Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
FALALA MAI YAWA DAGA HADISAN ANNABI MUHAMMAD SAW
 
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi FALALA MAI YAWA DAGA HADISAN ANNABI MUHAMMAD SAW

Wani lakani ne zan bayar wanda nake fatar in samu lada mai wanda yayi aiki da shi shima ya samu lada. Wanda kuma ya turawa dan uwansa shima ya samu lada.

HADISI NA FARKO Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa kata faren gida a gidan Aljanna sai Sayidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawai tawa sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.

HADISI NA BIYU Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

HADISI NA UKU Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai kiyayeshi daga fitinar dujal.

HADISI NA HUDU Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatal kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.

HADISI NA BIYAR Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da daddare to ka karanta kulya ayyuhal kafirun to bazaka mutu mushriki ba a idan ka mutu a wannan dare.

HADISI NA SHIDA Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu wahadahu lasharika lahu wa anna muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma Jaalni minattauwabina wajaalni minal mutadhahhirina.

Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to zaa bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga.

HADISI NA BAKWAI Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash-hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka waatubu ilaika.

Zaa rubuta wannan acikin wata takarda bazaa bude ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta.

HADISI NA TAKWAS Wani sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabira, Walhamdulillahi kasira, Wasubhanallahi bukratan waasila, Sai manzon Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai manzon Allah ya ce nayi mamakin wadan nan kalma da ka fada, anbude rofofin sama gaba daya saboda wannan kalma da ka fada. Sai Abdullahi Dan Umar ya ce tun daga wannan rana kullum sai na fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba.

HADISI NA TARA Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga rukuu sai ya ce Samiallah Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Rabbana Walakal Hamdu, Hamdan Kasiran Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutum ya ce Ni ne ya manzon Allah Sai manzon Allah ya ce Naga malaika talatin da yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.

HADISI NA GOMA Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda ya yi sallar nafila rakaa goma sha biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna.

HADISI NA SHADAYA Wanda ya kiyaye yanayin nafila rakaa hudu kamin sallar azahar da kuma rakaa hudu kamin sallar laasar to Allah zai haramta masa shiga wuta.

HADISI NA SHA BIYU Manzon Allah Yana cewa Allah ya jikan wanda ya jikan wanda ya yi sallar nafila rakaa hudu kamin laasar.

HADISI NA SHA UKU Wanda yake karanta ayoyi goma da daddare to bazaa rubuta shi cikin gafalallu ba wanda ya ke karanta ayoyi dari to zaa rubuta shi cikin masu bauta ga Allah, wanda kuma ke karanta ayoyi dubu a cikin dare kullum to zaa rubuta shi daga cikin masu arzikin lahira.

HADISI NA SHA HUDU Wanda da yi Sallar nafila a cikin duhu inda bawanda zai ganshi to Allah zai linka masa sau ashirin da biyar na sallar da zai yi wani ya ganshi.

HADISI NA SHA BIYAR Annabin tsira ya ce Wanda yayi sallar walha (Sallar hantsi/Luha) rakaa hudu kuma yayi rakaa hudu kamin sallar laasar, Allah zai gina masa a cikin aljanna.

HADISI NA SHA SHIDA Hakika malaiku suna yin salati ga wadanda suke cika sahun farko, idan suka ga wata kafa a cikin Sallah suna cikata basa barin ta kuma Allah zai cika darajar sa da kimarsa da martabar sa.

HADISI NA SHA BAKWAI Babu wani Bawa da zai yi sujada ga Allah face Allah ya rubuta masa lada ya kankare masa zunubi ya kuma daukaka masa daraja don haka mu yawaita sujjada.

HADISI NA SHA TAKWAS Wanda yayi sallar asuba a cikin jami sannan ya zauna yana ta salati yana ta ambaton Allah bai bari ba harsai da rana ta fito, sannan ya tashi yayi sallar walha rakaa biyu to Manzon Allah ya ce Kamar yayi hajji cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! hajji cikakke! hajji cikakke! hajji cikakke! Haka Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallama ya mai maita.

HADISI NA SHA TARA Manzon Allah ya ce wanda ya yi Sallah arbain a cikin jami maana kwana takwas jami bai tsere masa ba, sallolin nan biyar a jere duk da shi ake kabarta kabbarar harama, to Allah zai rubuta masa kubuta daga musibu guda biyu na farko Allah zai rubuta masa kubuta daga wuta bazai shiga wuta ba, na biyu kuma Allah zai rubuta masa kubuta daga muna funci bazai mutu muna fuki ba.

HADISI NA ASHIRIN Sallar da Allah ya fi so itace sallar asuba ta ranar jumaa a cikin jami, kuma duk wanda ke abin da Allah ke so to Allah zai so shi, idan kuma Allah Ya so shi

HADISI NA ASHIRIN DA DAYA Wanda ya ce Subhanallahil azim Wabihamdihi, zaa dasa masa wata bishiya a cikin gidan Aljanna wadda zai ginda tsinkar alkhairin ta.

HADISI NA ASHIRIN DA BIYU Manzon Allah ya wanda ya ce, duk wanda ya karanta Subhanakallahumma Wabihamdika Ash-shadu Allah Ilaha Illah anta astagfiruka waatubu ilaika, a wajen jira ko inda ake shiririta ko shirme bayan sun gama kamun su watse ya karanta wannan zai zame masa kaffara bisa ga kura kuran da ya tafka a wurin.

HADISI NA ASHIRIN DA UKU Manzon Allah (S.A.W) ya ce Hakika fadar Subhanallahi, Walhamdulillahi, Walaila ha Illallahu, Wallahu Akbar, tana girgijewa mutum zunubai kamar yanda bishiya take girgije ganyen da yake zubuwa a kasa. Don haka mai makon mutum ya zauna yana hira to ya yi ta fadar wannan don Allah ya girgije masa zunubain sa.

HADISI NA ASHIRIN DA HUDU Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan dayan ku ya gajiye bazai iya tarawa kansa lada dubu ba to yayi Subhanallahi sau dari sai a rubuta masa lada dubu ko a kankare masa laifuffuka guda dubu.

HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR Manzon Allah (S.A.W) ya ce hakika Allah ya zabi wasu kalmomi uku wanda ya nace musu to zai samu alkhairin duniya da lahira sune (Subhanallah, Walhamdulillah, Wallahu Akbar. Wanda ya ce Subhanallah zaa bashi lada 20 a kankare masa zunubi 20 Wanda ya ce Alhamdulillah zaa bashi lada 30 a kankare masa zunubi 30 wanda Allahu Akbar zaa bashi lada 20 a kankare masa zunubi 20.

HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA Manzon Allah (S.A.W) ya ce Bana gaya maka wani abu wanda ya fi haka alkhairi? Kace Subhanallah, Walhamdulillah, Walailaha Illallah, Wallahu Akbar, zaa dasa maka bishiya a cikin gidan Aljanna da kowace kalma da ka fada.

HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI Manzon Allah (S.A.W) ya ce Wanda ya yi ruwa da kudi bai ba dasu sadaka ba kuma ya yi rowa da dare bai tashi yayi tsayuwar dare ba, to ya lazimci wannan kalma sai ta tsaya masa a matsayin sadakar da bai yi ba da tsayuwar dare da ya kasa bai yi ba Subhanallahi Wabihamdihi ya yi ta fadar wannan sai ya zamu a bakacen kudin da bai bayar ba a bakacen daren da bai yi tsayuwa a cikin sa ba.

HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI Manzon Allah ya ce wanda zai shiga kasuwa sai ya ce Lailaha illallahu wahdahu lasharikalahu, Lahul mulku, walahul Hamdu, Yuhyi wayumitu, wahuwa hayyulla ya mutu biyadihil khairu wahuwa ala kullhi shaiin kadir. Allah zai rubuta masa lada million daya ya goge masa zunubi million daya zaa daukaka darajar sa million daya sannan zaa gina masa gida a cikin gidan Aljanna.

HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS Manzon Allah ya ce bana gaya maka abin da ya fi ambaton Allah ka da daddare da rana ba?, to kace Alhamdulillahi Adadama khalaka, Alhamdulillahi mila ma khalaka, Alhamdulillahi adada mafissamawati wama filardhi Alhamdulillahi adada ma aksa kitabuk, Walhamdulillahi ala ma akhsa kitabuk, Walhamdulillahi adada kulli shaiin, Walhamdulillahi minha kulli shaiin, kuma ka ce Subhanallahi Adada ma halaka, Subhanallahi mila ma halaka, Adada mafissamawati Wama filardi, Subhanallahi ala ma ahsa kitabuk, Subhanallahi adada kulli shaiin, Subhanallahi minha kullhi shaiin, Subhanallahi wanda ya fadi wannan wato yafi kowane irin ambaton Allah da zakayi fadin duniyar nan Inji Manzon Allah.

HADISI NA ASHIRIN DA TARA Manzon Allah (S.A.W) ya ce wanda ya min salati kafa 10 lokacin da ya wayi gari, ya yimin salati kafa 10 lokacin da ya yammatu, cetona zai riskeshi ranar Alkiyama.

HADISI NA TALATIN Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam Ya ce wanda ya ce radhitu billahi rabban Wabil Islamidinan Wabi Muhammadin Nabiyan, aljanna ta tabbata a gareshi, ba wai zata tabbata ba tariga ta tabbatar masa don haka muyi ta fadar wannan kalma don Aljanna ta tabbata a garemu.

HADISI NA TALATIN DA DAYA Mazon tsira ya na cewa wanda ya yiwa dan Uwansa kyakkyawar Adua batare da dan Uwan nasa ya sani ba Ya ce Allah ga dan Uwana wane yana da bukata iri kaza ka biya masa, ko yana cikin balai ka yaye masa ko yana cikin wata fitina ko damuwa ka dauke masa, ba tare da shi wancan dan uwan yasan kayi masa adua ba koma baka gaya masa ba. Malaika ya na nan kusa da kai sai ya ce amin walaka, kai ma Allah ya baka irin kwatan kwacin abin da ka roka wa dan uwanka. Kunga jamaa mu rinka rokawa yan uwan mu adua mai kyau saboda muma malaiku suyi mana adua mai kyau.

HADISI NA TALATIN DA BIYU Manzon Allah ya ce wanda ya kare mutun cin dan uwansa baya nan (maana ana kokarin tuzarta dan uwanka baya nan sai kayi kakagida ka kare masa mutuncin sa) to ya zama hakke ne ga Allah ya yanta ka daga wuta.

HADISI NA TALATIN DA UKU Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam ya ce wanda ya dauke abunda zai cutar da mutane a kan hanya to hakika Allah zai rubuta masa cikacciyar lada, wanda kuma Allah ya rubutawa cikakkiyar lada Allah zai shigar dashi a Aljanna.

ALLAH YA TAIMAKE MU Masoyin ku Mai neman Rahamar Ubangiji
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 03:37:39 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"FALALA MAI YAWA DAGA HADISAN ANNABI MUHAMMAD SAW" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: