Muhawara Hausa
 



Tuba Da Sharuddanta
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji Daga Hudubar Sheikh Muhammad bn Saleh Al-Usaimin

Fassarar Salihu Makera

Tuba Da Sharuddanta

Godiya ta tabbata ga Allah, Mai yawan afuwa, Mai yawan gafara, Wanda ni'imarSa ba ta yankewa, kuma Yana karbar tuba daga wanda ya tuba, Ya gafarta wa wanda ya komo zuwa gare Shi. Muna gode maSa Madaukaki godiyar mai mika da shukura. Muna neman tsari da hasken fuskarSa Mai girma daga kafirci da fajirci. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mahaliccin sammai bakwai. Kuma na shaida shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, mai cikakken haske. Ya Ubangiji Ka kara tsira da aminci a gare shi a alayensa tsarkaka da sahabbansa shugabannin shiriya da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da takawa, ku tuba zuwa gare Shi ta hanyar komawa gare Shi daga barin sabo zuwa ga da'a, daga nisantarSa zuwa ga kusantarSa. Ku tuba daga daudar zunubi zuwa ga tsarkakuwa, domin lallai Allah Yana son masu yawan tuba, kuma Yana son masu tsarkakuwa. Ku sani lallai wajibi ne a tuba daga zunubi cikin gaggawa, ba ya halatta a jinkirta ta, ko a yi kasala a kanta, domin jinkirta tuba wani zunubi ne da yake bukatar tuba a kansa shi ma.

Tuba wajiba ce saboda Allah ne Ya yi umarni da ita a cikin LittafinSa, kuma Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da ita, ya sanya ta a cikin ayyukan rabo da dacewa a duniya da Lahira. Allah Madaukaki Ya ce, ''Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba gare Shi, sai Ya jiyar da ku dadi, dadi mai kyau zuwa wani lokaci ambatacce, kuma Ya zo wa kowane ma'abucin falala da falalarsa.'' Sannan Allah Madaukaki Ya ce, ''Ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku Muminai! Tsammaninku za ku samu nasara.'' Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah, kuma ku nemi gafararSa, domin ni hakika ina tuba zuwa ga Allah a kowace rana sau dari.'' Kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce ''Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: ''''Ni ina neman gafarar Allah tare da tuba gare Shi a kowace rana fiye da sau saba'in.'' Buhari ya ruwaito shi.

Ya ku Musulmi! Lallai tuba ga Allah wajibi ne, kuma cikin gaggawa, domin umarnin Allah da na ManzonSa duk ana bin su ne cikin gaggawa, domin ba a samu dalilin hallacin jinkirta su ba. kuma jinkirta tuba sababi ne na hauhawa da damfaruwar zunubai su yi tsatsa a kan zukata. Ya zo cikin Hadisi daga Annabi (SAW) cewa, ''Idan mumini ya yi wani zunubi sai ya zame masa bakin gudan jini a zuciya, idan ya tuba sai a wanke shi daga cikinta, idan ya kara sai ya yi ta girma har sai ya toshe kafar zuciya, to wannan shi ne tsatsar da Allah Ya ambata a cikin LittafinSa. ''A'aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai,ya yi tsatsa a cikin zukatansu.'' (83:14).

Ya ku Musulmi! Ku tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, sai Allah Ya shafe zunubbanku da ita, kuma Ya kankare munanan ayyukanku, Ya daukaka darajojinku. ''Ya ku wadanda suka imani! Ku koma (tuba) zuwa ga Allah, komawar gaskiya. Sai Ubangijinku Ya kankare muku miyagun ayyukanku, kuma Ya shigar da ku a cikin gidajen Aljanna, koramu na gudana daga karkashinsu a ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, ''Ya Ubangijinmu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lallai Kai a kan dukkan komai, Mai ikon yi ne.'' (k:66:8).

Tuba ba ta kasancewa ta gaskiya, karbabbiya, har sai ta hada sharudda biyar:

1.Ta kasance bisa ikhlasi domin Allah, wato ya zama an yi ta saboda son Allah da girmama Shi da kwadayin neman ladarSa da tsoron ukubarSa, ba a yi nufin kusanta ko nuna wa abin halitta ba, kuma ba domin neman wani abin duniya ba.

2. Ya zamo mutum ya yi nadama da bakin ciki kan abin da ya aikata na sabo, ta yadda zai yi burin ina ma bai aikata sabon ba, domin nadamar tana wajabta sadda kai a gaban Allah da komawa gare Shi.

3. Mutum ya ciru daga aikata sabo, ya bar shi a take, idan ya kasance na barin wajibi ne, ya aikata shi nan take, idan kuma abin da zai iya rama shi ne ya rama. Idan kuma abin da ya shafi hakkokin bayi ne, ya ciru daga haka, kuma ya mayar musu hakkinsu.

Tuba daga giba ba ta inganta alhali mutum yana ci gaba da ita. Tuba daga riba ba ta inganta alhali mutum yana ci gaba da mu'amala da ita. Da yawa mutane idan aka yi musu nasiha kan su bar sabo, sai wani ya ce maka, ''Allah Ya taimake mu mu iya haka.'' Madallah da abin da ya fada, domin in Allah bai taimaki bawa ba, ba zai tsira ba, sai dai kuma wannan kalma ce ta gaskiya da ake nufin karya da ita, ake neman uzuri don ci gaba da aikata sabo, wannan ba uzuri ne da aka yarda da shi ba, domin an umarci bawa ya yi aiki nagari ne tare da neman taimakon Allah a kan abin da zai amfane shi. Annabi (SAW) ya ce, ''Ka yi yunkuri ka aikata abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka nuna gazawa.''

Ba a karbar tubar wanda ya bar yin Sallah a cikin jama'a, alhali yana ci gaba da kin yin sallar a cikin jama'ar. Ba a karbar tubar mai algushu mai ha'inci, alhali yana ci gaba da aikata su. Duk mai da'awar tuba daga zunubi alhali yana ci gaba da aikata shi, to tubarsa isgili ce ga Allah. Babu abin da za ta kara masa a wurin Allah sai nisanta, kamar mutum ne ya zo maka yana nadamar yi maka wani abu, amma kuma bai daina ba, hakika ba za ka dauki nadamar da yake yi maka face isgili da raina hankali.

Don haka ku ji tsoron Allah kuma ku bi Allah da takawa ya ku Musulmi! Ku tuba ku koma ga Ubangijinku, ku ciru ku bar aikata zunubi, ku yi azamar ba za ku koma ga zunubi a nan gaba ba.

4. Tuba ba za ta zama karbabbiya ba, har sai mutum ya yi azama da niyyar ba zai koma ga zunubin ba a nan gaba. Domin idan bai yi niyyar haka ba, to tubarsa na wani lokaci ne, da zai nemi wani sarari da zai koma ga zunubi, wato dai tubar muzuru, wadda ba ta nuna cewa ya tuba ne, saboda ganin munin abin da yake aikatawa da komawarsa zuwa ga da'a ga Allah.

5. Sannan Tuba ba za ta zama karbabbiya ba, har sai an yi ta a lokacin da ake karbarta, shi ne lokacin da ke gabanin fitar rai ko fitowar rana ta mafadarta. Idan ya zamo an tuba ne a lokacin da ajali ya zo, ko rai yake kokarin fita, ake gagarwar mutuwa ba za a karbe ta ba. Allah Madaukaki ya ce, ''Bai zamo tuba ba, ga wadanda suke aikata miyagun ayyuka, har sai mutuwa ta halarto wa dayansu, ya ce, na tuba yanzu.'' Ma'aiki (SAW) ya ce, ''Lallai Allah Yana karbar tubar bawa matukar bai kai ga gargara ba.'' Kuma idan ya zamo tuba ta zo ne bayan fitowar rana daga mafadarta ba za a karba ba, saboda fadin Allah Madaukaki. ''A ranar da wasu ayoyin Ubangijnka za su zo, imanin ran da bai yi imani ba a gabani ba zai amfane shi ba, ko kuma bai aikata wani alheri ba a gabani.'' Abin nufi da fitar rana daga mafadarta, shi ne idan mutane suka gan ta tana fitowa daga can suka yi imani gaban dayansu, imanin ba zai amfani rai ba, domin bai yi imani ba a gabani ko kuma bai aikata aikin alheri da imanin ba. An karbo daga Abdullahi bn Amru bn Al'as cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, ''Ba za a gushe ba ana karbar tuba har sai rana ta fito daga mafadarta, idan ta fito sai a sanya rufi a kan kowace zuciya da abin da yake cikinta.'' Ibn Kasir ya ce Hadisin mai kyan isnadi ne. Kuma an karbo daga Abu Huraira cewa Annabi (SAW) ya ce, ''Wanda ya tuba gabanin rana ta fito ta mafadarta, Allah Zai karbi tubarsa.'' Don haka ku tuba zuwa ga Allah ya ku Musulmi! Ku mika maSa wuya tare da sallama maSa. Ku hakkake cewa tuba ta gaskiya tana shafe abin da ya gabata na zunubai komai girmansu. Allah Madaukaki Ya ce, ''Ka ce, (Allah Ya ce), ''Ya bayiNa wadanda suka yi barna a kan rayukansu! Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lallai Allah Yana gafarta zunubai gaba daya. Lallai Shi, Shi ne Mai gafara Mai jin kai. Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama maSa,a gabanin azaba ta zo muku, sa'an nan kuwa ba za a taimake ku ba. Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, gabanin azaba ta zo muku, bisa auke, kuma ku ba ku sani ba. (Don) Kada wani rai ya ce, ''Ya nadamata a kan abin da na yi sakaci a cikin sashin Allah, kuma lallai na kasance hakika daga masun isgili! Ko ya ce, ''Da Allah Ya shiryar da ni, da na kasance daga masu takawa. Ko ya ce, a lokacin da yake ganin azaba, ''Da lallai za ce ina da wata komawa (zuwa duniya) da na kasance daga masu kyautatawa. Na'am! Lallai ayoyiNa sun je maka, sai ka karyata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kafirai.'' (k:39:53-59).

Ya Ubangiji! Ka datar da mu ga tuba ta gaskiya wadda za ta shafe abin da ya gabata na zunubanmu, kuma Ka saukaka mana al'amuranmu da ita, Ka daukaka darajojinmu da ita, lallai Kai Mai yawan kyauta ne Mai girma. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, June 12 @ 06:10:44 PDT Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji



"Tuba Da Sharuddanta" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com