Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Tsokaci Dangane Da Zumunci Da Muhimmancinsa (2)
 
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga Ahmad Muhammad

Tsokaci Dangane Da Zumunci Da Muhimmancinsa (2)

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya halicce mu kuma Ya sanya mu cikin Musulmi. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga bawanSa, ManzonSa, Annabi Muhammad, wanda ya kawo mana cikon addinin Musulunci, tare da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka, yau ma ga ci gaban tsokacinmu dangane da lamarin zumunci da fata Allah Ya sa mu amfana da shi, duniyarmu da Lahirarmu.

In ana biye da mu, a makon jiya, mun gabatar da Hadisin Abu Ayyub al-Ansari na mutumin da ya tambayi Manzon Allah (SAW) kan abin da zai yi ya shigar da shi Aljanna, aka jera masa wsu ayyukan ibada, wadanda cikinsu har da sada zumunci. Sannan ga Hadisin da Imam Baihaki ya ruwaito a cikin littafin Shu'abul Iman, mai cewa, ''Jinkan Allah ba zai sauka a kan mutanen da a cikinsu akwai wanda yake yanke zumunci ba.'' Wanda a dalilinsa ne ma aka gabatar da labarin sahabi Abu Huraira a yayin da ya bukaci duk wanda ya san ya yanke zumunci a taronsu da ya bar wurin saboda za a yi addu'a.

A karshe aka nuna cewa yanke zumunci wani nau'in zalunci ne wanda yake da girma, musamman da yake al'amari ne na yanke wata igiyar 'yan uwantaka ta soyayya da kauna da shaukin juna. Ga ci gaba:

Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayyana irin narkon da ke fadawa kan lamarin yanke zumunci, inda ya ce, ''kullin zumunci, wata sarkakkiyar dangantaka ce, wadda ta tuzgo daga Allah, Mai rahama. Zumunta ta ce, ‘Ya Ubangiji! An zalunce ni, ya Ubangijina! An yanke ni…' Sai Allah Ya amsa mata, ''Ba za ki wadatu ba, idan na yanke duk wanda ya yanke ki, kuma in kula da duk wanda ya kula da ke?'' (Imam Buhari ne ya ruwaito shi).

Hasali ma dai Allah, Mai girma da daukaka, Ya daukaka matsayin kulla zumunci, Ya ba shi matsayin rahmu, wanda yake da tushe daya daga cikin sunayenSa na Arrahman, a yayin da Ya ce, ''Ni ne Arrahman (Mai rahama - tausayi), kuma Na halitta rahmu (zumunta), Na ciro sunanta daga sunaNa. Duk wanda ya kula da ita, Zan kula da shi, kuma duk wanda ya yanke ta, Zan wofinta da shi.'' (Hadisin kudsi, wanda Buhari ya fitar da cikin littafinsa Al-Adab Al-Mufrad, Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi sun ruwaito shi).

Wannan yana nuna wa Musulmi mai hankali, irin muhimmancin da sada zumunta ke da shi, musamman ma da yake Allah Zai kula da shi, Ya kare shi, idan ya kula da sha'anin zumunci. Zai dandani zakin jinkan Mahaliccinsa. Wanda kuwa ya yanke igiyar zumunci, zai shiga cikin matsalar da bai san iyakarta ba, musamman domin Allah Zai wofinta da shi, ya daidaita. Allah Ta'ala Ya kare mu daga fadawa cikin ramin yanke zumunci.

Shi Musulmi na kwarai yana kula da zumunci ne, ya rike shi sosai a karkashin koyarwa ta addinin Musulunci, ta yadda ba zai bari kyale-kyalen duniya na dukiya ko iyali (mata da'ya'ya) ya dauke hankalinsa, har ya juya wa danginsa baya ya kyale su, ya ki girmama matsayinsu ko ya taimaka musu ba. Zai kula da su ne gwargwadon yadda tsarin addininsa na Musulunci ya koyar da shi, wato bayan mahaifansa, wadanda uwa ita ce kan gaba wajen kulawa a matakai biyu; sai uba, sannan dangi na kusa da na nesa.

Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi tambaya, ''Ya Manzon Allah! Wa ya fi cancantar kulawata?'' Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''Mahaifiyarka; mahaifiyarka; mahaifiyarka; sannan mahaifinka; sannan danginka na kusa.'' (Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin).

Duk Musulmin da yake kyautata wa danginsa, yana samun lada ribi biyu ne: daya don zumunci, dayan kuma don kyautatawar da ya yi, lamarin da zai karfafa masa gwiwar kula da dangin nasa a duk lokacin da suke da bukata kuma yana da halin da zai taimaka musu din. Wannan shi ne ake kira dadi biyu, wato ga dai Allah Yana farin ciki da shi, ga kuma danginsa suna na'am da al'amarinsa cikin soyayya da girmamawa.

Wannan dabi'a ita ce Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci Musulmi da su yi kuma ya karsasa lamarinsu a kan haka, kamar dai yadda ya zo a wani Hadisin Zainab Assakafiyya, matar Abdullahi dan Mas'ud, (Allah Ya yarda da su). Ma'aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''Ya ku mata! Ku ba da sadaka koda daga cikin gwala-gwalanku ne.''

Jin haka ya sa Zainab ta tafi wajen mijinta ta bukaci ya je wajen Manzon Allah (SAW) ya tambaya ko ya dace ta ba shi sadaka tunda ba shi da wadata, sai ya ba ta iznin ita ta je ta tambaya. A lokacin da ta tafi wajen Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ta iske wata mata daga cikin Ansarawa, ita ma ta je da kwatankwacin bukatar ba mijinta sadaka. Sai suka aiki Bilal, (Allah Ya yarda da shi), don ya tambayo musu Manzon Allah (SAW) kan wannan bukata tasu, sai Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''Za su samu lada biyu; ladar kyautata zaman tare da kuma ta sadaka.'' (Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin).

Sau da yawa Manzon Allah (SAW) yakan karfafa bayar da muhimmanci kan abin da ya danganci kyautatawa ga dangi da zarar bukatar haka ta samu. A yayin da aka saukar da aya ta 92 cikin surar Al-Imran, mai cewa, ''Ba za ku samu kyautatawa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so…'', sai sahabi Abu dalha (RA) ya tafi wajen Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''Ya Manzon Allah! Ga abin da Allah Ya ce (a wannan aya), ni kuma abin da ya fi soyuwa gare ni a cikin dukiyata ba kamar gonata Bayraha (gonarsa ce ta dabino da take da rijiya mai ruwan dadi, wadda har Annabi kan shiga ya sha ruwan), na bayar da ita sadaka saboda Allah da fatar in samu lada daga gare Shi, sai ka yi yadda ka so da ita.''

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, ''A gaishe ka namiji! Ka kuwa samu gwaggwabar riba a wannan ciniki naka. Na ji abin da ka ce, amma ina ganin sai ka raba ta tsakanin danginka.'' Haka kuwa ya yi! (Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin).

Shi sha'anin nan na zumunta yana yin naso ne har ya kai ga kyautatawa da girmama dangin-dangira, wato wadanda suke da kowane irin nisancin kusanci da wadanda ake dangantaka da su. Haka abin yake idan muka yi dubi da irin jan hankalin da Manzon Allah (SAW) ya yi wa sahabbansa kan su kyautata wa mutanen Masar, idan sun ci su da yaki, saboda surukutar da ke tsakaninsu, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito.

Malamai sun fassara wannan al'amari da Hajara mahaifiyar Annabi Isma'il, (Amincin Allah ya tabbata gare su), da Mariya Al-kibdiyya, mahaifiyar Ibrahim dan Manzon Allah (SAW), wadanda dukansu biyun, sun fito ne daga Masar.

Madallah kuwa da irin wannan kyakkyawar dabi'a, wadda har wadansu na nesa ma suke samun alherinta, saboda haka ba abin mamaki ba ne a ga Musulmi na kwarai yana dokin ya ba danginsa hakkokinsu kamar yadda ya kamata, kuma ya kyautata musu.

Allah Ya tabbatar da duga-duganmu cikin wannan addini na Musulunci.

Za mu ci gaba
 
 
 Posted By Aka Sanya A Wednesday, December 09 @ 19:31:52 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Tsokaci Dangane Da Zumunci Da Muhimmancinsa (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: