Muhawara Hausa
 



Fitinan ‘Kharamidah' Da Fitinan Hajjaj Ibn Yusuf AssaQafi
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi Daga Masallacin Sheikh Dr. Sayyid Abdulwahab 1/12/1435H

Fitinan ‘Kharamidah' Da Fitinan Hajjaj Ibn Yusuf AssaQafi

Yau Malam yayi maganane kan Fitintinu dasuka shafi dakin Allah. Kafin turo annabi(Sallallahu alaihi wasallam) da kuma bayan turoshi.

Wanda wa'innan fitintinu suna da yawa amma wanda malam yayi magana akansu sune kaman haka.

1.Fitinan ‘kharamidah'

wanda wannan wasu ‘yan ta'addan ‘yan shi'ah ne masu tsattsauran ra'ayi. Yakai ga sun kawo wa makkah hari suka Kai farmaki wa dakin Allah sannan suka ciro ‘hajr alaswad' daga wurin da yake suka tafi dashi sukaje suka gina sabuwar ka'aba ta dabam. Wanda daga karshe aka kwatota aka dawo da'ita

2.Fitinan Hajjaj ibn yusuf assaQafi.

Alokacin Daulan umawiyyah. Wanda hajjaj da rundunarsa suka kai hari da har ta shafi ka'abah. Akayi kisa da kuma kone kone.

3.Fitinan Sufaye.

Bayan da Duniyar musulunci ta fada cikin rudani da shirka wanda Jahilan sufaye suka kirkirota. Suka maida makkah wurin bautan waliyyai wanda alokacin ansami hubbare wurin 360 na waliyyai wanda ake zuwa rokonsu. Kullum acikin mauludi ake na wa'innan waliyyan. Da sauran abubuwa wanda addini ya hana.. Ana cikin haka Allah ya kawo sheikh ibn Abdulwahab yazo ya jaddada tauhidi ya kuma Kori wannan dabi'a mummuna.

4. Fitinan Bayyanar mahadin karya.

Wanda ya faru a 1979 Miladiyyah. Inda aka samu wasu matasa mazu zafin kai suka kai wa wannan wuri mai tsarki hari. Hakan yakai ga zubda jini sosai da rushe rushe. Malam ya bayyana cewa yana nan alokacin da abin ya faru kuma alokacin da da'awar ta taso malamai sunyi zama da wa'innan matasa babu iyaka. Sannan yana daga cikin wa'inda aka saka musu nauyin yiwa wa'innan matsa raddi a rubuce ta wasika kaman yanda su matasan suka rubuto wasika suna neman ayi wa mahadinsu mubaya'a. Rikicin ya somane da asubahi Bayan idar da sallah kuma Rikicin ya dade tsawon kwana 13 anayinta. Haka Masallaci mai alfarma ya zauna ba'a sallah aciki har sai da Allah ya kawo nasara a rana ta 14 aka kammala kuma aka fara aikin ibadah a wannan wuri.

Allah muke roko ya kara karemu ya kare mana addininmu.

Wassalatu wassalam ala rasulillah.

 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 14:40:55 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 4
Kurioi: 1


Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi



"Fitinan ‘Kharamidah' Da Fitinan Hajjaj Ibn Yusuf AssaQafi" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com