Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


HADARIN ZALUNCI DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA)
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen DR. MANSUR IBRAHIM SOKOTO

HADARIN ZALUNCI DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al'ummar musulmi! Addinin musulunci addinin Allah ne da ya shinfida hanyoyin zaman lafiya da jin dadin rayuwa. Daga cikin manya manyan dokokin ubangiji shi ne ya wajabta adalci kuma ya haramta cuta.

Wadannan dokokin Allah ya dora su har ga kansa. Don haka, Allah Tabaraka Wa Ta'ala ba ya zalunci kuma ba ya bari a zalunci bayinsa. Allah Ta'ala yana cewa:

A hadisul kudsi ga abinda Allah ke cewa:

A cikin dukkan addinan da Allah ya saukar ba in da bai haramta zalunci ba, Gashi ko dan adam an halicce shi da son yin zalunci da cuta kamar yadda Allah ya ce:

Al-Hafiz Ibnu Kayyim al-Jauziyyah yana cewa:

Duk asalin kowane alheri abu biyu ne: Ilmi da adalci. Haka kuma duk asalin kowane sharri daga jahilci ne da zalunci. Idan Allah yana son alheri ga mutum sai ya sanar da shi abinda ke amfaninsa, sai ya kawar da jahilci, sannan ya ba shi ikon amfani da shi sai ya gusar da zalunci. 

Duba Igathatul Lahfan (2/136-137).

Hadarin zalunci ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya shelanta haramcinsa a taro mafi girma kuma mafi daraja da musulmi suka taba yi a zamaninsa.

Hadarin zalunci yana kara hauhawa idan ya kasance ya auka ma jama'a masu yawa, ko wadanda aka sani ko wadanda ba a sani ba.

Wannan shi ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya tsananta maganar cin dukiyar ganima kafin a raba ta kuma ya ce, { ﻋﺎﺭ ﻭﻧﺎﺭ ﻭﺷﻨﺎﺭ ﻋﻠﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ } kuma da aka kashe wani yaronsa da ake ce ma Mid'am sahabbai suka ce, muna yi masa murnar shiga aljanna, sai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, sam. Na rantse da Allah yana can yana ci da wuta a kan bargon da ya dauka daga cikin ganimar Khaibar. Da jin haka sai wani sahabi ya yi sauri ya dawo da saitin takalma guda daya da ya dauka. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, ka kuru, domin da sun zame ma ka takalma biyu na wuta.

Kafin mu fadi irin hadurran da ke tattare da zalunci bari mu diba irin tsawatawar da Allah Ta'ala ya yi dangane da shi:

Kuma shi zalunci ba ya da kadan. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya ci zalun wani mutum da karfi Allah zai haramta ma sa aljanna ya wajbta ma sa wuta. Sai wani ya ce, ya manzon Allah, ko da abin kadan ne? sai Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, ''Ko da karen aswaki ne''. Muslim ya ruwaito shi.

Daga cikin manyan bala'oin da zalunci ke haifarwa akwai:
br>
3. Allah ba ya son azzalumai:

6. Zalunci yana janyo halaka ga al'umma

7. A kullum wanda ke zalunci ba ya rabuwa da Allah ya isa. Wannan ko yana da matukar hadari. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma Mu'az bin Jabal Radiyallahu Anhu: «Ka kiyayi «Allah ya isar» wanda aka zalunta, don ba ta da shamaki tsakanin ta da Allah». Haka kuma sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu ya ruwaito daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa: «Addu'ar mutum ukku Allah na karbar su: «Wanda aka zalunta da Matafiyi da Mahaifi».

Kana can kana sharar bacci, kana ta sakin hansari, hankalinka a kwance, ba ka tunanin kome, shi kuma wannan bawan Allah yana can yana dako, sai dare ya kai tsakiya ko ya kusa karewa, a cikin duhu zai tashi, cikin natsuwa ya yi alwala ya kabbarta sallah..

idan ya kai goshinsa ga kasa sai ya tartsa ma Allah kuka, a daidai lokacin da Allah ke shelar: «Ina mai kirana in karba ma sa?» «Ina mai neman agajina in agaza ma sa?».

Ana haka ne zai kai karar ka ga buwayayyen sarki. Don haka ne sai ka ga kwatsam!

al'amarin mutum ya dagule, basirarsa ta toshe, dabararsa ta kare, jarinsa ya kare, ikonsa ya gushe, lafiya ta karanta, jin dadi ya kau, jama'a sun watse, an bar shi da tarin zunubi, da yawan bakin ciki da karancin jin dadi ..Wannan duk karamin aikin Allah ya isa kenan. Wannan shi ne abin da sarki Khalid al-Barmaki ya fada ma dansa lokacin da aka tsare su a kurkuku, yaron ya ce, Baba! dubi halin da muka fito kuma dubi yanayin da muka samu kanmu. Sai sarki Khalid ya ce ma sa, Allah dai ya kiyaye. Watakila wani ne ya yi mana ''Allah ya isa» muna can muna bacci.

Wani fursuna ya yi ma sarki Khalid bin Abdillah al-Kasari wa'azi mai kama da haka a lokacin yana gwamnan Khurasan sai ya kai ziyara gidan kaso yana raba ma fursunoni kyauta. Da ya kawo ga wannan bawan Allah sai ya ce ma sa: In don ka tausaya kake bayarwa to, tausaya ma kanka daga wanda ka zalunta. Yi hattara da wanda bai da kowa sai Allah, bai da wani makami sai addu'a. Ka sani kofofin sama gaba daya budewa su ke in an ce, ''Allah ya isa».

Ga nasihar da wani mawaki ya yi:

Saurari abinda annabin Allah Yusuf Alaihis Salam ya ce a lokacin da matar maigidansa ta neme shi da ya ci amanarsa:

9. Allah ba ya shiryar da azzalumi

10. Azzalumi zai gamu da gamonsa tun a nan duniya

11. A ranar alkiyama azzalumi yana da ban tausai:

A rannan ne azzalumi zai nemi ba da fansa da duk abinda ya mallaka, ciki har da dan jarinsa na duniya, kai da ma duk abinda ake so in zai samu. Amma ina!

12. Ba yadda za a yi a shiga aljanna tare da digon zalunci domin kuwa ko bayan tsallaka siradi ba a shiga aljanna har sai an kawar da zalunci kowane iri, an kwatar ma kowane mai alhaki hakkinsa. Abu Sa'id al-Khudri Radiyallahu Anhu ya karbo daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa, ''Idan mummunai suka tsallaka siradi za a tsayar da su a kan wata gada da ke tsakanin aljanna da wuta sai a caje su da wasu laifukka na zalunci da suka gudana a tsakanin su. Sai an gama tsarkake su tsabal sannan ayi ma su iznin shiga aljanna''.

Sannan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya yi rantsuwa cewa, idan suka shiga aljanna kowa zai gane gidansa fiye da yadda ya ke gane gidansa na duniya.

Sahihul Bukhari (2440). Allah Ta'ala ya yi gaskiya:

Ya ku bayin Allah! Da yawa mukan yi kuskure in mun ji ana ruwan ayoyi game da zalunci da azzalumai sai mu ce, sarakuna sun halaka! Kaicon masu mulki! Bone ya tabbata ga alkalai!!! Babu in da ba a iya samun zalunci a cikin zamantakewa ta rayuwa. Akwai zalunci a ciniki, akwai shi a bashi, akwai a kwadago, akwai a auratayya, akwai a makwautaka, akwai malanta. Haka kuma akwai shi a magana, akwai a kallo, akwai har a batun zucci ta hanyar miyagun zace-zace. Idan ka sa mutum aiki ka rage ma sa hakkensa kai azzalumi ne. idan ka yi algussu a cikin sana'arka kai azzalumi ne.

Idan ka sare icce wanda mutane suke shan inwa kai azzalumi ne. Idan aka yi yarjejeniya da kai ka saba kai azzalumi ne. Idan ka kwance sharadi kai azzalumi ne. Idan macce ta debi kayan gidan mijinta ba da izninsa ba ita azzaluma ce. Idan miji ya kasa ba matarsa hakken kwanciya ko na abinci ko karantarwa ko kulawa da lafiyarta shi azzalumi ne. Kai, idan ma ya kasa ba ta alhakinta na zaunawa su yi fira, da jiyar da ita dadin rayuwar macce da namiji shi azzalumi ne. Haka kuma azzalumi ne idan ya kasa daidaita alhakin matansa ko 'ya'yansa.

Babu shakka shugaba in ya zamo azzalumi to, hadarinsa ya fi girma wannan shi ya sa za a zo da kowane shugaba koda na mutum goma ne a daure ranar alkiyama sai dai in ya yi adalci adalcin nasa ya warware shi kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi. Duba Sahihul Jami' 5571 da Silsila Sahiha 344.

Zalunci mataki ukku ne:

1. Mafi hadarinsu shi ne wanda ya danganci hakkin Allah kamar Shirka. Sai kuma sauran zunubbai da Allah ya hana.

2. Zaluntar bayin Allah. Mafi hadari daga cikin zaluntar bayin Allah shi ne zubar da jininsu, sannan cin mutuncinsu, sannan kwace ko satar dukiyarsu.

3. Mutum ya zalunci kansa ta hanyar aikata abinda zai halaka shi ko ya sa shi cikin kunci a nan duniya ko a gobe kiyama.

Idan an zalunce ka ya zaka yi? akwai matakai guda uku, wanda duk kayi babu laifi a kanka:

1. Ka rama daidai yadda aka zalunce ka in kana da iko.

2. Ka roki Allah ya rama maka, ko ya kwatar ma ka hakkinka.

3. Ka yafe saboda Allah

Wadannan matakan gaba daya Allah Ta'ala ya fade inda yake cewa:

Ya ku bayin Allah! wanda ya fada a cikin zalunci alhakinsa a kan mu shi ne mu taimake shi. Ya zamu taimake shi? wannan shi ne abinda sahabbai suka tambayi manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama a lokacin da ya ce, ''Ka taimaki dan uwanka ko shi ke zalunci ko shi aka zalunta''. Amsar da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ba su ita ce, taimakon azzalumi shi ne a kange shi a hana ma sa yin zalunci. Allah Ta'ala na iya yi wa azzalumi talala amma ba zai taba kyale shi ba. Sau da yawa kuma Allah ya ke sallade wani azzalumi don ya darkake wani. Kamar yadda madaukakin sarki ya ce:

Don haka ne wani malami ya ce:

A nan duniya azzalumi na iya samun girma da kima ko don kwadayin abin hannunsa ko don gudun sharrinsa, amma a ranar alkiyama babu wulakantacce marar daraja da kima irin sa. Sai dai yana da kyau mu sani cewa, kome girman zalunci yana da tuba kamar yadda madaukakin sarki ya ce:

Don haka, Allah ya bude kofa gare ka ya kai dan adam mai yawan zalunci. Ka tuna duk irin nau'in jama'ar da ka zalunta. Sannan ka bi hanyar sasantawa da su tun ba a tafi lahira ba suka nemi ladarka sa'adda ka fi kome bukatuwa zuwa gare ta, kuma a rannan kana ji kana gani za a ba su ladar azuminka da umrarka da sauran ibadarka.

An gabatar da ita a ranar 2 ga jimada Akhir
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 04:24:08 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"HADARIN ZALUNCI DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA)" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: