Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Daga Salihu Makera

Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi

Babi na Goma Sha Biyar: Idan mutum ya ce ga wakilinsa: ''Ka sanya (raba) shi inda Allah Ya sanar da kai. Kuma wakilin ya ce, hakika na ji abin da ka ce'':

52. An karbo daga Yahya dan Yahya ya ce: ''Na karanta wajen Malik daga Is'hak dan Abdullahi cewa: ''Lallai shi ya ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: ''Abu dalhat ya kasance ya fi mutanen Madina yawan dukiyar gonar dabinai. Kuma lallai dukiyar da ya fi so ita ce, wadda take Burha'u, kuma ta kasance tana mai fuskanta Masallaci, kuma Manzon Allah (SAW) ya kasance yana shigarta ya sha daga ruwan cikinta mai dadi. Lokacin da wannan aya ta sauka cewa: ''Ba za ku samu cikakken da'a ba, har sai kun ciyar daga abin da kuke so… (k:3:93).'' Sai Abu dalhat ya tafi zuwa ga Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Ya Manzon Allah! Hakika Allah Madaukaki yana cewa, a cikin littafinSa. ''Ba za ku samu (kaiwa ga) cikakkiyar da'a ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so….har zuwa karshe.'' Kuma lallai mafificiyar dukiyata da na fi so ita ce wadda take Burha'u, to yau, lallai na bayar da ita sadaka ga Allah ina kaunar ladarta da tanadin sakamakonta a wurin Allah. Ka sanya ta ya Manzon Allah, duk inda ka so.'' Sai (Annabi) ya ce, ''Madallah! Wannan dukiya ce wadda aka bada ta ta hanyar Allah! Lallai na ji abin da ka fadi game da ita, amma ina ganin ya kamata ka sanya ta sadaka ga makusantanka. Ya ce, ''Zan aika ta haka ya Manzon Allah, sai Abu dalhat ya raba ta cikin makusanta (danginsa) da 'ya'yan baffaninsa.'' Isma'il ya karbo shi daga Malik ya ce, ''Manzon Allah Ya ce, ''Wannan dukiyace mai ribah.''

Babi na Goma Sha Shida: Wakilta amintacce cikin taska (ma'ajiyar dukiya) da makamancin haka:

53. An karbo daga Muhammad dan Ala'u ya ce: ''Abu Usama ya ba mu labari daga Buraida dan Abdullahi daga Abu Burdata daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: ''Mai tsaron taska amintacce wanda ke ciyarwa da yawa, (Annabi) ya ce, wanda ke aika ta abin da ka umarce bisa kamala da cika. Kuma bisa dadin ransa zuwa ga wanda aka umarce shi da shi yana daga cikin dayan masu (ladan) yin sadaka.''

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.

Littafin bayanin gonaki (noma):

Babi na Farko:

Fifikon noma (shuka) da dashen itace, idan aka ci daga gare shi. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: ''Shin ba ku ganin abin da kuke shukawa (nomawa), shin ku ne kuke tsirar da shi ko kuwa Mu ne masu tsirarwa. Da Mun so sai Mu sanya shi ya zamo kekasasshe wanda ya marmashe…'' (k: 56: 63 - 65):

54. An karbo daga kutaiba dan Sa'id ya ce: ''Abu Awanata ya ba mu labari, Hawwala Sanad ya ce, ''Abdurrahman dan Mubarak ya ba mu labari ya ce, Abu Awanata ya ba mu labari daga kattada daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Babu wani mutum Musulmi wanda zai dasa wani abin dashe (itace), ko ya shuka wani abin shuka (hatsi), tsuntsu ya ci ko wani mutum ko wata dabba, face ya kasance masa sadaka a gare shi.'' Muslim ya ce, Abanu ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba mu labari ya ce, Anas ya ba mu labari daga Annabi (SAW).

Babi na Biyu: Abin da ake jin tsoro daga abin da zai biyo bayan amfani da kayan noma, ko hukuncin ketare iyakar abin da aka yi umarni da shi:

55. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: ''Abdullahi dan Salim ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Ziyad Alhani ya ba mu labari daga Abu Umamata Albahili ya ce: ''Lallai shi ya ga wasu kayan aikin gona (noma). Sai ya ce: ''Na ji Annabi (SAW) yana cewa: ''Wannan ba zai shiga gidan wasu mutane ba face Allah Ya shigar da wulakanci gare su.'' (Wannan Hadisi yana koyar da hana barin kayan aiki a gona saboda kada abokan gaba su samu wannan makami su yi wa Musulmi barna.) Abu Abdullahi (Buhari) ya ce, ''Sunan Abu Umamata shi ne, Suda dan Ajalan.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 15:16:39 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Fassarar Sheikh Is'hak Yunus Almashgool, Bauchi" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: