Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
[ Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi ]

·Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)
·Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi
·Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto
·**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)
·IBN TAIMIYYAH GWARZON NAMIJI. (Misbahu Abdullahi)
·Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi'ah
·AA'SHUURAA (1) BANDA BIDI'AR SHI'AH BANDA KUMA BIDI'AR NAASI
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Ta'addanci Bai Da Madogara A Musulunci (2)
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Daga Imam Murtada Gusau - Masallacin Juma'a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi

Ta'addanci Bai Da Madogara A Musulunci (2)

A yau masu wuce iyaka sun zamo marasa hakuri da tarihi kuma sun zamo marasa hakuri da sa ran samun rahamar Allah. Sheikh Abdulhakim Murad ya yi bayani kan wannan batu a cikin wani rubutu nasa mai suna ''Biyayyar Musulmi da yadda suke.'' Na tsakuro wasu muhimman bayanai da ya rubuta kamar haka:

''Samun nasara a Makka ba ya zo ne ta hanyar fusata da gaggawa da firgitawa da barna a lokacin wahala ba, a wasu lokuta Musulmi sun shiga tsaka mai wuya, sun kasance karamin tsibiri a tsakiyar tekun kafirci da arnanci. Sun samu nasara ce ta hanyar kwantar da hankalinsu da biyayyarsu. Ibnu Juzi ya bayyana mana cewa wannan yana nufin karfin halinsu da sadaukar da kai da kuma tausayawarsu. Wadannan baiwoyi ne na dogaro ga alkawarin Allah a lokacin da ake cikin tsanani. Sabaninsu su ne wadanda aka bayyana da: ''Suna mugun zato ga Allah,'' wadanda malama tafsiri suka ce, hakan na nufin zargin Allah Zai kunyata muminai. Alhali Allah Madaukaki ba Zai kunyata muminai ba, kamar yadda Ya sha nanatawa a cikin Alkur'ani Mai girma: ''Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, alhali kuwa ku ne mafiya daukaka, idan kun kasance masu imani.'' (k:3:139).

An saukar da wannan aya ce bayan nasarar da kafirai suka samu kan Musulmi a yakin Uhudu. Don haka matashi mai gaggawa, da kan yi amfani da rabin hankalinsa wajen fassara Sunnah da muguwar fassara tunaninsa game da tarihin al'ummarsa shi ne an yi watsi da ita – wato Allah Ya yi watsi da ita kacokan.'' Wannan shi ne takaitaccen abin da na cirato daga rubutun Sheikh Abdul Hakim Murad.

Ya 'yan uwa Musulmi! Duk wanda ya yi ta'addanci a kan mutane mai laifi ne koda da wane suna suka kira kansu. Fushi da kiyayyarsu ne suke rinjayarsu. Tunaninsu ya sa sun makanta daga yakini da dogaro ga Allah, don haka suke yanke wa kansu hukunci. Kuma babu wata nasara da za su samu ta haka. Wajibi ne mu karantar da matasanmu hadarin batattun kungiyoyi da darikoki.

Huduba ta Biyu:

''Subhanallah walhamdu lillah wa la haula wa la kuwwata illah billah.''

'Yan uwa maza da mata! Me za mu yi rigakafi ko hana sake tashin bama-bamai, kuma ta yaya za mu dakatar da bata kyakkyawan sunan Musulunci?

1. Na farko, idan muka san akwai wanda yake kokarin kai hari, ko yana da hannu a ayyukan ta'addanci, mu hanzarta sanar da hukumomin tsaro. Aiki ne da Musulunci ya wajabta mana, kuma nauyi ne a kanmu a masayinmu na 'yan wannan kasa tamu Najeriya, kuma hakan zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyar kowa da kowa. Najeriya kasarmu ce, bai kamata mu lamunci aikin ta'addanci ba ko daga wane bangare ya fito, kuma bai kamata mu kawar da kai ko mu toshe kunne ba. Mu ko wani makusancinmu yana iya zama wanda harin zai shafa ko wanda suke son kashewa.

2. Mu zauna cikin shiri abin da ka iya biyowa bayan wannan lokaci na bakin ciki da zaman makoki. Fushi da zargin juna za su biyo baya, kuma mu Musulmi ne za a fi cutarwa. Tuni an kakkama Musulmin da ba su da laifi ana musguna musu ana cutar da su ana kai musu hari ana wulakanta su, an kai farmaki ga masallatai da makarantun Musulunci da dama. Don haka ya kamata kafafen watsa labarai da jami'an tsaro da coci-coci da sauran hukumomi su yi taka-tsantsan kada su musguna ko su yi kudin goro ga daukacin al'ummar Musulmi. Mu kuma a namu gefen mu yi namu kokarin. Kuma mu fito da karfin murya mu la'anci wannan mugun ta'addanci. Kuma wajibi ne mu rika ziyartar asibiti muna ba da taimakon jini mu rika rubuce-rubuce a jaridu kan illar haka mu bayyana matsayinmu a fili. Alhamdu lillahi, wata sabuwar kungiyar yaki da nuna kyama da bambanci ga Musulmi, wato Forum Against Islamophobia and Racism (FAIR), ta bude shafin intanet kuma tana gudanar da bincike kan duk hare-haren da aka kai wa Musulmi. Suna bayar da bayanai ga 'yan sanda, sai dai suna fama da karancin kudi don haka sun bukaci mu roke ku ku tallafa musu, don su ci gaba da gudanar da aikinsu.

3. Na uku, wajibi ne mu samar da ingantaccen shugabanci a tsakanin al'ummarmu. Akwai bukatar masu gudanar da masallatanmu ya zamo sun san yadda za su warware matsalolin addininmu da na rayuwarmu da bukatun iliminmu. Bai kamata kwamitocin masallatanmu su ci gaba da kasancewa kamar kulob na Musulmin da suka yi ritaya daga aiki ba. Al'ummarmu tana da wadatar mutane masu hazaka da kuma dukiya. Ya wajaba a yi amfani da wadannan domin amfaninmu.

4. Ya wajaba Musulmi su fahimci cewa neman ilimi da koyo abu ne da ked a dogon zango, a gidajenmu mu ci gaba da koyon ilimi don inganta rayuwarmu. Wajibi ne mu zama mazaje nagari da mata nagari, iyaye masu wayewa da 'ya'ya masu godiya. Manyan dabi'unmu na adalci da tausayi wajibi ne su karu a tsakaninmu da sauran jama'a a cikin dukkan al'amura, ga iyalanmu da al'ummarmu da kuma kasarmu. Kuma daga nan ne kyawawan dabi'un adalci da tausayi za su watsu a sauran kasashen duniya. Idan muka san abin da ya kamata mu yi, za mu kintsu kuma mu taimaki saura wajen gina al'umma da kasa. Kuma hakan zai fara ne daga daidaikunmu. Wannan hanya ta gina lafiyayyiyar al'umma mai tsaka-tsaki mai cike da daidakun mutane adalai Alkur'ani ya bayyana tad a ''Ummatan wastan'' wato ''Al'umma matsakaiciya.'' Kuma kamar yadda na fada a hudubar da ta gabata, ginshikin samun lafiyayyiyar al'umma matsakaiciya shi ne zuciyar taimakekeniya. Idan muka sanya Allah a zukatanmu za mu samu natsuwa ‘sakina' da kwanciyar hankali da tausayin juna. Wajibi ne koyaushe mu sanya Allah a zukatanmu, mu tuna gafala ba namu ba ne.

Shekarun farko na Musulunci a Makka kafin Hijira zamani ne da ke cike da kunci. An musguna wa Musulmi an ci zarafinsu kuma sun mutu saboda sun yi imani da Allah. Amma za ku ga surorin farko na Alkur'ani Mai girma sun fi mayar da hankali ne kan gina kyawawan dabi'u da tsarkake zuciya. Wannan babban mataki ne na kintsawa ta yadda Musulmi za su iya fuskantar manyan kalubalen da ke zuwa da fadada da samun nasara. Don haka Makka wadda take cike da makiyayan dabbobi ake ganin gidadawa ne ta sauya zuwa jagorar wayewa da ci gaba a duniya, kamar yadda maeri yake iya tace baki karfe daga zinare.

'Yan uwa maza da mata! Mu dauki halin kunci da hadarin da muke ciki ya zamo kamar na mutanen Makka, ta yadda za mu yi wankan tsarki ga al'ummarmu, mu kyautata kawunanmu mu zama al'umma matsakaiciya da Allah Yake so mu kasance. Magabatanmu na kwarai ba su cika damuwa damuwa da zahiri ba fiye da badini. Yayin da duniyarmu ke fashewa a kanmu, yanzu ba lokaci ba ne na tsayawa muna ta surutu kan dogon gemu ko fasalin suturarmu ba, (duk da cewa su ma bangare ne na Musulunci). Sahabban Annabi (SAW) ba su cika damuwa da tufafin da suka sanya ba, sai dai abin da ke cikin zukatansu.

Imam Murtada Gusau ya gabatar da wannan huduba ce a ranar Juma'a 7 ga Ramadan 1435 BH daidai da 4 ga Yuli, kuma za a iya samunsa a 08038289761 ko murtadagusau@gmail.com
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 09 @ 19:15:09 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Ta'addanci Bai Da Madogara A Musulunci (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: