Muhawara Hausa
 



DANDALIN AHLULBAITI DA SAHABBAI
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi DANDALIN AHLULBAITI DA SAHABBAI

ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻌﻪ ﺃﺷﺪﺍﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﺭﺣﻤﺎﺀ ﺑﻴﻨﻬﻢ

AIWATAR DA SHARI'AR MUSULUNCHI A NIGERIA: NASARORI DA MATSALOLI SHIMFIDA Abu ne sananne a wajen manazarta tarihi cewa, babu wani lokaci da yan Adam suka sami rayuwa nagartacciya wadda take cike da farin ciki da Jin dadi tare kuma da walwala da samun ci gaba a cikin aminci da kwanciyar hankali ga samuwar 'yanci da adalci hade da kaunatayya a tsakanin mutane kamar lokutan da aka dabbaka Shari'ar Musulunci.

Kasancewar shariar Musulunci ita ce jigo a wajen gyara Rayuwar Dan Adam ya sanya Allah madaukakin sarki ya ba ta cikakken muhimmanci da kulawa a cikin littafinsa Mai albarka. Idan muka duba a cikin Alkurani zamu ga zancen aiwatar da Shari'a a cikin surori sama da guda 50, kuma ayoyin da suka yi wannan maganar sun zarce aya 200.

Aiwatar da Sharia ga musulmi ba zabi ba ne, tilas ne. Domin kuwa Allah mahaliccinmu shi kadai yake da ikon ya zartar da hukunci ga Rayuwar bayinsa, kamar yadda ya ce:

(( ﺍﻥ ﺍﻟﺤﻜﻢ ﺍﻻ ﻟﻠﻪ ﺍﻣﺮ ﺍﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺍ ﺍﻻ ﺍﻳﺎﻩ، ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻛﺜﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻻ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ( ( ﻳﻮﺳﻒ ٤٠ :

A wani wurin kuma Allah mabuwayi ya ce:

(( ﺍﻡ ﻟﻬﻢ ﺷﺮﻛﺎﺀ ﺷﺮﻋﻮﺍ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﺄﺫﻥ ﺑﻪ ﺍﻟﻠﻪ ( ( ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ ٢١ :

Saboda haka, duk musulmin da ya yi kalmar shahadaya zama tilas ya karbi Shari'ar Allah a matsayin doka wadda ba zai tsallaka ba.

Allah madaukaki ya zargi masu bin duk wani tsari da ba nasa ba, kuma ya nassanta cewa yin haka shine jahiliyyah.

(( ﺍﻟﺤﻜﻢ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ ﻳﺒﻐﻮﻥ ﻭﻣﻦ ﺍﺣﺴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻜﻤﺎ ﻟﻘﻮﻡ ﻳﻮﻗﻨﻮﻥ ( ( ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ ٥٠ :

Allah Tabaraka Wa Ta'ala bai nemi kawai mu sanya dokokinsa da suka zo ta hannun Manzo a matsayin abin aiwatarwa ba har sai ya kasance ba mu da 'dar-'dar a cikin zukata game da duk hukuncin da aka yanke. Ga abinda Allah ya ce Wa manzonsa:

(( ﻓﻼ ﻭﺭﺑﻚ ﻻ ﻳﺆﻣﻨﻮﻥ ﺣﺘﻰ ﻳﺤﻜﻤﻮﻙ ﻓﻴﻤﺎ ﺷﺠﺮ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺛﻢ ﻻ ﻳﺠﺪﻭﺍ ﻓﻲ ﺍﻧﻔﺴﻬﻢ ﺣﺮﺟﺎ ﻣﻤﺎ ﻗﻀﻴﺖ ﻭﻳﺴﻠﻤﻮﻥ ﺗﺴﻠﻴﻤﺎ ( ( ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ٦٥ :

Hukuncin da Alkurani ya yanke karara ga wadanda suka kauce ma Shari'a suka zabi wani tsari daban shi ne:

(( ﻭﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺤﻜﻢ ﺑﻤﺎ ﺍﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺄﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ﺍﻟﻜﺎﻓﺮﻭﻥ ( ( ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ ٤٤ :

Mu yi nazarin wadannan ayoyin har wayau:

(( ﻭﻟﻘﺪ ﺍﺗﻴﻨﺎ ﺑﻨﻲ ﺍﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻢ ﻭﺍﻟﻨﺒﻮﺓ ﻭﺭﺯﻗﻨﺎﻫﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﻴﺒﺎﺕ ﻭﻓﻀﻠﻨﺎﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ *
ﻭﺃﺗﻴﻨﺎﻫﻢ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺮ ﻓﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﺍﻻ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺟﺎﺀﻫﻢ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﻐﻴﺎ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺍﻥ ﺭﺑﻚ ﻳﻘﻀﻲ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻓﻴﻪ ﻳﺨﺘﻠﻔﻮﻥ * ﺛﻢ ﺟﻌﻠﻨﺎﻙ ﻋﻠﻰ ﺷﺮﻳﻌﺔ ﻣﻦ ﺍﻻﻣﺮ ﻓﺎﺗﺒﻌﻬﺎ ﻭﻻ ﺗﺘﺒﻊ ﺍﻫﻮﺍﺀ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻻ ﻳﺆﻣﻨﻮﻥ * ﺍﻧﻬﻢ ﻟﻦ ﻳﻐﻨﻮﺍ ﻋﻨﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺷﻴﺌﺎ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺍﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﺾ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻲ ﺍﻟﻤﺘﻘﻴﻦ *
ﻫﺬﺍ ﺑﺼﺎﺋﺮ ﻟﻠﻨﺎﺱ ﻭﻫﺪﻯ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﻟﻘﻮﻡ ﻳﻮﻗﻨﻮﻥ ( ( ﺍﻟﺠﺎﺛﻴﺔ٢٠-١٦ :

GABATARWA Yau muna a shekara ta 12 kenan da wannan sabon yunkuri na aiwatar da Shari'a a wasu jihohin da ke arewacin Najeriya. Babu shakka wannan bita da ma ita kanta wannan Mukala sun zo daidai Lokacin da ya dace a yi su domin mu auna nasarori da matsalolin da muka samu mu gano hanyar da zamu ci gaba.

To, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata mu soma gabatar da su kafin bayanin nasarori da matsalolin wannan tafiya mai albarka.

1. Ma'anar Shari'a:

Da yawan mutane sun dauka cewa Shari'a tana nufin yanke hukunci na ukuba a kan masu laifi. Wannan kuwa takaitawa ne da takurawa ga ma'anar Shari'a. Domin kuwa Shari'a ta hada duk wani tanadin da musulunci ya yi ma dan Adam ta fuskar yadda zai yi alaka da ubangijinsa da yadda zai yi hulda da mutane masoya da makiya.

Don haka ta kunshi Ibada da zamantakewa tsakanin jama'a da sha'anin tattalin arziki da siyasa da kome na rayuwa.

2. Manufofin Shari'a:

Jigon manufofin Shari'a shi ne samar da Jin dadi ga dan Adam a duniya da lahira.

Wannan kuwa ba zai yiwu ba sai an kiyaye masa addini da zai lamunce masa nagartacciyar rayuwa, an ba rayuwarsa da hankalinsa da mutuncinsa da dukiyarsa kariya. Binciken 'kwa'kwaf ya nuna cewa duk wata doka ta Shari'ar Musulunci ba ta fita daga manufofi.

3. Fifikon Shari'ar Musulunci a kan Sauran Tsare tsare Shari'a ba kamar sauran tsare tsaren da yan Adam suka yi wa kansu ba, ita tsarin Allah ce mahaliccinmu wanda ya san kome fai da boye. Don haka:

– Ba zai yiwu ka samu Kure ko kasawa ko jahilci ko zalunci ba a cikin ta.

– Tana daidai da kowane yanayi, da ko wace al'umma, a kowane lokaci ﴿ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎﻙَ ﺇِﻻَّ ﻛَﺎﻓَّﺔً ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﺑَﺸِﻴﺮًﺍ ﻭَﻧَﺬِﻳﺮًﺍ ﻭَﻟَﻜِﻦَّ ﺃَﻛْﺜَﺮَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻻَ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ﴾ ]ﺳﻮﺭﺓ ﺳﺒﺄ، ﺍﻵﻳﺔ 28 ].

﴿ ﻗُﻞْ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﺇِﻧِّﻲ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻴْﻜُﻢْ ﺟَﻤِﻴﻌًﺎ.... ﴾ ]ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ، ﻟﻶﻳﺔ 158 ].

﴿ ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎﻙَ ﺇِﻻَّ ﺭَﺣْﻤَﺔً ﻟِﻠْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ﴾ ]ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ، ﺍﻵﻳﺔ 107 ].

﴿ﺗَﺒَﺎﺭَﻙَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﺰَّﻝَ ﺍﻟْﻔُﺮْﻗَﺎﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﻋَﺒْﺪِﻩِ ﻟِﻴَﻜُﻮﻥَ ﻟِﻠْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ ﻧَﺬِﻳﺮًﺍ﴾ ]ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ، ﺍﻵﻳﺔ 1 ].

ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ) ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺒﻌﺚ ﺇﻟﻰ ﻗﻮﻣﻪ ﺧﺎﺻﺔ ﻭﺑﻌﺜﺖ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﺎﻣﺔ).

– Ba zaka samu nakasu ta fuskar an kula da wani sashe a manta wani ba. Don haka ita ba ta bukatar irin constitutional conference da ake Wa tsare tsaren yan Adam akai akai don a shigar da abinda aka manta ko a gyara abinda aka yi kuskure ko a riski wani sabon kalubale.

4. Wajabcin aiwatar da Shari'a baki daya Shari'ar musulunci tsari ne kammalalle da idan aka yi aiki da wani bangare nasa shi kadai ba tare wasu bangaroran ba ba za a samu cikakkiyar nasarar da ake so ba. Alal misali, Shari'ar musulunci ba ta yin doka a kan wani laifi har sai ta samar da dukan garkuwar da mutane ke bukata wadda zata hana su aukawa a cikin wannan laifi.

Akasarin wadanda suke yin sata ga misali ko dai talauci ne yake kai su ko handama da kwadayi ko kuma an zalunce su ne suka kasa kai ga hakkinsu don haka suka auka cikin na wasu mutane. Shari'ar musulunci duk ta magance wadannan matsaloli ta hanyar Zakka da Sadaka da karfafa yin taimako da umurni da yin adalci da gyara dabi'un mutane har su bar sha'awar abinda ba nasu ba.

Haka ita ma Zina, kafin a yanke hukunci a kan mai yin ta sai da aka haramta ko da kusantar ta; aka hana cudanyar maza da mata ko kebantar namiji da mace wadda ba muharramarsa ba ko yin tsiraici da rangwada a wurin tafiya da kashe murya ga mata da makamantansu. Bayan haka kuma sai aka tanadi hanyoyin sawwake aure da na samun abin yi. Duk da haka kuma sai aka tsananta sharudan tabbatuwar ta ta yadda wanda yake son bayyana alfasha a fili ne kawai ake iya saurin kamawa.

5. Aiwatar da Shari'a ba alhaki ne kawai a kan masu mulki da masu ilimi ba. Wajibi ne a kan kowane musulmi ya duba ta wace fuska yake iya bada tasa gudumawa. Kuma nauyin da ke kan kowane musulmi a wajen aiwatar da Shari'a ya dogara ne ga iya ikon da yake da shi. Amma musulmi mafi rauni shine ake bukatar ya bayyana son sa da goyon bayansa ga Shari'a fai da boye.

Allah Tabaraka Wa Ta'ala ya zargi wasu a kan kin ba Shari'a goyon baya, sune munafukai. Kuma ya rusa aikinsu a kan haka.

(( ﺍﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺭﺗﺪﻭﺍ ﻋﻠﻰ ﺃﺩﺑﺎﺭﻫﻢ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺗﺒﻴﻦ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﺳﻮﻝ ﻟﻬﻢ ﻭﺃﻣﻠﻰ ﻟﻬﻢ * ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻧﻬﻢ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﻛﺮﻫﻮﺍ ﻣﺎ ﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﻨﻄﻴﻌﻜﻢ ﻓﻲ ﺑﻌﺾ ﺍﻻﻣﺮ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻳﻌﻠﻢ ﺍﺳﺮﺍﺭﻫﻢ * ﻓﻜﻴﻒ ﺍﺫﺍ ﺗﻮﻓﺘﻬﻢ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻳﻀﺮﺑﻮﻥ ﻭﺟﻮﻫﻬﻢ ﻭﺍﺩﺑﺎﺭﻫﻢ * ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻧﻬﻢ ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻣﺎ ﺍﺳﺨﻂ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻛﺮﻫﻮﺍ ﺭﺿﻮﺍﻧﻪ ﻓﺄﺣﺒﻂ ﺍﻋﻤﺎﻟﻬﻢ * ﺍﻡ ﺣﺴﺐ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﻲ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ ﻣﺮﺽ ﺍﻟﻦ ﻳﺨﺮﺝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺿﻐﺎﻧﻬﻢ؟ ﻭﻟﻮ ﻧﺸﺎﺀ ﻻﺭﻳﻨﺎﻛﻬﻢ ﻓﻠﻌﺮﻓﺘﻬﻢ ﺑﺴﻴﻤﺎﻫﻢ ﻭﻟﺘﻌﺮﻓﻨﻬﻢ ﻓﻲ ﻟﺤﻦ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻳﻌﻠﻢ ﺍﻋﻤﺎﻟﻜﻢ ( ( ﻣﺤﻤﺪ٣٠-٢٥ :

Ya aka yi maganar Shari'a ta taso?

Muna iya cewa aiwatar da Shari'a a wannan marra ci gaba ne da aikin da magabatanmu jagororin addini da malamai na wannan kasa suka soma tun lokaci mai tsawo. Babu shakka anyi malamai masana masu kokarin tabbatar da kafuwar addini da yada shi tun kafin zuwan mujaddidi Usmanu Danfodiyo a wannan kasa. Alal misali akwai irin su Malam Abdullahi bakatsine mawallafin ADIYYATUL MU'UDI da Malam Muhammadu dan Masani mawallafin ALBUZUGUS SHAMSIYYAH sharhin Ashmawi wanda almajiri ne ga fitaccen malamin nan bakatsine Malam Muhammadu dan Marina. Akwai kuma irin su Malamin Hadisin nan na kasar Hausa; Malam Haruna Zazzau da Malam Umar Dan Muhammad At Torodi da Malam Jibril dan Muhammad wanda Sheikh Usman Danfodiyo yake bugun gaba da shi. A wannan zamanin dai har wayau akwai malamai irin su Malam Kabara daga cikin jikokin Ahmad Baba Tumbuktu da alkalin Kano Malam Muhammad bin Abdilkarim Al Magili dan asalin Tilmisan da ire irensu wadanda kirge su yana da wuya.

Malam Magili shine wanda ya rubuta ma sarkin Kano Muhammadu Rumfa wani muhimmin littafi a kan siyasar musulunci da tsarin gudanar da mulki wanda shine irinsa na farko a wannan kasa. Kuma Abdullahi Danfodiyo na yawan cirato maganganunsa a cikin DIYA'UT TA'AWIL da sauran rubuce rubucensa.

To, sai kuma bayyanar mujaddidi Shehu da almajiransa wadanda suka kawo sauyi mai girma kuma mai albarka a wannan kasa.

suka dawo da martabar Shari'a kuma Allah ya taimake su da mulki suka dabbaka ta.

Almajiran Shehu sun zo daga wurare daban daban irin su Malam Sulaiman daga Kano da Malam Musa daga Zariya da Malam Yakubu daga Bauchi da Modibbo Buba Yero daga Gombe da Malam Ibrahim Zaki daga Katagum da Malam Sambo Digimsa daga Hadejia da sauran su. Kai har mata a wancan lokaci ba a bar su a baya ba wajen yada addini irin su Khadijah da Maryam da Asma'u da Fatima 'ya'yan Shehu da Malama Aisha 'yar Malam Kabara wacce take gabatar da tafsirin Alkur'ani a fadar sarkin Kano da dai sauran su.

Wannan shimfida ta tarihi ta gabata ne don mu san cewa sha'anin addinin musulunci da kafuwar Shari'a a kasar nan ba sabon abu ba ne.

Sai kuma abinda ya biyo bayan kafuwar daular. An samu rahoton bayyanar matsaloli da dama wajen aiwatarwa. Amma kuma dai Shari'ar musulunci ita ce kadai dokar da aka amince da ita. Amma bayan zuwan turawa a kasar nan da kama madafan iko da suka yi sai suka yi iya kokarinsu domin su canja sha'anin Shari'a amma sai suka lura da yadda Shari'a take a cikin jini da tsoka ga jama'a. Don haka sai suka kafa kotuna da zasu aiwatar da hukunce hukuncen Shari'a a iya inda suka amince suke ganin bai ci karo da hankulansu ba wato abinda ake kira Al Ahwalus Shaksiyyah.

Sai kuma tasirin da turawa suka bari kafin su tafi a cikin al'adunmu da tunaninmu.

Wannan wani abu ne da magana a kan sa zata tsawaita wajen gano yadda suka nisanta mu daga Shari'ah.

Shari'ar musulunci kenan ba bakuwa ba ce a kasar nan. Kuma cikin hikimar Allah sai aiwatar da Shari'a da koma ma tsarin musulunci a wannan karni ya zo ta inda ba a tsammani. A daidai Lokacin da kasar nan take tafiya a kan tsarin dimukradiyya.

Sannan ya zo cikin ruwan sanyi da lumana a matsayin wata bukata ta al'umma. Wannan sai ya bamu darussa masu dinbin yawa.

Daga cikin su:

1. Karfin tasirin addini a cikin zukatan mutane la'akari da irin goyon baya da karbuwar da Shari'a ta samu.

2. Yiwuwar aiwatar da Shari'a a karkashin tsarin dimukradiyya kafin samuwar cikakken tsarin musulunci wanda zai tabbata ga baki dayansa cikin yardar Allah a nan gaba. A nan sai mu tuna da yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yarda da zama memba a cikin kwamitin da aka Kira HILFUL FUDUL a zamanin jahiliyyah tare da kasancewar sa ya kaurace ma dukan al'amurran jahiliyyah, amma shi wannan tunda ya dace da manufofin rayuwarsa sai ya shiga aka yi da shi.

3. Kuma ya nuna mana cewa, abinda bai samu gaba daya ba babu laifi idan an fara yin sashensa kamar yadda Najjashi sarkin Habasha ya musulunta a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam amma bai iya bayyana musuluncinsa a fili ba balantana zancen aiwatar da shi a kan talakawansa amma kuma duk da haka ya ci gaba da Taimakon musulunci ta wasu fuskoki da yake iyawa.

4. Har wayau aiwatar da Shari'a ya bamu darasi babba shine cewa, duk Lokacin da al'umma take da kuduri da cikakkaiyar azama ta kawo gyara to, abu ne mai yiwu idan an nemi Taimakon Allah.

NASARORIN AIWATAR DA SHARI'A 1. Haduwar kan musulmi da aka samu na wani dan lokaci wanda duk da yake bai dore ba amma ya bar tasiri mai yawa.

Darasin da ke cikin wannan shine cewa, a duk Lokacin da akwai kalubale a gaban musulmi akwai yiwuwar su hadu su samar da wata manufa hadaddiya kamar irin halin da muke ciki a yau.

2. An samar wa Shari'a wani gurbi a doka wanda zai hana tsangwama ga duk wata doka ta musulunci da za a aiwatar.

3. Samar da hukumomin aiwatarwa (Hisba, Anti corruption, gyara kayanka, a daidaita sahu, min. 4 religious affairs) wadanda a da ba a tunanin zasu iya kafuwa.

4. Alakanta hukuma da addini. A can baya abu ne da ake tsoro. Amma a yau kowace gwamnati na iya fitowa karara ta yi abu saboda musulunci koda kuma har ta yi alfahari yin hakan.

5. Raguwar Ayyukan barna a wasu jihohi ta yadda har alkaluman kididdiga ta nuna raguwar cututtuka a jihohin da aka aiwatar da Shari'a saboda reguwar Ayyukan assha a cikin su.

6. Karuwar ilimi da fahimtar jama'a a kan Sharia. Domin kuwa an yi nazarce nazarce da wallafe wallafe da dama, an gabatar da karatuttuka da muhadarori da wa'azoji da darussa masu dinbin yawa a kan wannan.

MATSALOLIN DA AKA CI KARO DA SU Shari'a ta gamu da tarnaki da samun cikas daga bangarori dama wadanda suka hada da makiya na ciki da na waje. Ta yadda aka mayar da ita wani mataki na bayyana a dawa da musulunci da dokokinsa. Alal misali, wace bajinta ce Safiya ta yi wadda ta sa aka mayar da ita a wancan lokaci a cikin kanun Labarin duniya na dukan manyan tashoshin duniya?

An yi ta sukar Shari'ar musulunci da cewa kauyanci ce, ba ta dace da zamani ba, akwai rashin tausayi a ciki da sauransu.

Gaskiyar magana ita ce ko don matsalar tattalin arziki bai kamata muyi tsammanin kasashen yamma su kyale mu mu aiwatar da Shari'a salun alun ba. Domin kuwa duk arzikin duniya yana shimfide ne a kasashen musulmi. Idan muka aiwatar da Shari'a bayan bunkasar arziki da zamu samu to, su fa zamu yanke da tattalin arzikinsu Wanda ya dogara a kan RIBA. Sannan zamu zama masu hankalin da yawo da hankalinmu da suke yi ba zai yiwu ba.

2. Akwai kuma tarnaki na constitution shi kansa da wasu sake-saken layi da karara suke cin karo da Shari'a.

3. Wasu masu son zuciya sun so suyi amfani da wannan su zafafa rikon da ke akwai a tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya. Sai aka nuna masu cewa yin Shari'a na sa a shiga cikin hakkinsu. Abinda ya biyo bayan kuma duka mun sani.

4. Akwai matsalar tsaro ga ita Shari'a din kanta. Jami'an tsaro na kasa duka mallakar gwamnatin tarayya ne. Ba 'yan sanda ga jihohi. Amma duk da haka, samar da hukumar Hisba na daga cikin abinda yake rage kaifin wannan matsala.

5. Rashin Isasshen tanadi don dorewa da ci gaba da aiwatar da Shari'a. Muna a zamani na wayewa da fadadar sha'anin kimiyya da fasaha. Ya kamata sha'anin aiwatar da Shari'a ya ci moriyar wannan ci gaban da Allah ya kawo. Amma sai ka ga ana amfani da hanyoyin tuka-tuka (sunan wani famfo tsohon yayi) wajen lamurran da suka shafi Shari'a. Wannan ba zai rasa dangantaka da cewa wasu mahukunta Shari'ar ta zame masu dole ba amma ba don tana cikin ajandarsu ba da kuma abinda zamu kawo a nan gaba na rashin cancantar wasu jami'an gudanarwa.

6. Takaita aikin Shari'a ga wasu hukumomi na musamman. Misali zaka taras da cewa, hukumomin aiwatar da Shari'a a kowace jiha irin su ma'aikatar la irfan addini, Hukumar Zakka, Hukumar Hisba da sauransu suna aiwatar da Shari'a, amma idan ka je ma'aikatar lafiya ko ta ilimi ko aikin gona ba zaka ga aiwatuwar Shari'a ba.

7. Rashin shugabantar da wadanda suka cancanta kuma suke da kwarewa a wasu daga cikin hukumomin aiwatar da Shari'a.

Wannan ya kawo rashin samun ci gaba a wasu jihohi musamman inda na ba wa al'amarin muhimmanci, an ba da kudi, an ba su iko amma ba a saka wadanda suka dace kuma suke iyawa ba.

8. Wasu na ci da Shari'a. Wannan ya jawo zubewar martabar wasu malamai da aka dora ma alhakin aiwatarwa.

Shawarwari:

1. Dole ne a dauki matakan wadatar da jama'a da kula da inganta rayuwarsu. Yin wannan shi ma Shari'a ne. Kuma shine abinda zai taimaka ainun wajen yakar wasu miyagun dabi'u da hukumomin aiwatar da Shari'a suka dukufa a kai.

2. Lalle ne a sanya zancen aiwatar da Shari'a a dukkan ma'aikatu da wurare na gwamnati da wadanda ma ba na gwamnatin ba. A inganta shiraruwan gyara Tarbiyya irin su A DAIDAITA SAHU da makamantansu.

3. A samar da hukumomi masu karfi da kuma kwararrun manazarta wadanda zasu rinka bincike da wallafa bayanai a kan hanyoyi bunkasa Shari'a.

4. A kara inganta matakan ilmantarwa irin wannan bita, a shirye tafiye tafiye zuwa kasashen da suka yi nisa wajen zartar da dokokin musulunci domin amfani da nasu dabaru da hanyoyi ci gaba.

5. A samar da ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin hukumomin da ke aiwatar da Shari'a na jihohi daban daban.

6. A tabbatar da an shugabantar da wadanda suka dace kuma suke himma ga duk hukumomin da ke da alaka da aiwatar da Shari'a.

7. Hukumar Hisba: A inganta ta sosai, a samar da horarwa isasshiya ga ma'aikatanta, a basu hurumi Mai karfi wajen yakar fitsara da shashanci a tsakanin al'umma.

8. Hukumar Hisba ta sanya hikima wajen gudanar da lamurranta. Ta fuskanci ilmantarwa da nasiha ga jama'a fiye da daukar matakin hukuntawa. Ta kuma bi abubuwa daki daki tana la'akari da yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya bi mutane a hankali har suka mika wuya. Sannan ta bude kofofinta don karbar shawarwari daga jama'a.

Daga karshe..

Wannan lamari fa addini ne. Kuma duk wanda Allah ya ba shi wata dama ta taimakawa domin ci gaban Shari'a da daukakar ta, to Allah ya bude masa wata babbar kofa zuwa aljanna. Don haka kada ya yi sakaci da ita.

Allah ya yi mana jagora, ya tsarkake zukatanmu, ya kyautata ayyukanmu, ya sa mu yi karshe mai kyau.

Na gode da wannan dama da aka ba ni.

ﻭﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺍﺷﻬﺪ ﺍﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 04:20:04 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai



"DANDALIN AHLULBAITI DA SAHABBAI" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com