Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Azumi Na Gaskiya (1)
 
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi Daga Hudubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-Sabitiy Masallacin Annabi, Madina

Azumi Na Gaskiya (1)

Huduba ta Farko

Godiya da hamdala ga Allah.

Bayan haka, ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, Allah Madaukaki Ya ce: ''Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)'' (k:3:102).

Ranaku suna shudewa kamar shudewar girgije, shekaru suna wucewa da sauri, alhali muna cikin mayen rayuwa muna shagaltattu. 'Yan kadan ne suke tunani kan halin da muke ciki ko makomarmu. Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.'' (k:25:62).

Musulmi a cikin shekarunsa abin iyakancewa ne, kuma rayuwarsa gajera ce. Hakika Allah Ya sanya masa wasu ayyukan musamman na alheri, kuma Ya ba shi daga zamani da wuri masu daraja da za su kange shi daga karkacewa su daidaita rayuwarsa. Daga cikin wadannan ayyuka akwai azumin watan Ramadan Mai albarka. Allah Madaukaki Ya ce: ''Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa.'' (k:2:183).

A cikin watan Ramadan takun sha'awoyi kan ragu a cikin zukatan da suke da imani. Ayyukan kankan da kai su daukaka a cikin yini da dare. Wani yana rokon afuwa kan gazawarsa, wani yana rokon dacewa a cikin ayyukan da'arsa, wani kuma yana isti'aza daga ukuba, wani yana fatar kyakkyawar lada, wani kuma zikiri ya shagaltar da shi. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya datar da su, yayin da aka haramta hakan ga wasunsu.

Watan Ramadan wata ne na karfi da kyauta, wata ne na raya dare da imani, wata ne na aiki da hakuri, ba wata ne na rauni da kasala da barci ba. Kasalar wasu masu azumi da komawarsu ga barci a wuninsa da karanta ayyukan da'a sun saba wa hikimar yin azumi, ba su dace da manufarsa ba.

Musulmin farko sun kasance suna rayuwa ne a cikin Ramadan da zukatansu da hankalinsu, idan dayansu na azumi, hakika yana kiyaye wuninsa yana mai hakuri kan wahalhalu, yana kiyaye dokokin Allah da jin tsoronSa. Mai nesa da duk abin da zai bata wuninsa ya bata azuminsa. Ba ya furta mummunar magana, kuma ba ya fadin komai sai alheri, ko ya yi shiru. Kuma darensa ya kasance yana kashe shi ne cikin Sallah da tilawar Alkur'ani da zikiri domin koyi da Manzon Allah (SAW).

Ribar azumi da sakamako da falalarsa ba su da iyaka, kidaya ba ta kididdige su, sai dai ba a sanya masu kasala a ciki, masu wasa da suke bata watan wajen barci, ko shafe dare a rumfunan kasuwanci da kashe dare ana wasa da shagala.

Azumi garkuwa ne daga wuta kamar yadda Ahmad ya ruwaito daga Jabir (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya ce: ''Abin sani azumi garkuwa ne daga wuta.'' Azumi garkuwa ne daga sha'awoyi, domin hakika ya zo a cikin Hadisin Ibnu Mas'ud (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya ce: ''Ya ku taron samari! Wanda yake da ikon yin aure daga cikinku, to ya yi aure, domin shi ne mafi sanya runtse idanu, kuma mafi tsaron farji (daga zina); wanda ba ya da ikon yin auren kuwa, to ya yi azumi, ''saboda shi dandaka ne.'' Buhari da Muslim suka ruwaito.

Azumi hanya ce ta zuwa Aljanna, Nisa'i ya ruwaito daga Abu Amama ya ce: ''Na zo ga Manzon Allah (SAW) na ce: ''Ka umarce ni da wani al'amari da zan rike daga gare ka.'' Sai ya ce: ''Na hore ka da yin azumi, domin babu kamarsa.''

An karbo daga Sahlu bin Sa'ad (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya ce: ''Lallai a cikin Aljanna akwai wata kofa ana ce da ita: Rayyan. Masu azumi ne za su shiga ta ita a Ranar kiyama, babu mai shiga ta cikinta bayan su. Za a rika cewa ina masu azumi? Sai su tashi, babu mai shiga ta cikinta sai su. Idan suka shiga sai a kulle, babu mai shiga a bayansu.'' Buhari da Muslim suka ruwaito.

Imam Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi bin Amru bin Al-As (RA) cewa: ''Lallai Annabi (SAW) ya ce: ''Azumi da Alkur'ani suna ceton bawa a Ranar kiyama. Azumi zai ce: ''Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha'awoyi da rana, Ka ba ni cetonsa. Alkur'ani kuma ya ce: ''Na hana shi barci cikin dare, Ka ba ni cetonsa. Ya ce: ''Sai su (biyun) su cece su.''

Azumi kaffara ce da gafara ga zunubai, domin kyawawan ayyuka suna kankare munana. Hakika (SAW) ya ce a Hadisin Abu Huraira (RA): ''Wanda ya yi azumi yana mai imani da neman lada, (ikhlasi) an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.''

Azumi sababi ne na samun sa'ada a duniya da Lahira. Manzon Allah (SAW) ya fadi a Hadisin Abu Huraira cewa: ''Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi soyuwa a wurin Allah daga kanshin turaren almiski. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buda-baki da kuma in ya hadu da Ubangijinsa, zai yi farin ciki da azuminsa.'' Buhari da Muslim suka ruwaito.

Shin za mu sanya wa Ramadan wani lokaci ya zama na komawa ga Allah da hisabi ga kai da kyautata inda muka gaza a bangaren Allah? Shin ko daliban ilimi da masu da'awa za su sanya Ramadan ya zama wani lokaci na jaddada himma da tsarkake niyya? Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ce da kowane Musulmi zai taimaki dan uwansa azzalumi ko wanda aka zalunta, ya taimaki wanda ake zalunta ta hanyar kwato masa abin da aka zalunce shi, ya taimaki azzalumi ta hana shi yin zaluncin, har sai mutanen kirki su shugabanci al'ummar Musulmi? Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ga mawadata su warware bukatun fakirai, su yi shukura kan ni'imar da aka yi musu ta hanyar ajiye ta a inda Wanda Ya ba su ni'imar Ya ce, ta yadda za su iya ceto mayunwata daga cikin al'ummar Musulmi, wadanda imaninsu yana iya fadawa ga hadari, idan suka gaza ciyar da mayunwatan cikinsu ko tufatar da marasa tufafinsu ko shayar da masu jin kishinsu? Ko kuwa Ramadan zai kasance wani lokaci da kowane Musulmi zai fahimci kasala da rashin kazar-kazar na iya jefa shi ga aikata kaba'ira, ta yadda zai ciru daga giba da annamimanci da mugun zato da wulakanci da raina dan uwansa Musulmi?

Ya ku bayin Allah! Ramadan babbar makaranta ce da muke samun horo a darensa da wuninsa, gabobinmu su karfafa da shiftarsa har sai sun yi kamar yadda Ubangiji Mahaliccinsu Ya yi nufi. Ya zo a cikin Hadisin kudusi cewa: ''BawaNa ba zai gushe yana kusantaTa da nafilfili ba, har sai Na so shi. Idan kuma Na so shi, sai in kasance jinsa da yake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damka da shi da kafarsa da yake tafiya da ita.'' Buhari ya ruwaito.

Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan karfi da gaskiyar niyya. Wadannan su ne ke karya turakun son zuciya, su mayar da igiyoyin sharri. Duk wani karfi ko tsari zai yi wuya ga mumini daga mafitar rana zuwa mafadarta yana ci abinci ko abin sha na wani lokaci. Za a ga yana rike da akalar rayuwarsa yana hana ta fadawa ga sha'awoyi ko abubuwan son zuciya. Kai yana iya ce da zuciyarsa na ki. Me ya fi dadi a ce ta kasance cikin neman yardar Allah. Ba ta jima'i da rana ba ta fasikanci. Kuma da jahili zai bata mata ya nemi tayar da hankalinta, zai ya yi linzami ga fisgar sharri da fadi da cewa: ''Ni mai azumi ne!''

Azumi na gaskiya yana tsarkake zuciya daga miyagun kullace-kullace da zunubai da sharruka. Yana kange harsuna daga furta maganganun banza da hana ido ganin haram.

Amma daga cikin masu azumi akwai mai azumin da ba ya da komai sai yunwa da kishin ruwa. Domin mutumin da ke barin abinci, amma ya ci naman 'yan uwansa da giba, yana kamewa daga abin sha, amma bai kamewa daga karya da algushu da zaluntar mutane, yunwa da kishin banza yake sha.

Azumi na gaskiya yana sa Musulmi ya zama mai faffadar zuciya, mai tattausan harshe, ya zamo mafi gudu daga husuma da sharri, idan aka yi masa laifi ko aka munanta masa ya yi hakuri. ''Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.'' (k:39:10).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 15:20:10 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"Azumi Na Gaskiya (1)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: