Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Al'Adun Musulmi Da Darajoji
[ Al'Adun Musulmi Da Darajoji ]

·Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
·Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
·Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
·Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
·Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Rashawa: Tushen Ruguza Zaman Lafiya Da Yada Fasadi (2)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Sheikh Ibrahim bin Muhammad Al-Hakil

Rashawa: Tushen Ruguza Zaman Lafiya Da Yada Fasadi (2)

Masallaci: Ba a fada ba

Rashawa tana raunana haibar kasa har ta ruguje, masu aikata mujirimai su ci karfinta su rika yin abin da suka so, suna shiga da abin da suka ga dama na kayan maye da giya da makamai, su rika jawo zubar da jini da mutunci, su rika ta'adda a kan mutane, kuma babu abin da zai hana su yin haka, saboda rashawa tana bude musu kofofin da ake rufe musu, tana rufe idanuwan masu tsaron kasa, ta hana hannun jami'an tsaro kama su.

A wasu kasashen mujirimi zai aikata barna mutane su kama shi, amma sai 'yan sanda su sake shi, saboda yana mika musu, sai a mayar da tuhumar ga waninsa!

Hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na duniya sun san manyan masu safarar miyagun kwayoyi, jiragensu suna isa kansu, amma saboda suna ba su rashawa sai su sake su, su dawo suna kama kananan wakilansu.

Hakika barna tana watsuwa ne a tsakanin mutane idan rashawa ta samu gindin zama a tsakanin jami'an tsaro da masu tsaron kan iyakar kasa, (kwastam da jami'an shigi da fici da sojoji da 'yan sanda), idan kuma rashawa ta samu shiga a wurin masu gudanar da shari'a (alkalai da ma'aikatan kotu), to sai a boye shaida a boye gaskiya a ki yin adalci, zalunci ya watsu, dukkan wadannan abubuwa su ne sababin dauke zaman lafiya da aukuwar tsoro da dagulewar al'amura da tayar da wutar fitina da susucewar al'amura a duniya.

Da mutane sun san cewa rashawa tana rusa zaman lafiyarsu da kwanciyar hankalinsu, da wani daga cikinsu bai yi mu'amala da ita ba, saboda ya san rashin zaman lafiya da tashin hankali zai zo masa shi da matarsa da dansa da wanda yake so, kuma dukiyar da ya dauki lokaci yana tarawa ta hanyar rashawa ba za ta amfane shi ba, a lokacin da aka shiga tashin hankali da rudu!

Da mutane sun iya hango hadarin mai karbar rashawa a kan jama'arsu da kasarsu da zaman lafiyarta da kwanciyar hankalinta da ba su yi shiru kan mai cin hanci da rashawa ba, da sun yi kokarin yakar rashawar, amma jahiltar yadda karshen al'amura za su zo, ya sanya mutane suke kai kansu ga halaka ba su sani ba.

Hakika fasadi da rashawa sun kai matsayin da al'ummomi da kasashe da yawa suka kakkafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa. Kuma hatta kungiyoyin kasa da kasa suka kebe ranaku domin yaki da barna da cin hanci da rashawa. Wannan yana nuni da munin halin da dan Adam ya samu kansa na rayuwa a karkashin tsarin azzalumar al'umma. Tana yada fasadi da zalunci, sannan tana dariya ga dan Adam ta wajen kebe ranar yaki da fasadi da rashawar!

To, haka dama lamari zai kasance idan kasa tana hukunci da wanin shari'ar Allah Madaukaki, kuma tana wasa da kira zuwa ga addininSa, tana tozarta mabiya gaskiya. Ina neman tsarin Allah daga Shaidan jefaffe. ''Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da yaudara, face idan ya kasance daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kanku. Lallai ne Allah Ya kasance game da ku, Mai jin kai ne. Wanda ya aikata wancan (cin dukiya da karya da yaudara, kamar cin rashawa ko almundahana), bisa ta'adi da zalunci, to, za Mu kone shi da Wuta. Kuma wannan ya kasance ga Allah (abu ne) mai sauki.'' (k:4:29-30).

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah godiya mai dadi mai yawa mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu Yake so kuma Ya yarda. Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da mabiyansa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ku bi Allah da takawa kuma ku yi maSa da'a. ''Ku ji tsoron wani yini (a cikinsa) wani rai ba ya tunkude wa wani rai komai, kuma ba a karbar musanya daga gare shi, kuma wani ceto ba ya amfaninsa, kuma ba su zama ana taimakonsu ba.'' (k:2:123).

Ya ku Musulmi! Wanda ya nazarci nassoshin da suke hani da gargadi kan rashawa da almundahana da labarin masu cin rashawa da mahnadama da abin ya same su, zai san hadarin rashawa da cin dukiyar talakawa game da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma. Kuma zai gano hikimar da ta sa Allah Ya haramta ta kuma Ya yi hani da gargadi a kanta.

Hakika Allah Ya bijiro da labarin kafiran Bani Isra'ila a cikin Alkur'ani Mai girma, Ya ambaci cewa lallai su suna cin Suhtu wanda shi ne rashawa, kuma malamansu ba su hana su a kan hakan, har suka auka tare da su a cikinta. Ya kaiton tabewarsu da jin kunyarsu: ''Kuma kana ganin masu yawa daga gare su, suna tseren gaggawa a cikin zunubi da zalunci da cinsu ga haram. Hakika, tir da abin da suka kasance suna aikatawa. Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hana su daga fadarsu ga zunubi da cinsu ga haram (rashawa) ba? Hakika, tir da abin da suka kasance suna sana'antawa.'' (k:5:62-63).

Ya kasance daga alamomin hannun malamansu a cikin rashawar, akwai kasancewar malamansu sun boye gaskiya, sai suka cancanci fushin Allah Madaukaki da azabarSa. ''Lallai ne wadanda suke sayen 'yan tamani kadan da alkawarin Allah da rantsuwoyinsu, wadannan babu wani rabo a gare su a Lahira, kuma Allah ba Ya yin magana da su, kuma ba Ya dubi zuwa gare su, a Ranar kiyama, kuma ba Ya tsarkake su, kuma suna da azaba mai radadi.'' (k:3:77).

Kuma hakika Allah Madaukaki Ya yabi wadanda suka yaki rashawa da almundahana daga cikinsu, suka bayyana gaskiya da ta wajaba a kansu, su ne 'yan kalilan idan aka kwatanta da masu cin rashawar: ''Kuma lallai ne daga Mutanen Littafi, hakika akwai wadanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu tawali'u ga Allah, ba su sayen tamani kadan da ayoyin Allah. Wadannan suna da ijararsu a wurin Ubangijinsu. Lallai ne Allah Mai gaggawar sakamako da yawa ne.'' (k:3:199).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 09 @ 19:23:52 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Rashawa: Tushen Ruguza Zaman Lafiya Da Yada Fasadi (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: