Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Ya Mai Neman Alheri Ramadan Ya Shigo
 
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Sheikh Abdullahi bin Muhamma Al-Basri, Masallacin Ar-Ruwaida ta Kudu, Saudiyya

Ya Mai Neman Alheri Ramadan Ya Shigo

Godiya da taslimi

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ya inganta daga gare shi (SAW) cewa: ''Idan daren farko na watan Ramadan ya kasance sai a daddaure shaidanu a kori aljannu, a kulle kofofin wuta ba za a bude ko kofa daya ba, kuma za a bude kofofin Aljanna ba za a rufe ko kofa daya daga cikinsu ba, sannan sai mai kira ya yi kira cewa: Ya mai neman alheri ka ci gaba! Ya mai neman sharri ka takaita!'' Daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya fi mutane wajen kyauta, kuma ya fi yin kyauta a cikin watan Ramadan. Jibrilu kan gana da shi a kowane dare cikin Ramadan Annabi (SAW) yana bitar karatun Alkur'ani a wurinsa. Idan Jibrilu ya gana da shi ya fi yin kyauta fiye da iskar sarfa.''

Ya ku Musulmi! Ramadan da alheri abokan tagwaici ne. Ramadan shi ne watan alheri kuma zamaninsa. Alheri kuma shi ne aikin Ramadan, masu yin alheri su ne ma'abuta Ramadan. Ramadan shi ne kasuwar ma'abuta alheri, duk wanda ya yi muwafaka da aikata alheri a cikin Ramadan kuma ransa ya ji saukin yin sa, to shi ne wanda ya dace. Wanda ya gaza aikata alheri, kuma aikin ya yi masa nauyi, ya kau da kai daga gare shi, ana zaton ba zai dace da alheri a waninsa ba, kuma ba za a shiryar da shi ga hanyarsa ba. Ba wani abu ya kawo haka ba face damar aikata alheri a Ramadan ta fi samuwa cikin sauki fiye da waninsa.

Don haka ake kiran ma'abucin alheri ya ci gaba kuma ana maraba da shi, shi kuma ma'abucin sharri ana garagadinsa ya takaita kuskurensa, ana daure shaidanu, a kuntata magudanunsu. A kulle kofofin wuta a bude kofofin Aljanna. A yi ta karatun Alkur'ani, Mala'iku su yi ta sassauka, a yi ta ibada cikin jam'i, kuma a ninnika lada. To duk wanda aka sahale masa wannan, amma ransa ba yi shaukin aikata alheri ba, bai yi hobbasa ba, to, ya nemi inda zuciyarsa ta tafi, domin ba ya da zuciya.

Hakika Ramadan ya shigo, wani yankinsa ya fara tafiya, shin waninmu ya tambayi kansa: ''Me na aikata na alheri a watan nan na alheri?'' Shin na kasance daga cikin dalibansa masu aiki da sabubansa, masu shiga ta kofofinsa? Idan haka ya samu, to, barkarsa da arziki, idan kuma akasin haka ne, to me yake jira? Yana jira a ce gobe Idi ne bai aikata wani alheri ba? Ko yana jiran watan ya fita ne kin sa da son sa ba tare da an gafarta masa ba?

Ku saurara! Allah Ya yi rahama ga mutumin da ke yi wa kansa hisabi alhali watansa ya fara, wanda ya yi dubi ga abin da ya gabatar, ya kintsa ga kwanuka masu zuwa. Idan ya kyautata ya kara, idan ba haka ba, ya juyo daga gazawarsa.

Ku biyo ni ya ku masu azumi! Mu nazarci wani abu daga abin da Manzon Allah (SAW) ya yi bayani cewa yana cikin alheri domin mu auna kanmu mu san matsayinmu. Mai Tsira da Aminci ya ce ga Mu'azu: ''Shin ba na nuna maka kofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana bice zunubi kamar yadda ruwa ke bice wuta, sai kuma sallar mutum a tsakiyar dare. Ko in ba ka labari kan al'amarin da ginshikinsa da kuma kololuwar tozonsa? Kan al'amarin shi ne Musulunci, ginshikinsa yin Sallah, kololuwar tozonsa shi ne jihadi. Ko in gaya maka abin da ya mallaki wadannan duka? Ka kame wannan, - sai ya yi nuni ga harshensa.'' Ya ce: ''Ya Annabin Allah, ashe za a kama mu da abin da muke furtawa?'' Ya ce: ''Haba ya Mu'azu! Ashe za a kifa fuskokin mutane a cikin wuta ba domin girbe-girben harsunansu ba?''

Kuma (SAW) ya ce: ''Wanda aka ba shi rabo na yin sauki ga jama'a, hakika an ba shi rabo na alheri, wanda aka haramta masa rabo na yin sauki ga jama'a, hakika an haramta masa rabo na alheri.''

Kuma an karbo daga Abdullahi bin Abu Aufa (RA) ya ce: ''Wani mutum ya zo ga Annabi (SAW) ya ce: ''Ni na gaza iya wani abu daga (karatun) Alkur'ani, ka sanar da ni abin da zai ishe ni.'' Sai ya ce: ''Ka ce: Subhanallahi wal hamdu lillahi wa la'ilaha illallahu wallahu akbar, wala haula wala kuwwata illa billah!'' Sai ya ce: ''Ya Manzon Allah! Wannan na Allah ne, to, ina nawa?'' Sai ya ce: ''Ka ce: ''Allahumma arhamni, wa afini wahdini, warzukni.'' Ya fadi haka da tara hannunwansa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Amma wannan hakika hannunsa ya cika da alheri.''

An karbo daga Abu Zarri (RA) ya ce: ''Masoyina (SAW) ya yi min wasiyya da dabi'u na alheri: Ya yi min wasiyya kan kada in dubi wanda yake sama da ni, sai dai in dubi wanda yake kasa da ni. Ya yi min wasiyya da son miskinai da kusantarsu. Ya yi min wasiyya da in sadar da zumuntata koda an juya min baya. Ya yi min wasiyya kada in ji tsoron zargin mai zargi wajen neman yardar Allah. Ya yi min wasiyya kan in fadi gaskiya komai dacinta. Ya yi min wasiyya in yawaita fadin La haula wala kuwwata illa billah, domin ita taska ce daga cikin taskokin Aljanna.''

Kuma (SAW) ya ce: ''An yi hisabi ga wani mutum daga wadanda suka gabace ku, amma ba a same shi da wani abu na alheri ba, illa yana bin wani mutum bashi, yana hulda da mutane, amma sai ya rika umartar yaransa cewa kada su matsa wa mai bashin nan. Sai Allah Madaukaki Ya ce ga Mala'ikunSa, ''Mu ne mafiya cancanatar yin haka daga gare shi, don haka ku kyale shi.''

Ya ku taron masu azumi! Ga wasu kofofin alheri nan: Sallah da azumi da tsayuwar dare da sadaka da kyautatawa da son matalauta da yin sauki ga mutane da kawar da kai ko yafe bashi ga kuntatacce da sadar da zumunta da tausayi da kame harshe daga fadin sharri a shagaltar da shi ga tilawa da zikiri da fadin gaskiya da umarni da alheri da hani daga abin ki. To daga cikinmu wane ne ya yi dacen hada wadannan halaye duka? Wane ne ya kiyaye wajen samun kabbarar harama tare da liman a kowace Sallah tun shigowar watan? Wane ne ya yi hakuri ya cije ya yi zaman dako ya tsaya ya yi tarawihi tare da liman kuma tsayuwar dare ba ta kubuce masa ba? Shin mun tsare harsunanmu daga fadin zur da yasassar magana da annamimanci da karya? Shin mun jika su da zikiri da karatun Alkur'ani? Shin mun yawaita tasbihi da hailala da takbiri da tahmidi, ko mun kiyaye azuminmu daga lagwu da batsa? Shin mun yi tawali'u muka tausaya wa wadanda muke mu'amala da su na daga 'ya'ya da makwabta da abokai da ma'aikata da 'yan kwadago? Shin mun yafe wa wadanda suka munanta mana, mun kawar da kai mun yi musu afuwa? Shin mun koma ga zumuntar da aka yanke muka sadar da ita don yin da'a ga Allah, sannan muka bar zunubi da la'ana? Ababen ki da ke cikin gidajenmu daga manyansu kamar na'urorin setlyit shin mun rufe su mun cire su?

Idan mun kasance mun yi riko da wadannan kofofi, to, barkanmu da duk wadannan tsiwurwura na alheri. Idan kuma sabanin haka ne, babu abin da ya saura sai jajen rashin babban rabo ga mai busasshiyar zuciya. Duk da haka har yanzu kofa a bude take, akwai sauran lokaci, kuma Allah Yana karbar tuba daga wanda ya tuba, kuma Yana maraba da wanda ya koma gare Shi.

Don haka mu ji tsoron Allah, mu tsara kawunanmu a hanyar alheri, mu riski jirgin ma'abuta alheri, mu kasance daga masu bude shi da koyar da shi da shiryarwa zuwa gare shi. Mu yi taimakekiniya a kan aikin alheri, kuma a samu wata al'umma daga cikinmu tana kira gare shi. Domin babu tsira face ga ma'abuta alheri. (SAW) ya ce: ''Za a fitar da mutum daga wuta muddin ya ce: ''La'ilaha illallahu kuma ya zamo a zuciyarsa akwai kwatankwacin kwayar alkama na alheri. Sannan za a fitar da mutum daga wuta muddin ya ce: La'ila illallahu, kuma a zuciyarsa akwai kwatankwacin kwayar gero na alheri. Sannan za a fitar da mutum daga wuta muddin ya ce: La'ilaha illallahu kuma a zuciyarsa akwai alheri kwatankwacin kwayar zarra na alheri.'' Kuma (SAW) ya ce: ''Daga cikin mutane akwai mutanen da suke mabudai ne na alheri makullai na sharri, kuma daga mutane akwai mutanen da suke mabudai ne na sharri makullai na alheri. To, albarka ta tabbata ga wanda Allah Ya sanya mabudin alheri a hannunsa, kuma bone ya tabbata ga wanda Allah Ya sanya mabudin sharri a hannunsa.'' Kuma (SAW) ya ce: ''Lallai Allah da Mala'ikunSa da ma'abuta sama da kasa hatta tururuwa a raminta hatta kifi (a cikin ruwa) suna addu'a ga mai koya wa mutane alheri.'' Kuma (SAW) ya ce: ''Mai shiryarwa zuwa ga alheri daidai yake da wanda ya aikata shi.'' ''Kuma wanda ya bude kofar alheri mutane suka bi, yana da ladarsa da kuma ladar wadanda suka bi shi ba tare da an rage komai daga ladarsu ba.''

Amma wanda alheri ya yi masa nauyi ko wani abu ya hana shi ko ya kange shi ga aikata shi, to, akalla ya so masu alheri, ya kame daga sharrinsa da cutarwarsa, in ya yi haka yana da lada. An karbo daga Anas bin Malik (RA) ya ce: ''Na ga sahabban Manzon Allah (SAW) suna farin ciki da wani abu da ban ga sun yi farin ciki mai tsanani a kansa kamarsa ba. Wani mutum ya ce: ''Ya Manzon Allah! Mutum ne yake son mutum a kan aikin alherin da yake yi amma shi bai iya wannan aiki.'' Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Mutum yana tare da wanda yake so.'' Kuma (SAW) ya ce: ''A kan kowane Musulmi akwai sadaka, koda bai samu ba, ya yi aiki da hannunsa ya amfani kansa ya yi sadaka. Idan ba zai iya ba, ya taimaki ma'abucin bukata mai rauni, idan ba zai iya ba, ya yi umarni da alheri, idan bai yi haka ba, ya kame daga sharri, lallai shi ma sadaka ne.''
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 15:14:21 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"Ya Mai Neman Alheri Ramadan Ya Shigo" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: