Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
[ Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi ]

·Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)
·Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi
·Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto
·**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)
·IBN TAIMIYYAH GWARZON NAMIJI. (Misbahu Abdullahi)
·Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi'ah
·AA'SHUURAA (1) BANDA BIDI'AR SHI'AH BANDA KUMA BIDI'AR NAASI
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Azumi Da Abubuwan Da Yake Koyarwa (2)
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen By Salihu Is'hak Maker

Azumi Da Abubuwan Da Yake Koyarwa (2)

Alkhurdabi ya ce: ''Azumi sirri ne a tsakanin bawa da Ubangijinsa, babu mai gano hakikaninsa sai Shi (Allah), domin haka ya kasance kebantacce gare Shi.'' (Al-Jami'u Li Ahkamil kur'an, Mujalladi na 2 shafi na 274).

Azumi da hakuri:

Baya ga takawa da kange gabbai da sanya wa dan Adam ikhlasi, azumi yana koyar da hakuri, bilhasali ma azumi wani yanki ne na hakurin kamar yadda Ibnu Rajab ya nuna: ''Azumi yana daga cikin hakuri. Shi kuma hakuri nau'o'i uku ne: kuma duka nau'o'in uku sun hadu a cikin azumi. Domin a cikinsa akwai hakuri a kan yi wa Allah da'a da hakuri daga aikata abin da Allah Ya haramta ga mai azumi na abubuwan sha'awa da kuma hakuri kan abin da zai shafi mai azumi na radadin yunwa da jin kishi da wahalar da rai ke gamuwa da shi da kuma raunin gababuwa. Allah Madaukaki Ya ce: ''Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.'' (k:39:10).'' (Lada'iful Ma'arif, shafi na 284 da Mawaridul Zam'an, Mujalladi na 1 shafi na 357).

Ibnu Aiyinah ya ce: ''Azumi shi ne hakuri, mutum yana hakurtar da kansa daga abinci da abin sha da jima'i. Sannan ya karanta: ''Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.'' (k:39:10).'' (Sharhu Sahihil Bukhari na Ibnu Baddal, Mujalladi na 4 shafi na 9).

Ibnu Hajri kuma ya ce: ''Masu hakuri su ne masu azumi a mafi yawan maganganu.'' (Fathul Bari, Mujalladi na 4, shafi na 130).

Abu Huraira (RA) ya ce: ''Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''Watan hakuri da ranaku uku na kowane wata azumin shekara ne.'' Suyudi ya ce: ''Watan hakuri shi ne watan Ramadan. Kuma asalin hakuri shi ne kamewa, sai aka kira azumi da hakuri saboda abin da ke cikinsa na kame rai daga ci da sha da jima'i.'' (Sharhu Sunani Nisa'i, Mujalladi na 4 shafi na 218).

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce da wani mutum: ''Ka azumci watan hakuri da wuni daya a kowane wata.'' Sai ya ce: ''Ka kara min domin ina da karfi.'' Sai ya ce: ''Ka azumnci wuni biyu.'' Sai ya ce: ''Ka kara min.'' Sai ya ce: Ka azumta daga masu alfarma, ka bari, ka azumta daga masu alfarma, ka bari, ka azumta daga masu alfarma, ka bari. Sai ya fadi (yana nuni da) yatsunsa guda uku ya damke su sannan ya sake su.'' (Abu Dawuda da Ibnu Majah da Ahmad suka ruwaito).

Al-Khidabi ya ce: ''Fadinsa: ''Daga masu alfarma,'' to lallai masu alfarma watanni hudu ne. Su ne wadanda Allah Madaukaki Ya ambata a cikin LittafinSa, inda Ya ce: ''Lallai kidayar watanni a wurin Allah guda goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah ranar da Ya halitta sammai da kasa, daga cikinsu akwai hudu masu alfarma.'' (Tauba:36). Su ne watan Rajab da Zul-kida da Zul-Hajji da Muharram.'' (Mu'alimus Sunani, Mujalladi na 3 shafi na 306).

Domin haka Ramadan wata makaranta ce ta koyon hakuri, shi ya sa Ibnu Rajab Al-Hambali ya ce: ''Mafi falalar nau'o'in hakuri shi ne: Azumi, domin shi ya tara hakuri a kan abubuwa uku. Shi hakuri ne a ka yi wa Allah Madaukaki da'a. Sai hakuri daga saba wa Allah, domin bawa yana bari sha'awoyinsa domin Allah a lokacin da ransa ke jayayya da shi kan ya aikata shi. Saboda haka ne ya zo a cikin Hadisi ingantacce cewa lallai Allah Madaukaki Yana cewa: ''Dukkan aikin dan Adam nasa ne sai dai azumi, lallai shi Nawa ne, Ni zan saka a kansa. Lallai shi ya bar sha'awoyinsa da abincinsa da abin shansa saboda Ni.'' (Buhari, Babin Azumi Hadisi na 1805 da Muslim Babin Azumi, Hadisi na 1151).

Azumi da shukura ga ni'ima:

Sheikh Abdul'aziz As-Salman ya ce: ''Azumi yana kira zuwa ga yin shukura ga ni'imar Allah. Domin shi kame rai ne daga abinci da abin sha da saduwa da mata. Kuma mutum ba zai san girman wadannan ni'imomi ba, sai bayan ya rasa su, sai wannan ya farkar da shi ga tsayuwa da yin shukura a kansu. Kuma zuwa ga haka ne Allah Madaukaki Ya yi ishara a cikin fadinSa: ''Tsammaninku za ku yi godiya (shukura)'' (Bakara: 185).

Azumi da dabi'ar karimci da tausaya wa fakirai:

Ibnu Rajab ya ce: ''An tambayi wani daga cikin magabata (Salaf) don me aka shari'anta azumi?'' Sai ya ce: ''Domin mawadaci ya dandani yunwa ya daina mantawa da mayunwaci.''

Sheikh Muhammad Rashid Rida ya ce: ''Lallai lokacin da mai azumi ya ji yunwa zai tuna da wanda bai samun abinci, sai hakan ya sanya shi ya rika tausayawa da jinkai da za su sanya ya rika yawaita kyauta da sadaka. Hakika Allah Ya siffanta AnnabinSa da cewa mai tausayi ne mai jinkai. Don haka Ya yardar wa bayinSa muminai abin da Ya yardar wa AnnabinSa (SAW), domin haka ne Ya umarce su da koyi da shi.''

An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: ''Manzon Allah ya kasance mafi kyauta da alheri ga mutane, amma ya fi yin kyauta a cikin watan Ramadan, lokacin da Jibrila ke ganawa da shi.'' Zubairu bin Al-Munir ya ce: ''Ma'ana alherinsa da kyautatawarsa (SAW) suna game mai siffar fakiranci ko mabukaci da wanda ke da siffar wadata da isa fiye da yadda girgijen da iska ke gamewa wajen saukar da ruwa.''

Ibnu Hajrin ya ce: ''Lallai a cikinsa akwai cewa yawan karanta Alkur'ani yana jaddada alkawari wajen karin wadatar zuci. Wadatar zuci kuma sababi ne na yin kyauta. Kyauta kuma a shari'a ita ce: ''Ba da abin da ya dace ga wanda ya dace. Kuma ita ta fi gamewa fiye da sadaka. Kuma har wa yau Ramadan lokaci ne na alherai, domin ni'imar Allah a kan bayinSa a cikinsa tana karuwa a kan waninsa.....'' (Fathul Bari, Mujalladi na 1 shafi na 31).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 06:08:06 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"Azumi Da Abubuwan Da Yake Koyarwa (2)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: