Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Husuma Don Kare Karya Yanki Ne Na Munafunci (1)
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Daga Hudubar Sheikh Abu Ibrahim Sa'ud bin Ibrahim as-Shuraim
Masallacin Haramin Ka'aba da ke Makka

Husuma Don Kare Karya Yanki Ne Na Munafunci (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Makagin halitta da ake komawa gare Shi. Mai aikata abin da Ya yi nufi, Ya saukar da Alkur'ani Mai girma a cikinsa akwai gargadi da jan kunne da kwadaitarwa da tsoratarwa. ''karya ba ta zuwa ta gaba gare shi ko ta bayansa, abin saukarwa ne daga Mai hikima Abin godewa.'' Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, shaidar da nake fatar tsira da ita daga narkon azaba. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, mai bushara ga mai neman shiriya, mai gargadi ga mai ketare iyaka, ya nuna duk wani al'amari mai kyau. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa taurarin shiriya da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, wasiyyar da nake gabatar muku ya ku bayin Allah, ita ce ta ku bi Allah da takawa da lizimtar jama'a da tsarkake zuciya da kwance kanku daga sarkakiyar kiyayya da take gadar da kaskanci ta tayar da fitina ta kuma rusa soyayyar da ke tsakanin Musulmi. Ina yi muku hani daga sabani da rarraba domin suna hallaka al'umma, suna cinye kyawawan halaye kamar yadda wuta take cinye kirare. ''Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukuncinsa (ku mayar da shi) zuwa ga Allah, wancan Shi ne Allah Ubangijina a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina.'' (k: 42: 10)

Ya ku mutane! Lallai husuma a tsakanin mutane al'amari ne da ba makawa za ta rika aukuwa, face wadanda Ubangiji Ya yi musu rahama. Domin mafi yawan masu hulda sashinsu na cutar da sashi face wadanda suka yi imani suka aikata ayyuka na kwarai kuma 'yan kadan ne ke hakan.

Ya ku mutane! Asalin abin da ke ga mutane shi ne, rashin sabani da husuma, amma sai hakan ya kau daga lokacin da daya daga cikin 'ya'yan Annabi Adam (AS) ya kashe dan uwansa, sai al'amari ya sauya aka wayi gari sabani da husuma abu ne da ba za a iya kauce musu ba. Sai dai kuma kusancin mutane ga aiki da shari'a, ya rika hana aukuwar hakan daga lokaci zuwa lokaci.

Kuma husuma da makiya ta fi tsanani daga wadda ake yi tsakanin masoya, sannan ta fi aukuwa a tsakanin wadanda suke kusa daga wadanda suke nesa. Kuma ta fi muni a tsakanin makwabta daga tsakanin iyali guda, sannan a cikin 'ya'ya ta fi muni a tsakanin shakikai. Haka dai lamarin yake a tsakanin makusanta da makusanta har zuwa abin da ya sauwaka.

Saboda haka ne shari'ar Musulunci ta zo tana mai sukar husuma, tana yaki da jayayya, tana tsoratarwa kan wuce iyaka a cikinsu da wuce gona da iri a kansu, wato a yi su don neman gano gaskiya, kuma ta sanya wanda yake wuce iyaka ya zamo yana da siffa daga cikin siffofin munafunci, ta hanyar aikata fajirci a lokacin husuma, wato kaucewa daga gaskiya.

Abu ne sananne cewa husuma tana aukuwa a tsakanin mutane kodai a cikin ibadoji ko mu'amaloli, kuma mu'amalar ko ta zamo niyya ce ko magana ko aiki. To duk wanda ya ketare iyaka wajen husuma a wadannan abubuwa uku, yana da yanki na munafunci gwargwadon abin da ya siffantu da shi. Annabi (SAW) ya tara hakan cikin fadinsa: ''Alamun munafuki uku ne: Idan ya yi magana ya yi karya; idan ya yi alkawari ya saba; idan aka ba shi amana ya yi ha'inci.'' Buhari da Muslim suka ruwaito. A wata ruwayar da ta fi dacewa da batunmu, ya ce, ''Idan ya yi husuma ya yi fajirci.''

Fajirci a cikin husuma sulusin mu'amaloli ne, domin magana tana fuskantar kalubale daga karya da fajirci a cikin husuma. Niyya kuma tana fuskantar kalubale daga saba alkawari, yayin da aiki ke fuskantar kalubale daga ha'inci.

Ya bayin Allah! Mai fajirci a cikin husuma shi ne wanda yake sane cewa ba ya kan gaskiya, amma ya tsaya yana kare karyar, har ya auka cikin abin da Allah Ya hana cikin fadinSa: ''Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadar da ita ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi alhali kuwa ku, kuna sani.'' (k: 2: 188). Wani magabacin kwarai ya ce: ''Wannan aya tana magana ne kan mutumin da yake husuma ba tare da hujja ba, kuma ya san ga inda gaskiya take, amma ya kauce mata.''

Ya bayin Allah! Mai fajirci cikin husuma- harshensa yana gaba da hankalinsa, kausasawarsa ita ce hakurinsa, zaluncinsa shi ne adalcinsa, harshensa ba ya da linzami, zuciyarsa kazantacciya ce, yana jin dadin tuhumar wadansu da kauce wa abin da shari'a ta ajiye.

Fajiri a wajen husuma yakan kara karya 100 a kan gaskiya daya. Shi kamar kuda yake, ba ya sauka sai a kan kazantar mutane, yana dubi ne da idon adawa, domin da idon yarda yake dubi da ya kyautata abin da ya baci, ba ya ganin abin kirkin mutane sai zunubansu. Wayyo Allah! Wane uzuri ne mai wannan hali zai bayar? Za ka gan shi yana cin mutuncin mutane, mai zunde mai watsa annamimanci, dan ta'adda mai yawan zunubi. Yana da dabi'a irin ta tsutsa, wadda ba ta shiga cikin abu, face ta lalata shi ko ta kazantar da shi.

Mai fajirci wajen husuma ya bayin Allah! Ba ya da amana kuma ba ya da sutura, yana da dabi'ar zargi. Idan ka saba masa a cikin kankanen abu, sai ya watsa sirrinka ya keta mutuncinka, ya tuno laifinka na baya da na yanzu. Aboki nawa ne ya tona asirin abokinsa, saboda sabanin da bai kai ya kawo ba? Mazaje da yawa sun faffallasa sirrin matansu, saboda gishiri bai ji a miya ba, ko rashin wanke sutura ko makamantan haka.

Ba husuma ne abin zargi ba, tunda abu ne da ba makawa tana cikin zukatan mutane da kwakwalensu da dukiyarsu da mutuncinsu da addininsu, domin babu mutumin da zai iya gamsar da dukkan mutane, abin zargi shi ne ketare iyaka wajen husuma.

Babban abin mamaki ya bayin Allah! Shi ne abu ne mai sauki a wurin mutane da dama su ci haram ko su yi zina ko su yi zalunci da sata da sauransu, amma abu ne mai wahala a gare su, su tsare harshensu. Mutum nawa ne muke gani suna aikata wadannan miyagun ayyuka da alfasha, suna tsoma harsunansu cikin cin mutuncin mutane, ba tare da sun damu da abin da za su fada ga abokan husumansu ba, alhali Allah Madaukaki Yana cewa: ''Lallai Allah Yana yin umarni da adalci da kyautatawa, da bai wa ma'abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin da aka ki da rarrabe jama'a. Yana yi muku gargadi tsammaninku, kuna tunawa.'' (k:16:90).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 05:56:14 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"Husuma Don Kare Karya Yanki Ne Na Munafunci (1)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: