Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc
[ Harkokin DuniyarMusulmi DaAddiniMusulunc ]

·Musulmi da farfagandar makiya
·Abin da za mu yi Allah Ya so mu (2)
·Abin da za mu yiAllah Ya so mu (1)
·Giba da illolinta (1)
·Yadda Musulunci ya 'yanta mace (5)
·Yadda Musulunci ya 'yanta mace (4)
·Tukuici ga mai azumi (4)
·Tukuici ga mai azumi (3)
·Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


BINCIKEN MALAMAN KIMIYYA KAN TSIBIRIN BAMUDA (1)
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen DAGA JARIDAR AMINIYA

Binciken malaman Kimiyya kan tsibirin Bamuda (1)

Category: Kimiyya da fasaha Published on Friday, 27 June 2014 01:00 Written by Maimaici Mai Fa'ida Hits:

3007 Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan alheri a gare ka.

Don Allah idan zai yiwu ka maimaita mana kasidar ''Tsibirin Bamuda'' mana. Lokacin da na fara karanta jaridar Aminiya ka riga ka gabatar da kasidar, kuma ni ba ni da adireshin Imel balle in ce a turo mini. Kuma na lura lallai babu kasidar da ta kai wannan kasida ta Tsibirin Bamuda farin jini. Da fatan za ka taimaka, idan babu damuwa. Allah Ya kara basira, amin. – Ummu Haidar, Gombe Wa alaikumus salam, Maman Haidar barka da warhaka. Lallai kamar yadda kika fada, wannan kasida mai take: ''Binciken Malaman Kimiyya kan Tsibirin Bamuda (Bermuda Triangle),'' ta shahara sosai, nesa ba kusa ba.

Ni kaina ban san sau nawa na aika wa masu karatu ba, a bisa bukatarsu. kasida ce da na rubuta tun shekarar 2007; shekaru kusan bakwai kenan a halin yanzu. Amma ko cikin makon da ya gabata akwai wadanda suka bukaci in tura musu, kuma na tura. Sannan akwai masu karatu irinki, marasa adireshi ko akwatin Imel, kuma masu sha'awar ace sun kara karanta wannan kasida a karo na biyu ko ma farko. Ganin sakonki ne ya kara mini kaimi wajen kara yin nazari kan kasidar, da gyara wasu kalmomi don kara musu amo da tsari a ka'idojin rubutu, duk da cewa babu wani abu sabo da ya sake aukuwa na mamaki a wannan tsibiri tsakanin bayyanar kasidar a karon farko zuwa yanzu. Da fatan wadanda ba su samu karanta kasidar ba a karon farko za su amfana. Allah sa mu dace, amin.

Mabudin Kunnuwa Duk da cewa akwai bigirorin duniya da dama da abubuwan mamaki ke faruwa a cikinsu ba tare da dan adam ya fahimci musabbabansu ba, Tsibirin Bamuda (Bermuda Island ko Bermuda Triangle) ne kadai ya fi shahara a bakunan mutane sanadiyyar haka.

Wannan shahara ta samo asali ne daga nahiyar Kudancin Amurka (South America), a hankali labarin ya ci gaba da yaduwa zuwa sauran kasashen duniya.

Manyan ababen mamakin da ake ikirarin suna faruwa a muhallin tekun da wannan tsibiri yake sun hada da bacewar jiragen sama – masu dauke da fasinjoji 'yan kasuwa ko na soji – da jiragen ruwa – manya da kanana da na shawagi. Idan suka bace a galibin lokuta, ba a ganin buraguzan jirgin balle a kaddamar da bincike kan dalilan da suka haddasa faruwar hadarin. Wannan al'amari abin al'ajabi, a cewar masu bayar da labarai, bai tsaya a bacewar jirage ba tare da ganin buraguzansu kadai ba, har da wasu labarai masu caza kwakwalwa kan irin yanayin da tekun ke kasancewa na launi da kuma sulmuya a wasu lokutan, ko kuma wasu irin dabi'u da ake ikirarin gira-gizan da ke saman tekun ke shiga, a yayin aukuwar hadarurrukan da suka fara faruwa shekaru kusan dari biyu da suka gabata. Ire-iren wadannan labarai sun samo asali ne daga irin jawaban da masu lura da na'urar filin saukan jiragen sama da ke tsibirin ke bayarwa. Ko wadanda ake tarawa wajen binciken da hukumomin gwamnatin Amurka da ke lura da ire-iren wadannan hadarurruka ke yi. Da wannan, marubuta suka sa wa wannan muhalli suna: The Bermuda Triangle (Kusurwar Bamuda), ko kuma The Debil's Triangle (Kusurwar Shedan).

A halin yanzu da dama cikin wadanda suka taba jin labarin wannan bigire na Bamuda, sun yarda cewa wani wuri ne mai cike da almara, kamar yadda galibin turawa masu bincike suka fada. Da kuma cewa babu wanda ya san abin da ke haddasa wannan al'amari, sai Allah (ga wadanda suka yarda da Allah kenan), ko kuma dabi'a ta shu'umcin wurin. Wasu suka ce aljanu ne a wurin. Wasu suka ce akwai wasu halittu ne na musamman da a harshen Turanci ake kira Aliens, masu haddasa hakan. Wasu suka ce a a, irin yanayin wurin ne kawai. Da dai sauran ra'ayoyi masu kama da haka. Shin, meye gaskiyar wadannan zace-zace da ake ta yi kan wannan tsibiri? Wani irin bincike aka yi wajen gano hakan? Jiragen ruwa da na sama guda nawa suka bace a wannan mahalli? Rayuka nawa suka salwanta? Wa da wa suka yi rubuce- rubuce kan haka cikin Malam Kimiyya da masu sha'awar rubutu kan al'amuran mamaki a duniya? Meye ra'ayin nazarin da Malaman Kimiyya suka yi kan dalilin faruwar wadannan abubuwan mamaki? Shin, wai ma tukun, a duniya akwai wasu wurare ne masu irin wannan dabi'a, ko dai tsibirin Bamuda ne kadai? In eh akwai, to me ya sa na tsibirin Bamuda ya sha bamban, ya shahara fiye da sauran a duniya? Wadannan, da ma wasu tambayoyi, za mu samu amsoshinsu cikin makonni masu zuwa in Allah Ya yarda.

A Ina Tsibirin Yake?

Kafin mu yi nisa, asalin tsibirin Bamuda, watau Bermuda Islands, yana gab da tsakiyar tekun Atlantika ne, Arewa da Jihar Fulorida da ke Amurka. Kuma duk da cewa ana danganta wannan wuri ko kusurwa da tsibirin Bamuda, sai dai ba a wannan tsibiri kadai wannan kusurwa yake ba. Kusurwar Bamuda wani wuri ne da ya hada manyan gabar tekunan kasashe guda uku da ke nahiyar Arewaci da kuma kudancin Amurka. Kusurwar farko ta faro ne daga gabar Fulorida ta kasar Amurka, ta zarce zuwa gabar babban tsibirin Puerto Rico da ke yamma maso-kudu da gabar Fulorida. Daga tsibirin Puerto Rico kuma kusurwar ta cilla Arewa, inda ta tike a gabar tsibirin Bamuda da ke kusa da tsakiyar tekun Atlantika.

Wannan wuri ko mahalllin teku da ke tsakanin wadannan gabobi guda uku, shi ake kira The Bermuda Triangle, ko The Debil's Triangle.

An danganta wannan kusurwa da tsibirin Bamuda ne saboda a nan ya tike, kuma galibin ababen hawa kamar su jiragen sama da na ruwa wadanda ake amfani da su wajen kasuwanci da shawagi da atisayen soji a wannan nahiya, duk a can suke tikewa kafin su komo inda suka taso. Ko kuma daga can suke wucewa zuwa wasu nahiyoyin, irin su Turai da Arewacin Amurka da kasashen Asiya.

Wannan kusurwa ta Bamuda ita ce bigiren da jiragen sama da na ruwa ke shawagi fiye da kowane wuri a duniya. An kiyasta cewa akalla akan samu sawun jiragen sama daga wannan nahiya zuwa kasashen turai da sauran nahiyoyi, sama da dubu hamsin a shekara. Bayan haka, akwai jiragen ruwa da na kasuwanci da na shawagi ko yawon bude ido, da kuma jiragen saman atisayen soji da Hukumar Sojin Amurka ke turawa suna shawagi, watau kai- komo don yin atisaye.

Har wa yau akwai masu shawagi da kananan kwale-kwalen shakatawa wadanda a harshen turanci ake kira Pleasure Boats, da kuma jiragen ruwan tsere da ake kira Yatchers. Bayan haka, akwai filayen saukan jiragen sama a dukkan kusurwoyin nan uku, tare da tashar jiragen ruwa masu karban manya da kananan jiragen da ke shawagi a wannan wuri. Sannan kuma sai miliyoyin masu zuwa yawon bude ido daga sauran kasashen duniya, musamman ma Amurka da Turai. A takaice dai, wannan wuri rayayyen wuri ne da sawun jirgin ruwa da na sama da na masu ziyara ba su daukewa; daga shekara zuwa shekara.

Zai dace mai karatu ya rike wannan karatu kan yawan zirga-zirgar da ake yi a wannan wuri, domin zai taimaka masa wajen karba ko rashin karbar dalilan da wasu marubuta suka bayar wajen yanke hukuncinsu na karshe.

Yaushe Abin Ya Fara?

Wannan kusurwa da ake wa take da ''Kusurwar Shedan'' – ko Debil's Triangle – ya fara cin jiragen sama da na ruwa ne shekaru kusan dari biyu da suka gabata, duk da cewa ba a fara fahimtar hakan ba sai wajen shekaru casa'in zuwa dari da suka wuce. Daga nan ne aka fara danganta hadarurrukan da suka gabata da wannan yanayi mai ban mamaki. Kamar yadda bayanai suka gabata, wannan kusurwa ta Bamuda ta yi kaurin suna ne wajen hadararruka masu ban mamaki, inda bayan hadarin ake rasa abin da ya haddasa shi, ko kuma a ma kasa samun buraguzai ko gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu da ma na jirgin gaba daya.

A wasu lokuta a kan samu sakon neman agaji daga direbobin jiragen sama cewa suna ganin wasu abubuwa masu ban tsoro ko firgitarwa. Kafin a mayar da jawabin ceto garesu, sai kawai a nemi hanyar sadarwa a rasa. Wani kuma zai bugo ne cewa ba ya ganin gabansa, bayan kuma a na'urar lura da yanayin sararin samaniya babu wata matsala da na'urar ke hangowa: babu yanayin hazo mai firgitarwa, babu ruwan sama, babu alamar mahaukaciyar guguwa mai yi wa jiragen ruwa dibar karan mahaukaciya, amma sai kawai a ji hanyar sadarwar ta yanke.

Mafi shahara daga cikin abubuwan mamaki da suka faru a wannan kusurwa shi ne hadarin tawagan jiragen kai hari da darkake abokan gaba na kasar Amurka masu suna Flight 19, wadanda hukumar sojin sama na kasar Amurka ta aika don yin shawagi a wannan kusurwa cikin shekarar 1945. Duk da cewa ana lura da tafiyar wannan tawaga na jirage ta hanyar na'ura hangen nesa sadda suka baro cikin kasar Amurka, sai dai cikin lokaci guda kawai sai aka neme su aka rasa.

Da aka nemi sadarwa da shugaban tawagar, sai ya ce: ''A yanzu muna shiga wani irin farin ruwa ne....al'amura sun fara lalacewa.

Bamu san inda muke ba a halin yanzu....ruwan kore ne....a a, fari ne!'', sai sadarwa ta yanke a tsakanin masu lura da na'urar da wannan shugaban tawaga.

Bayan faruwar wannan lamari, an yi ta bincike cikin teku ba a samu buraguzan wadannan jirage ba balle wadanda suke ciki. Babu wanda ke da wani bayani gamsasshe kan abin da ya haddasa wannan hadari har zuwa yau, balle bayani kan hakikanin wurin da abin ya auku. A lokacin da aka tura wata tawaga ta manema jirage, da suka isa wurin da na'urar ta sanar da faduwarsu, babu abin da aka gani a wurin.

Daga nan aka ci gaba da samun ire-iren wadannan hadarurruka masu ban mamaki da al'ajabi. Wasu a kan samu bayanai kan batansu, bayan tsawon lokaci; wasu kuma ko alama ba a samu, sai dai kawai a hakura.

Chelsea ta kori Jose Mourinho ....Real Madrid za ta dibar wa Rafa Benitez wa'adi Man. United da Manchester City sun kebe Naira biliyan 348 don sayo Messi da Neymar Za a sayar da kulob din FC Giwa A watan gobe za a fara gasar Firimiya ta Najeriya NFF ta yi wa 'yan wasan U-23 ruwan Naira Madrid ta fara zawarcin Mesut Ozil CAF za ta karrama Osimhen, Nwakali da Amunike A Abuja Gwamnan Neja ya kalubalanci kungiyar kwallon Gora ta Niger Flickers Ya tuka keke daga Indiya zuwa Sweden saboda soyayya Yana fuskatar daurin shekara 37 kan zagin karen sarki bayyade mu'amalar kafafen sadarwar zamani a basashen duniya (I)
Matakan Sulhunta Ma'aurata Mawaka sun nuna rashin gamsuwa da kalankuwar Kaduna Dokokin fim sun raba kan hukuma da 'yan fim din Hausa
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 04:03:15 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"BINCIKEN MALAMAN KIMIYYA KAN TSIBIRIN BAMUDA (1)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: