Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar
[ Yankamancin, Mara Labari Da Miskilar ]

·Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
·Asalin Hausa (3)
·Asalin Hausa (2)
·Asalin Hausa (1)
·Yadda Musulmi Zaiyi Ta'amuli A Bukin Kiresriti
·08 SHIN KASANCEWA SAYYIDUNA MU'AWUYA DAN ALJANNA NE ????
·002 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 2
·001 LADUBBAN TAREWA Rubutu na 1
·GASKIYA KENAN! YAU 'YAN IZALA NE AKE RIGIMA DASU WAJE KARE MARTABAR MANZON

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Hakuri Da Matsayinsa A Musulunci (2)
 
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifi, Masallacin Annabi, Madina

Hakuri Da Matsayinsa A Musulunci (2)

Sannan Ya yi umarni bisa abubuwan da suka shafi umarni da alheri da hana abin ki, saboda abin da ke cikin hakan na wahalhalu, kuma saboda mutane suna ganin mai umarni da alheri da hana abin ki, yana shiga tsakaninsu da son zukatansu da ababen amfaninisu, alhali amfani da maslaha suna cikin bin abin da shari'a ta tabbatar ne kuma ta yi umarni da shi, barna kuma tana cikin bin abin da shari'a ta yi hani a kansa ne. Allah Madaukaki Ya ce: ''Ya karamin dana! Ka tsaida Sallah, kuma ka yi umarni da abin da aka sani (alheri), kuma ka yi hani ga abin da ba a sani ba (abin ki), kuma ka yi hakuri a kan abin da ya same ka, lallai wancan yana daga muhimman al'amura.'' (k: 31:17). Kuma an umarci wanda aka ba shi shugabancin wani abu na al'amarin Musulmi kadan ne, ko mai yawa, da ya yi hakuri, domin hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Hakika an cutar da Annabi Musa fiye da haka, kuma sai ya yi hakuri.''

Kuma Allah Ya umarci Musulmi da ya nemi taimakon Allah wajen dabi'atuwa da hakuri da riko da da'a, sai Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma ku nemi taimako da yin hakuri da Sallah'' (k: 2: 45). Kuma an umurce Musulmi ya sabar wa kansa dabi'ar hakuri a kowane hali da al'amari na al'amuran duniya da duk wani sha'ani, domin wannan ada tana taimako wajen hali nagari, ya zo cikin Sahihaini cewa: ''Duk wanda ya nemi ya yi hakuri, Allah zai ba shi damar yin hakurin, wanda kuma ya koyi dabi'ar wadatuwa daga mutane, sai Allah Ya wadatar da shi''.

Allah Ya yi alkawarin lada mai girma ko tsira daga ukuba ga masu hakuri, sai Madaukaki Ya ce: ''Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu ba tare da wani lissafi ba.'' ( k: 39: 10). Sannan Madaukaki Ya ce kan ladan masu hakuri. ''Wadancan suna da akibar gida mai kyau. Gidajen Aljannar zama suna shigarsu, su da wadanda suka kyautatu daga iyayensu da matansu da zuriyarsu, kuma Mala'iku suna zuwa gunsu ta kowace kofa. (Suna ce musu) ''Amincin'' (Allah) Ya tabbata a kanku saboda abin da kuka yi wa hakuri.Saboda haka madalla da ni'imar akibar gida.'' (k: 13: 22-24).

Allah Ya albarkace mu cikin Alkur'ani Mai girma, Ya amfanar da mu daga ayoyinSa da Ambato Mai hikima. Ya amfanar da mu shiriyar Shugaban Manzanni da maganarsa madaidaiciya. Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah Mai girma a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa lallai ne Shi Mai yawan gafara ne Ma jin kai.

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki a ranar sakamako. Ina godiya ga Ubangiji ina yi maSa shukura. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, Mamallaki, kuma Gaskiya Mabayyani. Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki daya.

Baya haka, ku ji tsoron Allah, kuma ku yi masa da'a, domin yi masa da'a shi ne mafi tsayuwa da karfin ayyukan ibada, kuma tsoron Allah guzuri ne gare ku a duniya da lahira.

Ya bayin Allah! Lallai hakuri abu ne mai daci a lokacin da ake yin sa, amma abu ne mai zaki a karshen al'amari. Allah Madaukaki Ya ce, ''Kuma idan kuka yi hakuri, lallai shi ne mafi alheri ga masu hakuri. Kuma ka yi hakuri, kuma hakurinka ba zai zama ba face domin Allah, kuma kada ka yi bakin ciki saboda su, kuma kada ka kasance a cikin kuncin rai daga abin da suke yi na makirci.'' (k:17: 126-127). Kuma Allah Madaukaki Ya kara da cewa: ''Kuma wadanda suka yi imani, kuma suka aikita ayyukan kwarai, lallai za Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidajen bene, koramu suna gudana daga karkashinsu, suna madawwama a cikinsu. To madalla da sakamakon masu aikin kwarai. Wadanda suka yi hakuri kuma suna dogara ga Ubangijinsu kawai.'' (k: 29: 58-59).

Me ya kai girman dacewar mai hakuri bisa da'a ga Allah kuma ya kauce wa haramce-haramce, ya nemi lada a wurin Allah kan musibobin da aka kaddaro masa, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Hakika ba wani abu ne hakuri ba, face wanda aka yi a tashin farko, (ma'ana a farkon aukuwar musiba)''.

Ya kai Musulmi! Ka yi aiki domin gidan tabbata da ni'ima madawwamiya, kada rayuwa mai gushewa ta rude ka, lokaci kadan ya rage ka yi gaba ka bar ta a bayanka, kuma dukiyarka da 'ya'yanka da abokin da ka fi ji da shi ba za su iya amfana maka komai ba! Ibn Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: ''Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Ka kasance a duniya kamar bako, ko mai tsallaka hanya.'' Shi kuma Ibn Umar ya kara da cewa: ''Idan ka wayi gari, to kada ka jirayi yammaci, idan kuma ka yi yammaci, to kada ka jirayi asubanci, ka ribaci lafiyarka kafin rashin lafiyarka, ka ribaci rayuwarka kafin mutuwarka.''

Duk wanda ya san Ubangijinsa kuma ya san abin da ya tanada ga masoyanSa da abin da ya yi tattali ga makiyanSa, ya kuma san matsayinsa game da rayuwar duniya, to sai ya ji dadin yin hakuri wajen neman yardar Allah, ya rika ganin duk aikin da yake na da'a bai isa ba, ya rika tsoron kada Allah Ya leka irin ayyukan da yake yi, kuma ba makawa ya guji abubuwan da aka haramta.

Ya bayin Allah! ''Lallai Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.'' (k:33: 56). Ku yi salati ku yi taslimi a kan shugaban mutanen farko da na karshe, kuma shugaban Manzanni. Ya Ubangiji Ka yi salati ga Shugabanmu Muhammadu da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim. Lallai Kai abin godewa ne Mai girma. Ya Ubangiji Ka yi albarka ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim. Lallai Kai abin godewa ne Mai girma, da aminci aminci mai yawa.

Ya Ubangiji Ka yarda da sahabban Manzonka baki daya, Ka yarda da Halifofin Annabi (SAW), Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da sauran sahabbai baki daya da wadanda suka biyo su da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Ya Ubangiji mu ma Ka yarda da mu don kyautarKa da karimcinKa da rahamarKa, ya Mafi rahamar masu rahama.

Ya Ubangiji Ka daukaka Musuluci da Musuimi, Ka kaskantar da kafirci da kafirai, Ka darkake makiyanka, makiya addini ya Ubangijin talikai! Ka daidaita tsakanin zukatan Musulmi, Ka gyara tsakaninsu, Ka shiryar da su tafarkin zaman lafiya, Ka fitar da su daga duffan zalunci da kafirci da wahalhalu zuwa ga hasken adalci da imani da sauki. Ya Ubangiji! Ka taimake su a kan makiyanKa, makiyansu ya Ubangijin talikai. Ya Ubangiji! Ka taimaki addininKa da LittafinKa da Sunnar ManzonKa, ya Mai ikon yi! Ya Mai cikakken karfi!
 
 
 Posted By Aka Sanya A Saturday, May 21 @ 20:55:40 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Hakuri Da Matsayinsa A Musulunci (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: