Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
[ Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi ]

·Sabuwar Shekarar 1439 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi (2)
·Sabuwar Shekarar 1409 BH: Watannin Musulunci a kundin tarihi
·Me Ya Sa Yan Shi'a Suke Kin Banu Umayya?! -Dr Mansur Sokoto
·**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)
·IBN TAIMIYYAH GWARZON NAMIJI. (Misbahu Abdullahi)
·Halin Musulmi Na kwarai Ranar Ashura, Da Halin Masu Bi'ah
·AA'SHUURAA (1) BANDA BIDI'AR SHI'AH BANDA KUMA BIDI'AR NAASI
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB
·AHLUS SUNNAH BA YA ZAGIN SAHABIN MANZON ALLAH SAWA'UN ALIYYU BIN ABI TALIB

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Yadda Za Mu Shiga Watan Ramadan
 
 
Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai Hudubar Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan

Yadda Za Mu Shiga Watan Ramadan

Masallacin NASFAT na kasa da ke Abuja
Fassarar Salihu Makera

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Wanda Ya ce: ''Lallai adadin watanni a wurin Allah goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah, ranar da Ya halitta sammai da kasa daga cikinsu akwai hudu masu alfarma.''

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai shugabanmu masoyinmu abin girmamawanmu kuma maulanmu Muhammad ManzonSa ne, wanda ya ce: ''Allah Ya turbuda hancin wanda ya riski Ramadan amma ba a gafarta masa ba.'' Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

Bayan haka, ku bi Allah da takawa ku yi bincike, kuma ku sani, sani na yakini cewa ''Lallai ne Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa.''

Hudubarmu ta yau tana magana ne kan yadda za mu shiga watan Ramadan.


Ya bayin Allah! Me ya yi kama da dare mai wucewa a wadannan ranaku da suke gaggawar wucewa, kamar kyiftawar ido. Hakika mun fuskanci Ramadan sannan muka yi ban-kwana da shi, kamar jiya-jiyan nan, ga shi mun sake tunkarar wani Ramadan din!

Ya ku 'yan uwa! Da za mu duba, a cikinmu za mu ga wasunmu da suka riski azumi bara, sun wayigari cikin mutanen kabari! Kuma ta yiwu wasunmu a bana su kasance cikin wadanda Allah Ya kaddara za su azumci watan cikakke, kuma Ya kaddara musu su kasance cikin rayayyu su cimma wani Ramadan din su azumce shi su yi tsayuwarsa. Da kowannenmu zai rika jin wannan al'amari a jikinsa, ya rika tattalin mutuwa bayan Ramadan ko a cikinsa da ya azumci Ramadan yana mai imani da fatar samun lada, kuma da ya yi tsayuwarsa yana mai imani da fatar samun lada domin ya samu sa'ada da rabauta da Aljanna.

Tattalin zukata da yin aiki domin wannan wata:

1. Dagewa da yin addu'a kafin zuwan Ramadan, daga cikin addu'o'in da aka samu a nassi, akwai: ''Allahumma barik lana fi Rajab wa Sha'aban. Wa balligna Ramadan.'' Ma'ana ''Ya Ubangiji! Ka yi mana albarka a cikin Rajab da Sha'aban, kuma Ka riskar da mu Ramadan.'' Da kuma ''Allahumma sallimni ila Ramadan wa sallimi li Ramadan wa sallim minni mustakbilan.'' Ma'ana ''Ya Ubangiji Ka isar da ni Ramadan lafiya, Ka sa in yi Ramadan lafiya kuma Ka kai ni wani Ramadan lafiya.''

An karbo daga Abu Huraira (RA) a cikin Hadisin kudisiy cewa: ''Idan bawaNa ya yi tunani ko niyyar aikata alheri a zuciyarsa, lallai Ni, sai in rubuta masa ladansa.''

2. Ya kyautata niyyarsa kafin Ramadan ta wajen yin ayyuka nagari, kamar:

1. Yawaita saukar karatun Alkur'ani tare da tadabburi. ''Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabeewa…''
2. Daga ciki akwai niyyar tuba ta gaskiya daga dukkan zunuban da suka gabata.

3. Sai niyyar wannan wata ya zama fara rabuwa da munanan ayyuka tare da yin kyawawan ayyuka har abada da izinin Allah.

4. Niyyar kyautata hali da dabi'a da yin mu'amala mai kyau ga dukkan mutane.

5. Niyyar yin aiki ga wannan addini da yada shi a tsakanin mutane ta hanyar shagaltuwa da gyaran ruhin da ke cikin wannan wata.

6. Niyyar sanya wani jadawali mai cike da ibada da ayyukan da'a da sabunta lizimtar abin da ake umarni kan a aikata shi.

Allah Madaukaki Ya ce: ''Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fadinta (daidai da) sammai da kasa ne, an yi tattalinta domin masu takawa. Wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafe wa mutane laifi. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa. Wadanda suke idan suka aikata wata alfasha ko suka zalunci kansu sai su tuna da Allah, kuma su nemi gafarar zunubansu ga Allah. Kuma wane ne ke gafara ga zunubai, face Allah? Kuma su ba su doge a kan abin da suka aikata ba, alhali kuwa suna sane. Wadannan sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu (suna) da Gidajen Aljanna (wadanda) koramu na gudana daga karkashinsu, suna madauwama a cikinsu, kuma madalla da ijarar masu aiki.''

Daga cikinsu akwai sadakar Ramadan ko zakka:

Idan zakka ta kasance farilla ce a kanka, to ba makawa ga shirya mata. Ita ce ta uku cikin ginshikan Musulunci. Kuma hakika Musulunci ya umarci wasu Musulmi kan al'amarin zakka. Duk dukiyar da aka bayar da zakkarta, sai albarkarta ta karu. Ita sau daya ce a shekara tare da cikar nisabi. Amma sadaka ita ba ta yankewa har abada, za ka yi ta bayar da ita har karshen rayuwarka. Allah Madaukaki Ya ce: ''Ka karba daga cikin dukiyarsu wata sadaka da kake tsarkake su da tsabtace su da ita. Kuma ka yi musu addu'a, lallai addu'arka natsuwa ce a gare su.''

Sai kuma sanya hannu wajen ciyar da masu azumi na daukacin watan. Aikin alheri ne a tara abin ciyarwa da za a rika rarraba wa fakirai tun daga farkon watan.

Sai tafiya dakin Allah Mai alfarma domin gudanar da Umara.

Ya Ubangiji! Ka isar da mu Ramadan don hakkin Lahaula wala kuwwata illa billah.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Wanda Ya farlanta azumin Ramadan a kanmu, kuma Ya sanya shi rahama ga talikai. Na shaida babu abin bautawa sai Shi. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, bayan haka:

Yadda za mu shiga wata Ramadan.

1. Daga ciki ya bayin Allah! Akwai rage tafiye-tafiye musamman zuwa kasashen waje a cikin watan Ramadan idan ba Umara da abin da ya shafi al'amuran addini ba.

2. Ka takaita cin abincinka domin tattalin zuwan watan Ramadan domin ka samu lada ninki ba ninki.

3. Daga ciki akwai hutar da rai da jiki, ka rage shagulgulanka ko ayyuka kafin Ramadan, kuma ka tsabtace zuciyarka gare shi.

4. Ka yi azumi a Rajab da Sha'aban gwargwadon ikonka.

5. Ka yi tattali ga watan Ramadan ta yadda azumin Ramadan ba zai zamo bako ga jikinka ba, bayan shekara guda cikakkiya rabonka da azumin.

Allah Madaukaki Ya ce: ''Ku yi azumin shi ne mafi alheri a gare ku, in kun kasance kuna sani.''

6. Daga ciki ya bayin Allah! Akwai karanta littattafai da mujallun da suka shafi watan Ramadan da hukunce-hukuncen azumi a cikinsa.

7. Ka shirya iyalanka don watan na Ramadan ta hanyar wa'azi da fadakarwa da bayanin hukunce-hukuncen azumi da abin da yake kyautata shi na daga niyya da ayyukan ibada da sauransu.

Allah Madaukaki Ya ce: ''Ka gargadi 'yan uwanka makusanta.'' Kuma Ya ce: ''Ka umarci iyalanka da yin Sallah da kuma hakuri a kanta. Ba mu tambayar wata dukiya daga gare ka, Mu ne ke azurta ka, kuma kyakkyawan karshe na masu takawa ne.''

Sayyidina Aliyu (Karramallahu Wajhahu) ya ce: ''Ka koya wa iyalinka ladabi zai amfane su.''

Mai tsira da Amincin Allah ya ce: ''Ka ribaci abubuwa biyar gabanin biyar: Rayuwarka kafin mutuwarka da lafiyarka kafin rashin lafiyarka da wadatarka kafin talaucinka da lokacinka kafin shagaltuwarka da kuma samartarka kafin tsufarka.''

''Lallai Allah Yana yin umarni da adalci da kyautatawa da bai ma'abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani ga alfasha da abin da aka ki da rarrabe jama'a. Yana yi muku gargadi, tsammaninku, kuna tunawa.''
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 06:09:23 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· EsinIslam Turanci Kusa
· Fiye Da Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai:
MARTANI: Yadda rikicin Izala da darika ya kasance a Sabo Ibadan: Kwan-gaba kwan-


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai

"Yadda Za Mu Shiga Watan Ramadan" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: