Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
[ Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen ]

·Illolin zina da luwadi da madigo (1)
·Layya da hukunce-hukuncenta
·Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
·Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
·Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
·Menene Hunkunci Azumtar Watan Rajab??

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Lokaci: A Cikinsa Ake Shuka Alheri Ko Sharrin Da Za A Girba Ranar Lahira (1)
 
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga Dokta Mansur Sakkwato

Lokaci: A Cikinsa Ake Shuka Alheri Ko Sharrin Da Za A Girba Ranar Lahira (1)

Masallacin Khidmatul Wadaniyya, Khartoum Sudan

Hamdala da taslim:

Bayan haka, babu wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar Musulmi. Idan Musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne Sallar Asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar, haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta don ya gana da Ubangijinsa. A mako kuma akwai Sallar Juma'a, a shekara akwai watan azumi, akwai Sallar Idi, akwai Idin Layya, akwai aikin Hajji. Idan Musulmi yana da dukiya kuma akwai fitar da zakka duk shekara.

Allah Ya rantse da lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci ga dan Adam shi ne jarinsa, kai shi ne rayuwarsa, a cikinsa ne kake murna ko ka samu damuwa, a cikinsa kake ciwo ko ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake shuka alheri ka girbe shi a Lahira ko ka shuka sharri ka same shi yana jiran ka gobe kiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne ake samun Aljanna ko a fada cikin Jahannama, Allah Ya kiyaye mu.

Lokaci ya fi komai saurin wucewa, ba ya jira, kuma in ya tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai sanar da kowa lokacin da Ya diba masa ba. Lokacin da Allah Ya ba ka shi ne tsawon shekarun rayuwarka, idan ka kwantar da hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da bai da yawa. Wanda aka ba shi shekara 60 misali nawa ne za a cire daga cikin kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci? Nawa ne adadin kwanaki marasa amfani a cikinsu?

dan Adam yakan yi nadama a kan lokacinsa da ya wuce a wurare muhimmai guda biyu: Na farko: Idan Mala'ikan mutuwa ya damke shi, ya hakikance cewa tilas zai bar duniya a nan yake cewa: ''Ya ubangiji Ka dawo da ni, domin kila in yi aikin kwarai a cikin abin da na bari. Ina! Wata magana dai ce da shi yake fadar ta, kuma a bayansu akwai rayuwar barzahu da za su yi har zuwa ranar da za a tashe su. (Muminun: 99-100). Wuri na biyu: Shi ne idan aka yi tashin Alkiyama, kowa ya ga sakamakonsa, aka yanke wa kowa hukuncin in da zai zauna. A nan ne dan Adam ke cewa: ''Kuma da za ka ga kangararru sun sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, (suna cewa): ''Ya ubangijinmu! Mun fa gani kuma mun jiya, to, Ka mayar da mu mu yi aikin kwarai, mu fa tabbas mun gano gaskiya.'' Kuma da Mun so da Mun bai wa kowane mai rai ikon shiriya, amma maganarMu ta riga ta tabbata cewa, lallai sai Mun cika wutar Jahannama da aljanu da mutane baki daya. To, ku dandani azaba don mantawar da kuka yi da haduwarku da wannan rana, Mu ma Mun manta da ku, kuma ku dandani azaba ta dindindin saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.'' (Sajdah: 12-14).

Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Akwai ni'imomi guda biyu da ake kwarar dan Adam a kansu; lafiya da lokaci.'' Dalilai uku ne ke sa a kwari mutum game da lokaci. Kodai ya kasance bai yi cikakken amfani da lokacin ba ta hanyar yin abin da ya kamata wanda zai samu babban lada, ko ya kasa yin aikin ladan sam sam, ko kuma a cikin lokacin ya yi aikin zunubi. Mutane sun kasu kashi-kashi dangane da lokaci. Wani za ka ga mafi yawan lokacinsa yana cike da abubuwa masu amfani, wani duk lokacinsa na sharholiya ne, wani kuma bai ma san ya zai yi da lokacin ba! Matsalar wani ita ce bai tsara wa rayuwarsa komai ba, wani bai san muhimmancin lokacin ba. Wani ya sani amma bai da karfin zuciya da kwarin gwiwar maida hankali ga abin da ke amfaninsa.

Yana da kyau mu duba rayuwar magabata mu ga yadda suke cin moriyar lokaci. Abdurrahman bin Mahdi ya ba da labarin malaminsa Hammad bin Salamah ya ce, da an ce wa Hammad ga Alkiyama nan za ta tsayu bai da yadda zai kara bisa ga aikin da yake yi. Ba za mu yi mamakin wannan maganar ba in muka san cewa Malam Hammad ya rasu yana cikin Sallah. Saurari abin da wani dalibin ilimi Abu Hatim Ar-Razi (Rahimahullah) yake cewa: ''Mun nemi Malam Ka'anabi ya karantar da mu Muwadda sai ya ce, to ku zo da safe. Sai muka ce masa da mun yi Asuba wurin Malam Hajjaj muke zuwa. Ya ce, to ku zo in kun kare. Muka ce sannan muke zuwa wurin Malam Muslim bin Ibrahim. Ya ce to ku zo in kun gama. Muka ce ko da muke gamawa Azahar ta yi, sannan muke karatu ga Abu Huzaifa. Ya ce, to, ku zo bayan La'asar. Muka ce, makarantar Arim. Ya ce to ku zo bayan Magariba. To, daga nan muka rika zuwa wurinsa idan an yi Magariba sai ya fito ana sanyi ya nade kansa ya yi ta karantar da mu har illa masha Allahu.''

Ta hanyar amfani da lokaci ne kawai ake iya fito da baiwa iri-iri da Allah Ya yi wa dan Adam. Bincike ya nuna cewa akasarin mutane ba su amfani da kashi 25 cikin 100 na baiwar da Allah Ya ba su. Yaron da ya fadi jarrabawa kuma ya rufe aji yana iya zama na daya ba a makarantarsu kawai ba a fadin jiha inda aka yi kokarin fitowa da baiwar da Allah Ya ba shi. Shiriritaccen da za ka gan shi yana kashe wando a bakin titi yana iya zama babban malami ko babban mawallafi ko kwararren likita ko gogaggen dan siyasa ko fitaccen dan kasuwa. Amma an watsar da baiwar da Allah Ya ba shi, shi ya sa ya lalace. Wanda ya zo na baya a wajen tsere ko gasar karatun Alkur'ani yana iya zarce kowa in da an tona baiwar Allah da ke tattare a cikinsa. Kana iya gwada wannan ga dan takara a wajen tseren gudu idan ya kasa, ya koma baya har ya kai ga faduwa saboda gajiya. Idan likitoci suka auna shi a lokacin za su ce mana akwai sauran karfi da kuzari mai yawa a jikinsa amma yana bukatar abin da zai zakulo wannan karfin. Yaya za mu gane wannan? Mu sakar masa zaki ko maciji misali. A nan ne za ka sha mamaki. Suna yin arba da zaki za ka ga ya tashi ya ruga da gudu, irin gudun da can da farko ma bai yi shi ba. Me ya tono wannan kuzari na gudu daga jikinsa? Daga sama aka sauko masa da shi? A'a. Dama yana nan cikin jikinsa amma yana neman abin da zai motsa shi! Wannan shi zai fassara maka irin albarkar rayuwar magabata wajen jihadi da karantarwa da rubuce-rubuce da makamantansu. Sun sanya wata manufa a gabansu ita ce neman yardar Allah. Wannan manufa sai take fitar da iyakar abin da yake yiwuwa na baiwa da ke cikinsu. In ba don Manzon Allah (SAW) ba, da su Sayyidina Umar da Ibnu Mas'ud da Khalid bin Walid da sauransu duk iyakarsu su zamo makiyaya ko 'yan kasuwa ko 'yan tauri ko wani abu mai kama da wannan. Amma da aka samu jagora cikakke mai manufa sai ya fito da ikon Allah a cikinsu. Nan take kowanensu ya taka rawa mai muhimmanci a tarihin duniya. Wani daga cikin magabata ya ce, wani lokaci sai barci ya fara dauka ta, ina cikin jin dadinsa sai in tuna da wuta da Aljanna. Idan na tuna haka sai in ga na zabura kamar zaki na tafi zuwa kiyamullaili.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 14:26:33 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Lokaci: A Cikinsa Ake Shuka Alheri Ko Sharrin Da Za A Girba Ranar Lahira (1)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: