannan wata na Sha'aban don tarbar Ramadan? Wane tattali ka yi masa? Saurara Allah Ya tsare ka; na farko ka yi tattalin ranka cikin abin da Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar maka, wato yawaita azumi a wannan wata. Hakika (SAW) ya kasance yana yawaita azumi a cikinsa. An karbo daga A'isha (RA) ta ce: ''Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har sai mun ce ba ya shan ruwa, kuma yana shan ruwa har sai mun ce ba ya azumi. Amma ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata guda ba, sai Ramadan. Kuma ban taba ganinsa ya yawaita azumi a wani wata fiye da Sha'aban ba.'' Buhari da Muslim suka ruwaito.

A wata ruwaya ta Buhari ya ce, ''Ya kasance yana azumtar Sha'aban dukkansa.'' Muslim kuma ya ruwaito cewa: ''Yana azumtar Sha'aban sai dan kadan.'' A ruwayar Abu Dawud ta ce: ''Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha'aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.''

Dukkan wadannan Hadisai ingantattu ne, kuma wannan yana nuni ne da tsananin kiyayewarsa ga yin azumi a cikin Sha'aban. Kuma manufa ita ce ya fi yin azumi a cikinsa, ba wai yana azumtarsa gaba daya ba.

Ibnu Hajrin (RH) ya ce: ''Ya fi yin azumin tadawwa'i a cikin Sha'aban fiye da kowane wata. Ya kasance yana azumtar mafi yawan kwanakin Sha'aban.''

Ya ku Musulmi! Malamai sun ce: ''Yin azumi a Sha'aban ya fi falala daga yin azumi a sauran watanni kamar azumin Muharram, wanda shi ne mafi falalar azumi a bayan Ramadan. Domin falalar azumin tadawwa'i, shi ne ya kasance a kusa da azumin farilla na Ramadan a gabansa ko bayansa. Idan yana daf da azumin Ramadan sai ya zamo kamar an jeranta azumin sunnoni da na farilla a gabansa ko bayansa. Don haka azumin Sha'aban kamar Sunnah ce ta kabliyya ga Ramadan, yayin da azumin shida na Shawwal suke zaman ba'adiyya ga Ramadan. Don haka jerantattun sunnoni sun fi tadawwa'in da ke zaman kansa cikin abin da ya shafi Sallah. To kamar haka lamarin yake, cewa yin azumi a gabani ko bayan Ramadan ya fi falala daga yin azumin da bai saduwa da shi.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 09 @ 19:04:15 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 01" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: