Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Shiri Domin Gamuwa Da Allah (6)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Daga Salihu Makera

Shiri Domin Gamuwa Da Allah (6)

Kamar yadda muka yi bincike makon da ya shige; muka ce idan Allah Ya yarda yau za mu ci gaba da koyarwar da muka soma. Muna magana ne a kan Shari'a wadda za a yi wa masu bin Yesu Kiristi, mu koma inda muka yi karatu makon jiya daga cikin Littafin 1Korithiyawa 3 : 7 - 15 wanda yake cewa ''Domin wannan fa shi wanda ya dasa ba wani abu ba ne, ko shi wanda ya yi ban ruwa kuma, sai Allah Wanda ke ba da amfani. Yanzu fa da mai dasawa da mai ban ruwa daya ne: amma kowane za ya samu nasa lada gwargwadon wahala tasa. Gama mu abokan aiki na Allah ne, ku kuwa gonar Allah ne, ginin Allah ne. Ni kuwa bisa ga alherin Allah da aka ba ni, kamar magini mai gwaninta, na kafa gindi; wani kuwa yana tada gini a kai, Amma sai kowane mutum ya yi hankali irin gini da yake yi a kai. Gama ba wanda yana da iko ya kafa wani gindi daban da wanda an rigaya an kafa ba, Yesu Kiristi ke nan. Amma idan kowane ya yi gini bisa gindin nan, ko zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ingirci, ko tattaka; aikin kowane mutum za ya bayyana: gama ranar nan za ta tone shi, da yake cikin wuta za a gwada ta, wuta kuwa da kanta za ta gwada aikin kowane mutum, na kowane iri ne. Idan aikin kowa da ya gina a kai ya tsaya, za ya karbi lada. Idan aikin kowa ya kone, za ya sha asara, amma shi da kansa za ya tsira; amma sai ka ce ta wurin tsakiyar wuta.''

Ina so mu gane wani abu sosai domin shi ne zai zama tushen gane wannan koyarwa, a cikin makonnin da suka gabata, mun yi magana a kan fyaucewa da za a yi wa masu bin Yesu Kiristi daga cikin wannan duniya, maganar Allah kuma ta koya mana cewa sai wadanda suke a shirye ne za su samu a fyauce su, duk wanda ba ya da dangantaka tsakaninsa da Yesu Kiristi, kada ma ya yi tsammanin zai tafi tare da shi a lokacin, wannan ba zancen zuwa coci ko masujada ba ne, ba kuwa zancen wai kana kiran kanka Kirista ban ne, ko kuwa kana ji kamar domin an haife ka a cikin gidan masu bin Yesu Kiristi ba, ba kawai domin an yi maka baptisma ba ne, domin akwai mutane da yawa a yau a cikin ekklisiyoyi ko kwa coci-coci wadanda kowane Lahadi suna zuwa sujada amma gaskiyar ita ce, ba su da dangantaka tsakaninsu da Yesu Kiristi Ubangijinmu.

Su dai sun tashi ne suna ganin iyayensu suna zuwa coci (Majami'a); haka suka girma suna gani, zuwa coci kawai ba ya mai da mutum ya zama Kirista, abin da zai kawo mutum cikin wannan zumunci ko kuwa dangantaka da Yesu Kiristi, shi ne ban-gaskiya cikin shirin ceton da Allah Ya kawo ga dukan duniya, wanda ta cika yanzu ta wurin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya, ya mutu bisa gicciye, aka bizine shi, bayan kwana uku ya tashi daga matattu, domin ya wanke mu daga zunubanmu, wannan ita ce hanya kadai da za ta kawo mu cikin wannan dangantaka, muddin ba ka furta wannan shaidar ban-gaskiya da bakinka ba, ba ka da rabo cikin masu bin Yesu Kiristi ko da kana kiran kanka mai bin Yesu. Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Matta 7: 21 - 23, cewa; ''Ba dukan mai ce mini, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga mulkin sama ba, sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama, a cikin wannan rana mutane da yawa za su ce mini, ubangiji, ubangiji, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, da sunanka kuma muka fitar da aljanu da sunanka kuma muka yi ayyuka masu iko? Sa'annan zan furta musu ban taba saninku ba dadai, rabu da ni, ku masu aikata mugunta.'' Mu gane cewa kawai domin ka iske kanka cikin masu zuwa Majami'a domin sujada bai isa ya sa ka shiga cikin mulkin Allah ba; amma kamar yadda maganar Allah ta ce a inda muka karanta a aya ta 21; Ba dukan mai ce mini Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba, sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama. Akwai bambanci tsakanin kiran sunan Ubangiji Allah; da kuma yi masa biyayya. Kowa ma zai iya cewa Ubangiji Allah, amma ba kowa ba ne zai yi maSa biyayya

Aikata Nufin Ubana Wanda Ke cikin sama: Wannan shi ne abin da Allah zai shar'anta yayin da muka sadu da shi cikin sama. Sai mu lura da wannan, bayan an fyauce masu bin Yesu Kiristi daga duniya, Lokacin wahala da tsanani zai soma na shekara bakwai, wadanda an raba su kashi biyu, wato shekara uku da rabi, sashi na farko, lokaci ne mai wahala kwarai ga dukan mazaunan wannan duniya, akwai kuma sauran shekara uku da rabi mai tsananin wahala a kan dukan mutanen da ke cikin wannan duniya. Mu tuna fa da cewa an rigaya an fyauce masu bin Yesu Kiristi, a lokacin irin kungiyar da ake ce da ita Majalisar dinkin Duniya za ta tashi domin ta yi kokarin magance abin da ya shafi al'ummar duniya da ta sa mutane da yawa sun bace kawai ba tare da wani cikakken bayani ba. Majalisar dinkin Duniya za ta yi kokari ta kwantar da hankulan mutane; amma na dan lokaci ne kawai. A daidai lokacin nan ne kuma masu bin Yesu Kiristi wadanda aka rigaya an fyauce za su fuskanci shari'a a gaban dakalin shari'a na Yesu Kiristi. Wannan shari'a ba domin ceto ba ne, a'a dukan wanda aka fyauce to, ya tsira, amma akwai zancen lada da wannan mutum zai karba gwargwadon aikin da ya yi a wannan duniya. Bisa ga yadda mutum ya yi wannan ne za a ba shi ladansa.

A cikin Littafin 1Korinthiyawa 4 : 1 - 5, maganar Allah tana cewa, ''Mu fa sai a yi lissafinmu haka nan, Ma'aikatan Kiristi ne, wakilai na asirin Allah kuma, daga nan kuwa abin da ake nema ga wakilai, a iske su da aminci. Amma ni, ba wani abu ba ne a gare ni in samu kwankwanto a hannunku, ko a hannun mutum: har ba ni kan yi wa kaina kwankwanto ba. Gama ban san wani aibi a kaina ba, koda haka wannan ba ya sa na barata ba: amma mai yi mini kwankwanto Ubangiji ne. Domin wannan kada a shar'anta komai da garaje, kafin Ubangiji wanda za Ya tone boyayyun al'amura na duhu, Ya bubbude shawarwarin zukata a sarari; sa'adda kowane mutum za ya samu nasa yabo daga wurin Allah.''

Zan so in ci gaba da bayani daga wannan wuri mako mai zuwa idan Mai duka ya bar mu cikin masu rai. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin. Idan Za Ku Fadi Magana Ku Yi Adalci

Daga hudubar Imam Salah bin Muhammad Al-Budair - Masallacin Annabi, Madina

Idan Za Ku Fadi Magana Ku Yi Adalci

Godiya ta tabbata ga Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku ji tsoron Allah, hakika wanda ya ji tsoron Allah ya tsira, wanda kuma ya bi son zuciya ya bata. ''Ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi).'' (k:3:102).

Ya ku Musulmi! Ku sani ana fassara maganar mutum bisa jahilci kuma a kafa masa hujja a kai. Kuma harshe yana da kaifi biyu kodai jahilci ya fi munanta shi, ko hankali ya rinjayar da shi. Kuma laifin magana barin yin adalci yayin furuci.

Wani mawaki ya ce: ''Yin shiru ya fi yin furuci da zunubi. Ka kasance mai shiru ka kubuta, idan kuma za ka yi magana, to, ka yi adalci.''

Kuma Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma idan kun fadi magana, to, ku yi adalci, kuma koda ya kasance (a kan) ma'abucin zumunta ne.'' (k:6:152). Kuma Ya sake cewa: ''Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wadansu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci. Shi ne mafi kusa ga takawa. Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa.'' (k:5:8).

Ka yi adalci koda an fusata ka, ka yi adalci koda ka yi fushi. Kada ka kasance wanda idan ba ya nan za a aibanta shi, idan kuma yana nan za a ci namansa a yawaita zaginsa a tsananta sukarsa.

Mutum mai girma abin kiyayewa, shi ne wanda ya kyautata harshensa ya lizimci hanyar gaskiya a furuncinsa, bai saba da karya a maganarsa ba. Kuma kiyayya da gaba da wadansu ba su dauke shi ga yin karya da kirkirar karya gare su ba. Fushi bai ingiza shi ya kirkiri karya ko ya yi ta'addanci ga wani.

Ya ku Musulmi! Sakin baki wajen cutar da wadansu da magana jahilci ne, sannan kirkirar karya zuma ce ta wawaye. Jin dadin yin karya dabi'ar fasikai ce, munantawa wajen tuhuma illa ce, kuma jifar mutane da kirkirarrun maganganu hanyar ma'abuta fajirci ce. Duk wanda ke da dabi'a abar zargi, mugun hali ya zame masa jiki, sai ya rika wuce gona da iri wajen cin mutuncin mutane. Ya rika halatta karya da shaidar zur don bata abokan aiki ko sana'arsa. Ya rika kaskantar da abokai da wadanda suka saba ga fahimta ko ra'ayinsa. Ya yi ta yin bakin fenti ga masu adawa da ra'ayi da fahimtarsa ta hanyar kirkira musu munanan abubuwa da jingina musu kazaman laifuffuka.

Ya ku Musulmi! Wanda ha'incinsa ya yi girma, makircinsa ya bayyana, sai ya rika yawaita yabo ga makusantansa da masu sam masa wani abu, ya yi sutura ga mai kin gaskiya, idan kyautar ta yanke ya yanke masa, sai yabon da yake yi masa ya koma cin zarafi, suturar da ya yi masa ta koma tsaraici, yabo ya koma zagi, addu'a ta koma la'ana. ''Idan aka ba su daga cikinta (dukiya), su yarda, kuma idan ba a ba su ba daga cikinta, sai su zamo suna masu fushi.'' (k:9:58).

Ya ku Musulmi! Hasada da bakin ciki suna yawaita a tsakanin mutanen da aiki ko sana'a ko zama ya hada su. Sai su yi ta gaba da hassada, sashinsu ya rika bata mutuncin daya sashin ta hanyar suka da zagi da batanci da wulakanci da kaskantarwa, musamman idan aka samu sabani komai kankantarsa. Babu mai kubuta daga haka sai wanda takawa ta yi masa katanga, kuma hankali ya tsare shi.

Za ka ga mutane na nade maganganun abokan zama sashinsu ga sashi ba za su ruwaito su ba, su binne su ba za a watsa su ba, saboda sun auku ne a lokacin fushi da hassada. Sai mutum ya dauki adawa da 'yar kure da tsarkake kai da kulli su zamo dabi'unsa. Sai wuce iyaka da karin gishiri da karya da kirkirar karya da kaidi su shigo cikin al'amuransu.

Ibnu Abdulbar (Rahumahullah) ya ce, ''Wallahi hakika mutane sun ketare iyaka wajen yin giba da zargi. Ba su tsaya kan zargin wani bangare kadai ba, sun hada da kowa, ba su tsaya ga zargin jahilai ba, sun hada da malamai. Wannan kuwa duk silarsa jahilci ne da hassada.''

Imam Az-Zahbi (Rahimahullah) ya ce, ''Maganganun batanci daga tsararrakin juna ba a kula shi, musamman idan ya bayyana maka an yi ne don adawa ko don mazhaba ko don hassada, kuma ba a kubuta daga hakan sai wanda Allah Ya tsare shi.'' Kuma ya sake cewa: ''Galibi ba a kula da maganganun tsararraki, musamman idan akwai munakasha a tsakaninsu.''

Don haka kashedinku daga bin muguwar hanya da ke zame duga-dugai ta gadar da nadama. Kashedinku - ya bayin Allah - daga shagala da watsa aibobi da bayyanar da laifuffukan wadansu da bin al'aurorinsu da gazawarsu da yi wa mutane karya da suka ko bata su, da bata sunansu domin wadansu dalilai na son zuciya mai umarni da mugun aiki.

Ku ciru daga munanta zato, ku nemi uzurori ga mutane, ku yafe laifuffuka da gazawarsu, kada ku bari Shaidan ya batar da ku, domin lallai shi makiyi ne mai batarwa mabayyani.

Ina fadin abin da kuke ji ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure, ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai gafartawa ne ga wadanda suka tuba suka koma gare shi.

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Makagin halitta, Masanin abubuwan da suke boye. Ina gode maSa cikakkiyar godiya marar iyaka. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma Shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, zababbenSa, mai ganawa da Shi, kuma abin yardarSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa mamaya a addini, mamaya a yakini. Tsira da amincin Allah matabbata har zuwa Ranar Sakamako su tabbata a gare su.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah da takawa domin yi maSa takawa shi mafi falalar abin nema, kuma yi maSa da'a ita ce mafi daukakar nasaba. ''Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa kuma ku fadi magana wadda take daidai. Sai Ya gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, hakika ya rabauta da rabo mai girma.'' (Ahzabi: 71-72).

Ya ku Musulmi! Babu abin da yake maganin wawa, irin yin hakuri, kuma babu abin da yake maganin jahili irin shiru. Idan ka yi shiru ga jahili hakika ya ishe shi jawabi, kuma ya ishe shi ukuba. Kuma babu hutu face ta yin afuwa da danne zuciya. Hakika an ce: ''A cikin danne zuciyarka akwai hutu gare ka.'' Al-Ahnaf Bin kais ya ce: ''Babu wani da zai yi gaba da ni face na kama shi a cikin al'amrinsa da halaye uku: Idan yana sama da ni, sai in ba shi girmansa, idan yana kasa da ni sai in daukaka matsayinsa; idan kuma tsarana ne sai in samu daukaka a kansa.''

Domin haka ku yi afuwa ku yi yafiya. Ku tuna da ladar afuwa da sakamakon yafiya da akibar hakuri. Ku guji abin da zai raunana karfinku ko ya rarraba kanku.

Ku yi salati da taslimi a bisa mai shiryar mafificin halitta (SAW).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Saturday, May 21 @ 21:03:57 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Shiri Domin Gamuwa Da Allah (6)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: