Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
[ Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen ]

·Illolin zina da luwadi da madigo (1)
·Layya da hukunce-hukuncenta
·Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
·Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
·Menene Hunkunci Azumtar Watan Rajab??

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Yadda Ya Kamata Musulmi Ya Fuskanci Fitina Da Jarrabawa (3)
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi Sheikh Ibrahim bin Muhammad Al-Hakil - Masallacin Juma'a na Al-Mukil

Yadda Ya Kamata Musulmi Ya Fuskanci Fitina Da Jarrabawa (3)

Hamdala da taslimi:

Bayan haka, ku ji soron Allah Madaukaki ku yi maSa da'a, kuma ku tsayar da addini a gare Shi, ku mika maSa wuya ku mayar da hankalinku gare Shi. Domin babu wurin gudu babu matsera face gare Shi. Babu mai kubutarwa daga abubuwan ki face yin addu'a a gare Shi. Babu tabbata a kan gaskiya face da tabbatarwarSa. Babu karfi babu dabara ga bayi face naSa. ''Ku yi da'a ga Allah kuma ku yi da'a ga Manzon (Allah), idan kuka juya baya abin sani babu wani abu a kan ManzonMu face isarwa mabayyaniya. Allah Wanda babu abin bautawa da gaskiya face Shi, kuma a kan Allah sai muminai su dogara.'' (Tagabun:12-13).

Ya ku mutane! A lokacin da bakin ciki ya sauka ga bawa, bai damuwa da abinci da abin sha da barci, har sai ya kawar da ita ko ta gushe masa, zai yi ta neman wanda zai taimaka masa a kanta. Lokacin da mutanen Annabi Lud (AS) suka kewaye shi suna nufin yin ta'addanci ga bakinsa sai ya ce: ''Ina ma ina da wani karfi (da zan hana ku) ko kuma in koma ga wani rukuni mai karfi (da za su taimake ni).'' (Hud:80). Annabi (SAW) ya ce ''Allah Ya yi rahama ga Lud. Hakika ya koma ga wani rukunin mai karfi.''Muttafakun. Yana nufin rukunin Allah Madaukaki wanda duk ya nemi tsari da Shi ba ya jin kunya. Hakika Lud (AS) da sauran Manzanni (AS) sun nemi tsari da Shi, kuma Allah Madaukaki Ya kubutar da su, kuma Ya hallakar da masu karyatawa.

Lallai duniya gidan bala'i ne ga bayi, gidan jarrabawa da wadata da tsanani. ''Kuma za mu jarraba ku da sharri da alheri a matsayin fitina, kuma gare Mu kuke komawa.'' (Anbiya:35). Wannan bala'in daga ciki akwai wanda yake shafar mutum shi kadai kamar talauci da ciwo da damuwa da kunci da makamanansu. Kuma akwai bala'in da ke game jama'a ya shafi gari ko ya watsu ya shafi kasashe ko ya kasance mafi watsuwa ya shafi daukacin duniya.

Bisa lura da masdarinsa, bala'i na iya kasncewa kaddara yanke ta yadda dan Adam bai iya yin komai a kai, koda ya kasance saboda zunubansu ne ya same su kamar girgizar kasa da ambaliyar ruwa da annoba da makamantansu. Akwai kuma abin da ke aukuwa sakamakon zaluncin dan Adam ga dan uwansa, kamar jawo yunwa da talauci da asara da boye kaya da kai hare-haren ta'addanci da sauransu.

Wadannan masifu da bala'o'i suna karuwa kuma suna tagayyara muminai a tsawon zamunna, wannan saboda ka'idar nan ce da ke cewa ''Babu wata shekara face mai biye mata ta fi ta sharri, har sai kun koma ga Ubangijinku.'' Kamar yadda Annabi (SAW) ya ba da labarin haka.

Idan aka lura bala'o'in wannan lokaci, aka lura da masifu a jumlatance, aka bibiye su, za a ga bala'o'i ne da suke shafar mutane da yawa, ja'ircinsu na kawo halaka mai yawa da talauci da wargajewar al'amura, 'yan kasuwa su rasa dukiyarsu baki daya ko mafi yawanta, tsoro mai tsanani ya lizimce su, suna haifar da masifu masu yawa da dayansu ke buwayar masu karfi, to ina ga a ce dukkansu sun hadu?

A lokacin da wadannan masifu suka rika maimaituwa a kasashe da dama, sai wadanda ba su isa gare su ba, su rika tsoron haduwa da su, musamman idan masana da kwararru suka ba da labarin cewa bala'i da annoba da alamun ambaliya ko girgizar kasa suna karuwa, inda masana rayuwa da harkokin siyasa da masu hangen nesa za su hadu kan cewa za a fuskanci matsaloli a fagen tattalin arziki da siyasa da zamanakewar kasa nan gaba.

