Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Sha'aban Da Kintsa Wa Ramadan 02
 
 
Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc Daga hudubar Yaseen Bi-Asbi'i
Masallaci: Ba a fada ba
Fassara Salihu Makera

Sha'aban Da Kintsa Wa Ramadan 02

Huduba ta farko
Hamdala da taslimi.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa. A kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita. Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da wuni a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.'' (k: 25:62).

Ya ku muminai! Mai rabo ya samu rabo a watan Rajab (mai karewa), ta wajen ayyukan da'a da kusanci ga Allah. To ga shi muna gab da shiga watan Sha'aban, me muka shirya za mu yi a cikinsa?

An kira wannan wata Sha'aban ne saboda Larabawa suna watsuwa a cikinsa don neman ruwa. Wadansu kuma sun ce, ana kiransa haka ne saboda watsuwarsu wajen kai hare-haren yaki bayan fita daga watan Rajab Mai alfarma. Wadansu suka ce saboda wata ne da ke bayyana, a tsakanin Rajab da Ramadan.

Falalarsa da abin da ake so a rika yi a cikinsa: Hakika ya zo daga Ahmad da wadansu, kuma Ibn Khuzaima ya inganta shi, sannan Albani ya kyautata shi daga Usama bin Zaid, ya ce: ''Na ce: ''Ya Manzon Allah! Ban gan ka kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha'aban ba! Sai ya ce: ''Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan. Shi ne watan da ake daukaka ayyuka zuwa Ubangijin talikai. Don haka nake son a daukaka aikina ina cikin azumi.''

Ya ku Musulmi! Ba ku ganin yadda mutane suke gafala a yau daga watan Sha'aban? Suna gafala daga ayyukan da'a da neman kusanci ga Allah. Suna nutso a cikin sha'awoyi da ayyukan jin dadi. Suna gafala daga Sha'aban alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance yana raya shi da ayyukan da'a da azumi. Ya ce da Usama: ''Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan.''

Mutane suna gafala daga Sha'aban saboda yana tsakanin watanni biyu masu girma wato Rajab da Ramadan. Mutane sun fi shagala da su biyun, don haka sai aka shagaltar da su daga gare shi. Ta kai wadansu mutane suna ganin azumin watan Rajab (azumin tsofafi in ji Hausawa), ya fi azumin Sha'aban, saboda shi Rajab wata ne Mai alfarma. Wannan ba daidai ba ne, azumin Sha'aban ya fi na Rajab falala saboda fadin Annabi (SAW): ''Ana daukaka ayyuka a cikinsa, kuma ina son a daukaka aikina ina azumi.''

Hakika malamai (Allah Ya yi musu rahama) sun ce: ''A cikin wannan Hadisi akwai dalili cewa mustahabbi ne a raya lokutan da mutane suka gafala da ayyukan da'a, kuma hakan abin so ne a wurin Allah Mabuwayi.''

Don haka ku koma ga Allah ya ku bayin Allah! Ku sallama ga abin da Yake yarda da shi, domin lada da ijara suna kara martaba idan aka yi su a lokacin da mutane suka gafala, fa'idojin raya shi da da'a ita ce mafi girma. Kuma wadannan fa'idoji za a same su ne idan aka yi ayyukan da'ar a asirce tare da boyewa. Sirrantawa da aikata aikin da'a a boye daya ne daga cikin manya sabubban karbar aiki. Akwai bukatar aiki ya kasance don Allah, a nesanta shi daga jiyarwa da riya.

Ku sani aikin da'a a lokacin gafalar mutane yana da wahala a tsakanin mutane. Mafi falalan aiki, shi ne wanda ya fi wahala ga mutane matukar ya dace da Sunnar Annabi (SAW). Manzon Allah (SAW) ya ce: ''Ladar aiki na dogara ne da irin wahalar da aka sha a kansa.''

Ya bayin Allah! Lallai ana daukaka ayyukan shekara zuwa ga Allah a watan Sha'aban. Ayyukan bayi suna bijirowa ga Allah bijirowa a kowane wuni da dare, sannan ayyukan mako su bijiro gare Shi a kowace Litinin da Alhamis, sannan a bijiro da ayyukan shekara a Sha'aban. Ga kowace bijirowa akwai hikima, Allah Yana bayyana su ga wanda Ya so daga cikin halittunSa, ko Ya asirta shi a wurinSa, alhali babu abin da Yake boyuwa ga Allah daga ayyukan bayinSa.

Ya ku muminai! A yayin da Sha'aban ya zama kamar kofar shiga Ramadan-kuma ba makawa ga tattalin zuwansa- sai aka shar'anta yin azumi da sauran ayyukan da'a a cikin Sha'aban domin kusantar Allah ta yadda za a yi tattalin zuwan Ramadan, a tarbe shi cikin annashuwa da shauki da sabo da da'a ga Mai rahama. Don haka ne Annabi (SAW) yake yawaita azumi a cikinsa, yake cin ganimar lokacin gafalar mutane duk da matsayinsa, na wanda aka gafarta masa abin da ya gabatar da wanda ya jinkintar na zunubinsa. Don haka ne magabatan kwarai suke kara kokari a Sha'aban suke tattalin zuwan Ramadan.

Ya kai bawan Allah! Me ka shirya a Sha'aban don marabtar Ramadan? Wane tattali ka yi masa?

Ka yi tattalin kanka da abin da Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar, wato yawaita azumi a watan. Hakika Annabi (SAW) yana yawaita azumi a cikinsa. An karbo daga A'isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ce: ''Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har sai mun ce ba ya shan ruwa, kuma yana shan ruwa har sai mun ce ba ya azumi. Amma ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata guda ba, sai a Ramadan. Kuma ban taba ganin ya yawaita azumi a wani wata fiye da Sha'aban ba.'' Buhari da Muslim suka ruwaito.

A wata ruwaya ta Buhari ya ce, ''Ya kasance yana azumtar Sha'aban dukkansa.'' Muslim kuma ya ruwaito cewa: ''Yana azumtar Sha'aban sai dan kadan.'' A ruwayar Abu Dawud ya ce: ''Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha'aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.''

Dukkan wadannan Hadisai ingantattu ne, kuma wannan yana nuni ne da tsananin kiyayewarsa ga azumi a cikin Sha'aban. Manufa ita ce ya fi yin azumi a cikinsa ba wai yana azumtarsa gaba daya ba.

Ibn Hajrin (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: ''Ya fi yin azumin tadawwa'i a cikin Sha'aban ne fiye da kowane wata. Ya kasance yana azumtar mafi yawan kwanakin Sha'aban.''

Ya ku Musulmi! Malamai sun ce: ''Yin azumi a Sha'aban ya fi falala daga yin azumi a sauran watanni kamar azumin Muharram, wanda shi ne mafi falalar azumi a bayan Ramadan. Domin falalar azumin tadawwa'i ya kasance a kusa da azumin farilla na Ramadan a gabansa ko bayansa. Domin yana daf da azumin Ramadan, sai ya yi kamar an jeranta azumin sunnoni da na farilla a gabansa da bayansa. Don haka azumin Sha'aban kamar Sunnah ce ta kabliyya ga Ramadan, yayin da azumin shida na Shawwal suke zaman Ba'adiyya gare shi. Jerantattun sunnoni sun fi tadawwa'in da ke zaman kansa cikin abin da ya shafi Sallah. To kamar haka lamarin yake, cewa yin azumi a gabani ko bayan Ramadan ya fi falala daga yin azumi mai zaman kansa da bai saduwa da shi.

Ibn Rajab (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: ''Game da azumin Sha'aban an ce: ''azumtarsa kamar jarrabawar share-fage ce ga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan bisa wahala. Kai yakan zamo mutum ya san wani abu kan azumin tare da sabawa da shi, ya samu dandanon Ramadan ta hanyar azumin Sha'aban, kuma ya shiga watan azumin Ramadan da karfin jiki da nishadi.''

Ya bayin Allah! Wanda azumin Sha'aban zai raunana shi daga yin azumin Ramadan, to, ya dakatar da azumin idan Sha'aban ya je kusan karshe, saboda fadinsa (SAW): ''Idan Sha'aban ya kai karshe, kada ku yi azumi har zuwa Ramadan.'' Ahmad da wadansu suka ruwaito, Albani ya inganta shi, amma a isnadinsa akwai magana.

Hanin da ke cikin Hadisin domin a samu karfin yin azumin Ramadan ne. Wadansu sun ce: ''Hanin a kan wanda ya sha ruwa ne, bai azumci farkon watan ba, don haka idan Sha'aban ya zama saura kadan ba zai yi azumi ba.

Na biyu: Ya kai bawan Allah! Da me za ka kintsa kanka domin shiga Ramadan? Ka kintsa kanka da abin da ya sauwaka na aikin da'a, kamar yawaita karatun Alkur'ani da sadar da zumunta da sauransu. Salmata bin Kuhail ya ce: ''Ana cewa: ''Watan Sha'aban watan masu karatu.'' Abubakar Albalkhiy kuma ya ce: ''Watan Rajab watan shuka, watan Sha'aban watan ban ruwa, watan Ramadan kuma watan girbi. Wanda bai yi shuka a Rajab ba, bai bayar da ruwa a Sha'aban ba, ta yaya zai yi girbi a Ramadan?''
Ya kai Musulmi! Rajab ya wuce, me za ka yi a Sha'aban, idan kana nufin girbi a Ramadan? Ka dai ji halin Annabinka (SAW) da magabatan kwarai na wannan al'umma a cikin wannan wata, a wane matsayi kake kan wadannan ayyuka da darajoji? Ka yi gaggawa zuwa ga da'a ga Mabuwayi Mai yawan gafara.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 05:47:47 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc:
Aliyu (r.a) Yayi Mubaya'a Ga Khalifancin AbuBakar (r.a)!


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc

"Sha'aban Da Kintsa Wa Ramadan 02" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: