Muhawara Hausa
 



Maraba Da Manzon Rahama (1)
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Daga Muhammad Habibullah Muhammad Shakidiy

Maraba Da Manzon Rahama (1)

Godiya da taslimi.

Bayan haka ya bayin Allah! Hakika Allah Ya yi mana rahama mayalwaciya sakamakon kebe mu da sanya mu mabiya mafi alherin halitta (SAW), wanda ya fitar da mu daga duffan kafirci da zalunci zuwa ga hasken imani, ya fitar da mu daga bata zuwa ga shiriya ya fitar da mu daga tabewa zuwa ga sa'ada daga kaskanci da zalunci da jahilci da rarrabuwa da wulakanci zuwa ga daukaka da adalci da haduwar kai da karimci. Shin yaya za mu kasance ba domin addinin Annabi Muhammad da akidarsa ba? Wace kima za mu yi in ba domin sakonsa da shari'arsa ba? Wace makoma muke da ita in ba domin da'awarsa da akidarsa ba? ''Lallai ne hakika, Allah Ya yi babbar falala a kan muminai, domin Ya aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littafi da hikima, kuma lallai sun kasance daga gabani, hakika suna cikin bata bayyananniya.'' (k:3:164).

Ya isar da sako mafi kyawun isarwa, ya bayar da amana, kuma ya yi nasiha ga al'umma, kuma ya yi kokari a cikin yada addinin Allah iyakar kokarinsa. Mutanensa sun cutar da shi, amma ya yi hakuri domin ya isar da wannan sako. Ya tafi zuwa da'ifa da kafa yana mai gabatar da Musulunci ga kabilunta, amma suka sanya kananan yaransu suka rika jifarsa suka raunata shi a kafarsa amma ya yi hakuri don isar da da'awar. 

Ya rika zuwa ga kabilun Larabawa amma suna korarsa, sai dai irin wannan bai kashe masa gwiwa ba. An rika azabtar da sahabbansa a cikin zafin rana suna masu igasa da Allah Madaukaki saboda wannan addini. Har ta kai an umarce shi da hijira daga garin Makka inda ya tsaya a wajen Makka yana mai cewa: ''Wallahi ke ci mafi soyuwar bigire zuwa ga Allah. Kuma wallahi ke ci mafi soyuwar bigire a wurina, ba domin mutanenki sun fitar da ni ba, da ban fita ba.''

Wata rana an fasa masa kai, an karya masa hakoran gaba, makiya sun yi yunkurin kashe shi a yakin Khandak, inda suka tura rundunoni domin neman kansa. Yahudawa sun sanya masa guba ko sammu a abinci, sun yi kokarin kashe shi a lokuta da dama. Sai dai wannan ba sanyaya azamarsa ta yada wannan addini ba, har sai da Musulunci ya isa mahudar rana da mafadarta.

Ba za a iya kirga falalolinsa ba, kuma martabobinsa ba za su kididdigu ba. Babu wata siffar kamala face ya siffatu da ita, Allah Ya tsarkake hankalinsa inda Ya ce: ''Ma'abucinku bai bata ba, kuma bai ketare haddi ba.'' (k:53:2). Kuma Ya tsarkake harshensa inda Ya ce: ''Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa.'' (k:53:3). Kuma Ya tsarkake shari'arsa inda Ya ce: ''(Maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa.'' (k:53:4). Kuma Ya tsarkake mai karantar da shi inda Ya ce: (Mala'ika) mai tsananin karfi ya sanar da shi. Ma'abucin karfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.'' (k:53:5-6). Kuma Ya tsarkake zuciyarsa inda Ya ce: ''Zuciyar (Annabi) ba ta karyata abin da ya gani ba.'' (k:53:11). Kuma Ya tsakake ganinsa inda Ya ce: ''Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ketare haddi ba.'' (k:53:17). Kuma Ya tsarkake sahabbansa inda Ya ce: ''Kuma wadannan da suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu.'' (k:48:29). Kuma Ya tsarkake shi gaba dayansa inda Ya ce: ''Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki manya.'' (k:68:4).

Kuma Ya jingina shi da risala inda Ya ce: ''Muhammadu Manzon Allah ne.'' (k:48:29). Kuma Ya kira shi da sunan annabta inda Ya ce: ''Ya kai Annabi!'' (k:60:12). Kuma Ya daukaka shi da bauta inda Ya ce: ''Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi tafiyar dare da bawanSa.'' (k:17:1). Kuma Ya yi masa shaida da tsayuwa da ibada inda Ya ce: ''Kuma lallai ne shi a lokacin da bawan Allah ya tsayu yana kiranSa.'' (k:72:19).

Allah Ya budada masa kirjinsa Ya dake masa nauyinsa, Ya daukaka ambatonsa Ya cika al'amarinsa Ya kammala addininsa, Ya sanya damarsa mai da'a. Ubangijinsa bai yi masa ban kwana ba, kuma bai ki shi ba. Sai dai ya same shi ba ya da shari'a, sai Ya shiryar da shi, Ya same shi fakiri Ya wadatar da shi, kuma Ya same shi maraya Ya yi masa makoma. Ya ba shi zabi tsakanin dawwama a duniya da haduwa da Shi, sai ya zabi haduwa da Majibincinsa ya ce: ''Na zabi haduwa da Madaukaki.''

Na rantse da Allah ba ta yi ciki ko ta haifi,

kamar Manzo, Annabin al'umma mai shiryarwa.

Sai ga shi wata rana ta zo, wasu mutane da ba su san Allah ba koda daidai da sa'a daya suna rayuwa cikin duffan sha'awoyi, manufofinsu da tunaninsu da akidojinsu batattu suna kokarin karkata daga wannan haske. Misali wata jaridar Denmark da sauransu sun buga zanen hoto na isgilanci ga mafificin halitta daukacin Musulmi na ji na gani, ina kishin addinin? Ina son Manzon (SAW)? Ina kare shi? Ashe ba wannan ne matsayin shugabanmu Manzon Allah (SAW) ba?

Wadannan Allah zai yi musu kamun ramuwa, domin Ya ce a cikin LittafinSa: ''Kuma Allah Yana tsare ka daga mutane.'' (k:5:67). Utbah dan Abu Lahabi ya cutar da shi ya yi masa isgili sai ya ce: ''Ya Ubangiji! Ka shushuta masa wani kare daga cikin karnukanka.'' Sai ya zamo bai iya barci sai a tsakiyar 'yan uwansa saboda tsoron addu'ar Manzon Allah (SAW), amma wannan bai kare shi ba, domin a daya daga cikin tafiye-tafiyensa sai ya farka ya ga mafadacin zaki ya sanya faratunsa a mukamikinsa, sai ya fasa ihu yana cewa: ''Yak u mutanena! Addu'ar Muhammad ta kashe ni.'' Kuma wannan bai wadatar da shi da komai ba.

Kisra yake ta wasikarsa sai ya yi masa addu'a, sai Allah Ya halaka shi a zamaninsa, Ya kekketa mulkinsa kekketawa, mulki bai sake komawa hannun kisrawa ba a bayansa, domin tabbatar fadinSa Madaukaki: ''Lallai mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.'' (k:108:3). Domin haka duk wanda ya zage shi ko ya tozarta shi ko ya nakasa shi ko ya yi gaba da shi, to lallai Allah zai karya kashin bayansa Ya debe albarka a idonsa da zuriyarsa. Ya zo a cikin Sahihu daga Annabi (SAW) cewa lallai ya ce: ''Allah Madaukaki Yana cewa, duk wanda ya yi adawa da wani waliyiNa, hakika Na yi masa izini da fafata yaki da Ni.'' To yaya kuma wanda ya yi adawa da Shugaban Annabawa (AS)?

Allah Ma'abucin Tsarki Yana cewa: ''Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.'' (k:15:95). Kan tafsirin wannan aya Ibinu Sa'ad (RH) ya ce: ''Hakika Allah Ya aikata haka, babu wanda ya bayyana isgili ga Manzon Allah (SAW) da abin da ya zo da shi face Allah Ya halaka shi, Ya kashe shi mugun kisa.'' Sannan dabarani a cikin Al-Ausad da Baihaki da Abu Nu'aim su biyun a cikin Ad-Dala'il da Ibinu Madawiyya da sanadi mai kyau da Ad-Diya'u a cikin Almukhtarat sun ruwaito daga Ibinu Abbas (RA) kan fadinSa Madaukaki: ''''Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.'' Ya ce: ''Masu isgilin su ne Walid bin Al-Mugira da Al-Aswad bin Abdu Yagusa da Al-Aswad bin Mudallib da Alharis bin Andalus Sahmiy da Al-As bin Wa'il…''

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 14:12:28 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi



"Maraba Da Manzon Rahama (1)" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com