Don haka babu abin zargi a kan mutane idan suka ji tsoro kan rayuwarsu da 'ya'yansu da gidajensu da dukiyarsu, suka rika tunanin abin da zai faru da su a gaba. Domin jin dadin rayuwa tana tare da zama lafiya ne a koyaushe, kamar yadda tabarbarewar rayuwa ke tare da susucewar zaman lafiya da azabar rayuwa da tashin hankali.

Sai dai duk da haka, lallai muminai suna da wurin fakewa da suke komawa gare Shi. Idan suka nemi tsari da Shi, Shi mai tsarewa ne, idan suka lizimce Shi, zai lizimce su. Shi ne ke ba da kariya idan rayukan da suka fada cikin matsala suka yi imani da Shi. Zukatansu suka natsu da Shi, koda sauran mutane sun kauce maSa.

Lallai wannan abu shi ne tawakkali (dogaro) ga Allah Madaukaki. Duk lokacin da zuciyar bawa ta kullu a kan imani da yakini, ta cika da tawakkali ga Allah, ba ta ta'allaka da kowane sababi ko yaya yake ba, ba ta yi kwadayin komai daga wanin Allah ba, kuma ba ta tsoron waninSa. Ya zamo zuciya tana sane cewa duk abin da ya auku bisa kaddararSa ce Madaukaki, kuma dukkan komai yana karkashin tankwarawarSa da karfinSa Mai girman daraja. Suna masu mika wuya ga hukuncinSa da umarninSa Madaukaki. A lokacin ne rayuka za su samu hutu su iya magance bala'insu, kirjinsu ya fadada, zukatansu su samu natsuwa, ba su tsoron kowa, ba su tsoron aukuwar komai, hakika Allah Madaukaki Ya ce: ''An kankare musu kananan zunubansu, kuma an kyautata rayuwarsu.'' (Muhammad:2).

Duk wanda aka kyautata masa, sai tunaninsa ya daidaitu shu'urinsa ya daidaitu, zuciyarsa da lamirinsa su natsu, ransa ya samu aminci da zaman lafiya.

Ibnu kayyim (RH) ya ce: ''Tawakkali ga Allah hakikanin tawakkali wajen gusar da dutse daga muhallinsa, da ya kasance abin umarni da kawar da shi zai kawar da shi.''

Tawakkali ga Allah ne ya sa Annabawa (AS) suka samu nasara kan duk masifun da suka same su da duk wahalar da ta mamaye su. Sun sanya tawakkali guzurinsu a lokacin tsanani, sun rike shi makamin yakar ma'abuta kaidi. Mutanen Annabi Ibrahim (AS) sun taru sun hura wuta ganga-ganga domin kone shi, amma sai aka tserar da shi daga gare ta saboda tawakkalinsa ga Allah!

Sannan kungiyoyi sun hadu a kan Annabinmu Muhammad (SAW), sai Allah Ya kunyata su, saboda tawakkalinsa ga Allah Madaukaki. Ibnu Abbas (RA) ya ce: ''Hasbunallhu wan ni'imal wakil'' Annabi Ibrahim ya fade ta lokacin da aka jefa shi a wuta, kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fade ta lokacin da suka ce: ''Lallai mutane sun hadu (domin yakarku) don haka ku ji tsoronsu, sai (hakan) ya kara musu imani, kuma suka ce: ''Hasbunallahu wan ni'imal wakil. (Allah ne Ma'ishinmu kuma madallah da Abin dogaro)'' (Al- Imran: 173). Buhari da Muslim suka ruwaito.

Kuma a lokacin da aka kori Annabi Musa (AS) da muminan da suke tare da shi, aka kewaye su suka ji tsoron halaka, ga Fir'auna da rundunarsa a bayansu, kuma ga teku a gabansu, sai tawakkalin Annabi Musa (AS) ga Ubangijinsa ya zamo sauki da sababbin kwaranye musu bakin cikinsu da ceto rayukansu. ''A lokacin da jama'ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce, ''Lallai mu ababen riskewa ne.'' Sai ya ce: ''Ba haka ba ne! Lallai ni ina tare da Ubangijina kuma da sannu Zai shiryar da ni (yadda za mu tsira). Sai Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa ka bugi tekun da sandarka, sai ta dare kowane bangare ya zamo kamar wani dutse mai girma.'' (Shu'ara:61-63).

Haka Annabi Yakubu (AS) ya nuna tawakkali lokacin da ya ji tsoron shaidanun mutane da aljanu a kan 'ya'yansa, sai ya yi musu wasiyya sannnan ya ce: ''Ba na iya wadatar muku komai daga Allah, hukunci dukkansa na Allah ne, a gare Shi nake dogaro kuma masu tawakkali su dogara a gare Shi.'' (Yusuf:67).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 14:08:26 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"Yadda Ya Kamata Musulmi Ya Fuskanci Fitina Da Jarrabawa (3)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: