Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
[ Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar ]

·Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
·Asalin Hausa (3)
·Asalin Hausa (2)
·Asalin Hausa (1)
·Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresriti
·08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????
·002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
·001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
·GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 02
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen Yaseen Bi-Asbi'i

Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 02

Ibnu Rajab (RH) ya ce: ''An ce kan azumin Sha'aban: azumtarsa kamar jarrabawar share fage ce ga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan bisa wahala. Saboda yakan sa mutum ya san wani abu kan azumin tare da sabawa da shi, ya samu dandanon Ramadan ta hanyar azumin Sha'aban, kuma ya shiga watan azumin Ramadan da karfin jiki da nishadi.''

Ya bayin Allah! Wanda azumin Sha'aban zai raunana shi daga yin azumin Ramadan, to ya dakatar da azumin idan Sha'aban ya je karshe, saboda fadinsa (SAW): ''Idan Sha'aban ya kai karshe, kada ku yi azumi har zuwa Ramadan.'' Ahmad da wasu suka ruwaito. Kuma Albani ya inganta shi, sai dai a isnadinsa akwai magana. Hanin da ke cikin wannan Hadisi domin a samu karfin yin azumin Ramadan ne. Wasu sun ce: ''Hanin a kan wanda ya sha ruwa ne bai azumci farkon watan ba, don haka idan Sha'aban ya zama saura kadan ba zai yi azumi ba.

Na biyu: Ya kai bawan Allah da me za ka kintsa kanka domin Ramadan? Ka kintsa kanka da abin da ya sauwaka na ayyukan da'a, kamar yawaita karatun Alkur'ani da sadar da zumunta da sauran ayyukan kyautatawa. Salmata bin Kuhail ya ce: ''Ya kasance ana cewa: ''Watan Sha'aban watan masu karatu ne.'' Abubakar Albalkhiy kuma ya ce: ''Watan Rajab watan shuka, watan Sha'aban watan ban-ruwa ga shukar, watan Ramadan kuma watan girbe shukar ne. Wanda bai yi shuka a Rajab ba, bai bayar da ruwa ga shuka a Sha'aban ba, ta yaya zai yi girbi a Ramadan?''

Kuma ya ce: ''Misalin Rajab kamar iska ce, misalin Sha'aban kuma kamar girgije ne, sannan misalin Ramadan kamar ruwan sama ne.''

Ya kai Musulmi! Rajab ya wuce me kake aikatawa a Sha'aban, idan kana nufin girbi a Ramadan? Ka dai ji halin Annabinka (SAW) da halin magabatan kwarai na wannan al'umma a cikin wannan wata, a wane matsayi kake game da wadannan ayyuka da darajoji? Ka yi sauri, ka yi gaggawa zuwa ga da'a ga Mabuwayi Mai yawan gafara.

Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah gare ni da ku, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa dacewarSa da ni'imarSa. Na shaida ba wanda za a bauta maSa da gaskiya sai Allah Shi kadai girmamawa ga sha'aninSa. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai kira zuwa ga yardarSa. Allah Ya kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da 'yan uwansa.

Bayan haka, ku sani-ya bayin Allah!- Lallai akwai shiriya da haske a cikin Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (SAW). bata da kuma rudu suna cikin abin da yake sabaninsu; ''To wanda ya bi shiryarwaTa, ba ya bacewa, kuma ba ya wahala. Kuma wanda ya bijire daga ambatoNa, (Alkur'ani), to, lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar kiyama yana makaho.'' (k: 20: 23-24).

Bayin Allah! Daga cikin manyan abubuwan da mutum zai tarbi Ramadan da su a watan Sha'aban akwai abin da dabarani da Ibnu Hibban suka ruwaito daga Mu'azu bin Jabal (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: ''Allah Yana duban daukacin bayinSa a daren rabin Sha'aban, sai ya gafarta wa dukkan bayinsa, face mushiriki da muhashin.''

Don haka ku tsare tauhidinku, ya ku bayin Allah! Kada ku yarda babba ko karamar shirka su warware shi. Ku tsarkake kawunanku daga rowa da keta da bakin rai da kuncin zuciya. Domin Allah Madaukaki Yana gafartawa a daren rabin Sha'aban ga dukkan bayinsa face mushiriki da muhashin. Kashedinku da yi wa Allah shirki, mu binciki kawunanmu, domin ta yiwu dayanmu an jarrabe shi da wani abu daga shirki amma bai sani ba. Mushiriki shi ne wanda ya bauta wa wanin Allah da kowane nau'i na ibada. Wanda ya kirayi wanin Allah ko ya yi bakace da shi, ko ya yi yanka dominsa ko makamancin haka na daga ayyukan ibada, hakika ya yi shirka, kuma ya cancanci ukuba, ita ce rashin samun gafara da tabbata a wuta. Allah Ya ce: ''Lallai shi wanda ya yi wa Allah shirki, hakika Allah Ya haramta masa Aljanna kuma makomarsa wuta ce, azzalumai ba su da wani mataimaki.'' (k5:72). Kuma Allah Ya ce: ''Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirki da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai haka ba, ga wanda Ya so. Wanda ya yi shirki da Allah, hakika ya bace, bacewa mai nisa.'' (k:4:116).

Muhashin shi ne mai gaba ko mai husuma ko mai yanke zumunta ko mai juya baya a fagen jihadi ko mai hasada ko mai kullatar mutane a zucci. Dukkan wadannan siffofi ne na muhashin. Kuma suna jawo rashin samun gafara.

An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) a Hadisi Marfu'i cewa: ''Ana bude kofofin Aljanna a ranakun Litinin da Alhamis, sai a gafarta wa kowane bawa da ba ya shirki da Allah, face wanda ya kullaci dan uwansa. Sai Ya ce: ''Ku dubi wadannan biyu har sai sun sulhunta.'' Muslim ya ruwaito. Daga Abu Sa'alabata Al-Khushni daga Annabi (SAW) ya ce: ''Lallai Allah Yakan duba bayinSa a daren rabin Sha'aban, sai Ya gafarta wa muminai, Ya yi wa kafirai talala, sannan Ya kyale masu hasada da kullatar juna da hasadarsu ko kullatarsu, har sai sun bari.'' dabarani ya ruwaito, kuma shi ne Hadisi na 1144 a Silsilatus Sahiha. kullin da ake nufi shi ne yanke zumunta da bata tsakanin mutane.

Annabi (SAW) ya ce: ''Wata cuta ta al'ummar da ta gabace ku, za ta shigo cikinku: Hasada da gaba. Ita mai askewa ce. Ban ce tana aske gashi ba, a'a tana aske addini. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba, har sai kun so juna. Ko kuna son in nuna muku abin da zai sa ku so juna? Ku yawaita yin sallama (ko zaman lafiya) a tsakaninku.''

Don haka hada shirka da kullata na nuni da cewa dukkansu suna aske addini su bata shi. Bambanci kawai shi ne shirka na bata addini ba ta barin komai daga gare shi, yayin da gaba da hasada da yanke zumunta da sauransu suke fatattaka shi su bar shi ba ya da ruhi, koda ba su tuttuge shi daga tushe ba. kullata da hasada suna bata addini suna aske shi. Hasada da keta da kullata ba su shiga zukata face sun zama sababi na raunin imani, kuma suna iya raba mutum da imani baki daya, kamar yadda ya faru da Iblis lokacin da ya yi hasada ya kullaci Annabi Adam (AS). Don haka Allah Ya yi gargadi mai karfi kansu, Ya ambace su tare da zunubi mafi girma wato shirka. Domin shirka tana bata alakar mutum da Ubangijinsa, yayin da kullata da hasada ke bata alakarsa da 'yan uwansa muminai. Idan alakar mutum ta baci a tsakaninsa da Ubangijinsa da kuma muminai, shi ke nan babu abin da ya saura a addininsa. Ta yaya Allah zai gafarta masa?! Don haka ne aka haramta masa falalar wancan dare mai albarka.

Ku saurara! Wadansu mutane sukan kebance ranar dare rabin Sha'aban da azumi da tsayuwar dare da wasu nau'o'in addu'o'i da zikirori da rera wakoki. To dukkan wadannan ba su tabbata ba daga Hadisin Annabi (SAW). Iyaka an samu hakan ne ko a Hadisi mai rauni ko kirkirarre da aka yi wa Annabi (SAW) karya, kamar yadda Ibnu Rajab da wadansu suka ce. Dukkan wadannan (Hadisai) ba a kafa hujja da su, kuma ba a aiki da su a hukunce-hukunce.

Amma duk mutumin da ya saba tsayuwar dare, to, ba zai bar tsayuwar daren a wannan ranar ba. Kuma duk wanda ya saba yin azumin nafila, idan ya dace da daren rabin Sha'aban, sai ya yi azuminsa ba zai bari ba. Haka ma wanda ya saba azumi a Sha'aban ya azumce shi (ranar rabin Sha'aban) yana mai koyi da Annabi (SAW). Ku tafi a kan shiriyar Annabinku (SAW) wadda take sadarwa zuwa ga Aljanna. Ku kiyayi hanyoyin bata da bidi'a, masu sadarwa zuwa ga gidan halaka.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 09 @ 19:07:09 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Sha'aban: Da Kintsa Wa Ramadan 02" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: