Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
[ Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar ]

·Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
·Asalin Hausa (3)
·Asalin Hausa (2)
·Asalin Hausa (1)
·Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresriti
·08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????
·002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
·001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
·GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Bayan Azumi Sai Kuma Me? (2)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Daga Hudubar Hasan bin Abdul'aziz Alu Sheikh - Masallacin Annabi, Madina

Bayan Azumi Sai Kuma Me? (2)

Ya al'ummar Musulmi! Wani yanayi na ayyuka masu girma yana wucewa ga al'umma a daidai lokacin da matsaloli masu yawa suke shake da wuyanta, tana fama da manyan cututtuka, tana fama da bala'o'i da wahalhalu da annoba iri-iri da cutarwa. Tana fama da rarrabuwar kai da rauni da tarwatsewa da wulakanci da al'amura masu tsanani, tana cikin hali mai sanya kuka. Shin lokaci bai yi ba da za mu duba wannan hali mai radadi da tafiya ta kuskure? Shin lokaci bai zo ba, da za mu yi tsinkaya kan abubuwan da suke kawo mana rauni, mu nemo abubuwan da za su magance mana cututtuka da matsalolinmu?

Allah Madaukaki Yana cewa: ''Shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani zukatansu su yi tawali'u ga ambaton Allah da abin da Ya saukar daga gaskiya?'' (k:57:16).

Babu abin da ya fi dacewa da al'umma a yau, bayan kammala azumin Ramadan mai girma irin ta yi fatali da munanan ayyukanta, ta magance raunukanta masu yawa da suke wurare da yawa a jikinta, wanda yake cike da gyambo yake fama da zogi. Kuma babu hanyar samun nasara da magani na hakika, sai ta komawa ga koyarwar addininta da riko ga cikakkiyar manhajar Littafin Ubangijinta da Sunnar Annabinta Muhammad (Sallahu Alaihi Wassalam). Yana daga cikin koyarwar wannan manhaja, kyautata aiki tare da gaskata Allah cewa zai taimaki addininSa a kowane wuri da kowane lokaci. Sai al'ummar ta tsayu wajen bayar da wajibai musamman kula da raunana da hana zalunci da cutar da bayin Allah masu rauni. ''Muminai maza da muminai mata, sashinsu masoya ne ga sashi.'' (k:9:71).

'Yan uwa a Musulunci! Lallai wajibin da ke kan 'ya'yan wannan al'umma ta Musulmi shi ne fadaka sosai da lura ta hakika game da irin hadarin makiya da yadda suke kulle-kullen wargazawa da bata akidar Musulmi da zame musu kafafu da barazana ga martabarsu. Akwai miyagun abubuwan da suke yi da suka buya daga gare mu, sannan suna ta kulle-kulle iri-iri da Allah ne kawai Ya san su.

Yahudawan duniya a yau suna ta jan duniya zuwa ga halaka da masifu, suna neman jefa al'ummar Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wassalam) a cikin rafkana da fitunu da cutarwa da wulakanci. Don haka ku farka, farkawa ta hakika, ya ku al'ummar Musulmi! Ku yi kwadayi da biyayya ga wannan addini iyakar kwadayi.

Ya 'yan uwa a cikin addini! Daga cikin miyagun tanade-tanaden makiya ga Musulmi, akwai watsuwar kafafen sadarwa da na watsa labarai masu dauke da miyagun koyarwa da ake kokarin watsawa a wannan kasa da sakon Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam) ya bubbugo, wato kasar da take da hurumomi biyu mafiya daraja, kasar da ta yi wa dan Adam abubuwa masu yawa. Ta sadaukar da abubuwa masu yawa domin tabbatar da zaman lafiya da amana da kwanciyar hankali da yada ayyukan alheri da kuma sauran kasashen Musulmi. Don haka wajibi ne a kan Musulmi su fahimci wadannan abubuwa ana yin su ne don a yi wa al'ummar nan kisan mummuke, a rusa kyawawan halayenta. Allah Ya yi gaskiya da Ya ce: ''Suna gurin ku kafirta kamar yadda suka kafirta domin ku yi canjaras (ku zama daya da su).'' (k:4:89).

Don haka wajibi ne a kan al'ummar Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wasallam) ta fahimci manufofin addininta da dalilan maganganun Mahaliccinta. Ta fahimci ginshinki da koyarwar Musulunci, idan ba haka ba - Allah Ya kiyaye - za ta wayi gari tababbiya wadda ta yi nesa daga shiryar Ubangijinta. Allah Madaukaki Yana cewa: ''Kuma ka ce: ''Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku da ManzonSa da Muminai.'' (k:9:105).

Allah Ya yi mana albarka a cikin Alkur'ani, Ya amfanar da mu da abin da ke cikinsa na ayoyi bayyanannu. Ina fadin wannan magana tawa, ina neman gafarar Allah gare mu da sauran Musulmi daga dukkan zunubi. Ku nemi gafararSa, ku tuba zuwa gare Shi, lallai ne Shi Mai yawan gafara ne Mai jinkai.

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah a bisa kyautatawarSa, muna yi maSa shukura a bisa datarwarSa da ni'imominSa. Na shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, girmamawa ga sha'aninSa. Kuma na shaida Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa da 'yan uwansa.

Bayan haka, mafi alherin zance shi ne maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammad Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam). Kuma mafiya sharrin al'amura fararrunsu, kuma kowane fararren al'amari bidi'a ne, kuma kowace bidi'a bata ce, kuma kowace bata tana cikin wuta.

Ya ku Musulmi! Mai rabo shi ne wanda ya tafiyar da lokacinsa a hanyar gyarar Lahirarsa, kuma rayuwar duniya ba ta rudar da shi daga bayar da hakkokin Mahaliccinsa ba. Kuma kwadayin abubuwan duniya makusanciya bai shagaltar da shi daga hakkokin Lahira mai wanzuwa ba.

Ya kai wanda ya dandani zakin da'a! Ka guji auka wa sabo, ka zamo mai da'a da takawa a wanin watan Ramadan kamar yadda ka zama a cikin Ramadan.

Sannan ka sani - ya kai Musulmi! - lallai wanda ya yi azumin Ramadan, sannan ya bi bayansa da shida a cikin watan Shawwal, kamar ya yi azumin shekara ne. Hakan ya inganta daga Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam). A duba Sahihul Muslim, Littafin Azumi, Babin Mustahabancin Azumtar Kwana Shida a Shawwal mai bi wa Ramadan, Hadisi na 1164, Hadisin Abu Ayyub (Radiyallahu Anhu). Don haka an so azumtar shida a watan Shawwal, amma wanda ake bin sa bashin azumin Ramadan, to, gaggauta biyan Ramadan ne ya fi masa, domin wajibi ne mafi dacewa daga mustahabbi.

Ku sani lallai Allah Ya umurce ku da yin salati da taslimi a kan Annabi mai girma. Ya Ubangiji! Ka yi salati da taslimi da albarka da ni'ima a bisa bawanKa kuma ManzonKa Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, April 26 @ 15:27:00 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Bayan Azumi Sai Kuma Me? (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: