Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin
[ Fiqh - Shin, Hakika, Mai jin ]

·It's Haram To Aid, Promote Or Participate In The Oodua Nation Agitation
·Tauhidi ginshikin Musulunci (5)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (4)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (2) - (3)
·Tauhidi ginshikin Musulunci (1)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (4)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)
·Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (1)
·Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


ARBA'UNA HADITH ARBA'UNA HADITH {1} HADISI NA FARKO
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji ARBA'UNA HADITH ARBA'UNA HADITH {1} HADISI NA FARKO

An karbo daga sarkin muminai, baban Hafs, Umar bin khaddabi yace naji Manzon Allah (SAW) yana cewa ''Lallai kadai, ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya (a zuciyarsa). Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda Allah da Manzon sa, wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda duniya da zai samu, ko don wata mace da zai aure ta, wannan sakamakon hijirar sa na nan kan abin da ya yi hijira zuwa gare shi.'' Shugabannin masu hadisai ne suka rawaito shi. Su ne Muhammad dan Isma'ila dan Ibrahim dan Mugirata dan Bardizbah Al- Bukhari Al-Ju'ufiy. Da Abul Husaini Muslimu dan Hajjaju dan dan Muslimu Alqushairiy Annaisaburiy. Acikin ingantattun littattafan su, wadanda sune mafi ingancin littattafai da aka rubuta.

SHARHI Wannan hadisi yana xaya daga cikin hadisai mafiya shahara daga cikin hadisan Annabi (SAW), mutum xaya ne yaji wannan hadisin daga bakin Annabi (SAW) shi ne Umar dan khaddab mutum daya ne yaji wannan hadisi daga Umar dan khaddab, shi ne Alqama bin waqqas Allaisiyyi. Haka kuma mutum xaya ne yaji shi daga wajen Alqama, shine Muhammad bin Ibrahim Attaimiyyi; mutum xaya ne tak yaji shi daga wajen Muhammad bin Ibrahim Attaimiyyi, shi ne Yahaya bin Sa'id Al-Ansariyyi. Daga kan wannan bawan Allah, Yahaya bin Sa'id Al- Ansariyyi ne wannan hadisi ya shahara.

Domin shi xaya sama da mutum xari biyu ne suka rawaito hadisin awajen sa. Wannan itace hanyar da ta inganta cikin hanyoyin wannan hadisin. Wasu malamai sukan rawaito shi daga Sa'ad bin Abi waqqas, amma bai inganta ba, wannan itace kaxai hanya ingantacciya da ta tabbata. Daga cikin mutanen da sukaa ji wannan hadisin awajen sa akwai Imamu Malik bin Anas, da Ishaq bin Rahawaihi, da Ahamad bin Hambal, da Shu'uba, da Sufyan bin Sa'id Assauriy, da Sufyan bin Uyayna.

Imam Bukhari ya mayar da wannan hadisi ya zamanto shine gabatarwar littafin sa Sahihul Bukhari. Bayan bismillah, sai ya kawo wnnan hadisin don ya mayar dashi gabatarwa ta littafin sa, domin yanu nawa mutane cewa, kowanne irin aiki da za ka yi, baya kasancewa abin qirgawa awajen Allah, sai in ya zamanto ka yi shi da kyakkyawar niyya, kuma domin ya nuna muna tsadar ikhlasi a cikin ayyuka. Malamai da dama sun yi magana kan matsayin wannan hadisin, har Abdurrahman bin Mahdi yake cewa,''Da zan sami damar wallafa littafi mai babi-babi na hukunce-hukunce, to da sai na mayar da wannan hadisi ya zamanto shi ne gabatarwar kowanne babi.'' Imamush- shafi'i yana cewa, ''Shi wannan hadisi shi ne sulusin ilmi gaba xaya.'' Abin da ake nufi da sulusin ilimi, kashi xaya cikin ukun ilmi, sannan ya ci gaba da cewa, ''Zai iya shiga babi xai-xai har guda saba'in daga cikin babin fiqhu. (Duba: Jami'ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/23. Fathul Bari 1/1011).

Lafazin Hafs da ya zo a wannan hadisi,a larabce, xaya ne daga cikin sunayen zaki, su kance Asad, sukan ce masa Aglab, sukan ce Hizabr. Zaki ya na da sunaye xai-xai har guda xari idan ka duba Qamus. Ana ce wa Umar xan Khaxxabi Abu Hafs, saboda jaruntakar sa kuma yana alfahari da wannan alkunya ta Abu Hafs, domin Annabi (SAW) ne ya yi masa alkunya da cewa Abu Hafsin.

Dangane kuwa da laqabin Amirl Mu'uminina Umar xan Khaxxabi shi ne mutum na farko daga cikin sahabbai wanda suka yi shugabanci a bayan Annabi (SAW) da ake yi wa laqabi da Amirul Mu'uminina(RA).

Dangane da faxinsa (SAW) cewa, ''Lallai kaxai ayyuka suna tare da niyyoyinsu..........,'' anan wurin duk aiki ne, ake yi wa niyya ko kuma akwai waxanda ba a yi musu niyya?

waxansu malamai sun ce akwai waxanda ake yi musu niya, akwai waxanda ba a yi musu niyya. Abin da ake nufi da 'ayyuka' a nan kuwa, shi ne ayyukan da suka shafi shari'a kai tsaye, kamar alwala da sallah da zakka da azumi da dukkan aikin da yake ibada ne tsansta. To irin waxannan ayyuka sune suke buqatar niyya. Amma akwai ayyukan da suka shafi xabi'arka ta xan adam ta yau da gobe, kamar zama da tashi da kwanciya dakishingixa da cin abinci da shan ruwa da yin wanka da sanya tufafi, da dai sauransu. Waxannan duk sunansu ayyuka, amma ba sa buqatar niyya don zaka zauna, ba wani buqatar niyar zama, don za ka tashi, ba buqatar sai kayi niyyar tashi.

Ashe lafazin 'ayyuka' a nan, ba ayyuka gaba xaya ake nufi, abin da ake nufi shi ne dukkan ayyukan da suke shari'a ce tace ayi su. To irin waxannan ayyuka, su ne suke buqatar niyya. [Duba: Jami'ul Ulum Wal- Hikam Na Ibnu Rajab 1/26].

Hadisin ya yi maganar hijira, abin da ake nufi da hijira shi ne mutum ya yi qaura daga garin kafirci zuwa garin musulunci.

Wannan shi ne asalin hijira, wannan hijirar wajibi ce, kuma abu ne mai falalar gaske, shi ya sa ko cikin Alqur'ani Ubangiji ta'ala ya kasa sahabban Annab (SAW) kashi biyu, akwai Al-Muhajirun, akwai Al-Ansar. Su Al- Muhajiru xin, kullum aka zo kawo labarin su ake fara gabatarwa. To irin wannan hijirar, idan mutum yana son ya yi ta, ya samu lada to dole sai ya kasance ya yi ta domin Allah, kuma ya yi ta domin koyi da Manzon Allah (SAW). Wannan shine ma'anar faxin Manzon Allah(SAW) cewa, ''........Wanda duk hijirar sa ta kasance saboda Allah da Manzonsa........'' Wani zai iya cewa, to ai anayin abu ne domin Allah kaxai, don me aka rava Manzon Allah (SAW) a ciki ? Ibnul Qayyim acikin littafinsa Zadul Ma'ad ya fasssara wannan hadisin ya ce, faxin Manzon Allah (SAW)
cewa, ''Wanda duk hijirarsa ta kasance sabo da Allah......'' yana nufin da tauhidi, cewar, ''.....da Manzonsa .....'', yana nufin don xa'a ga Manzon Allah (SAW). Don haka hijira zuwa ga Allah ita ce, qaura zuwa gare shi ta hanyar tauhidi; Hijira zuwa ga Manzon Allah (SAW) ita ce qaura zuwa ga reshi ta fuskar xa'a da biyayya, tunda shine yabada umarnin a yi hijira xin, amma ba wai don shi zai ba da ladaba. Yadda ba'a bautawa kowa sai Allah, haka kuma ba a yi wa kowa biyayya ta gaba xaya, sai Manzon Allah(SAW).

Faxin Annabi (SAW) cewa, ''......wanda hijirar sa ta kasance sabo da Duniya da zai samu, ko don wata mace da zai aure ta, wannan sakamakon hijirarsa na nan akan abin da ya yi hijira gare shi.'' Yana nufin dukkan wanda ya yi hijira daga wani gari zuwa gari, ya zamto abin da ke cikin zuciyarsa shine don ya ci ribar abu iri kaza na duniya, to wannan abin shi kaxaine abin da wahalar sa ta hijira za ta qare akai, ko ya sami abin ko bai samuba, ba shi da lada a wajen Allah. Haka nan wan da yayi hijira domin auren wata, shi ma wannan abin shi kaxai ne abin da hijirarsa za ta faru ta qare akai, ko ya sami auren ta ko bai sami auren ta ba, ba shi da ladan komai a wajen Allah Ta'ala.

Wasu malamai sukan rawaito hadisin cewa, akwai hadisin wani sahabi da ake cewa Muhajiru Ummu Qaisi, wanda yana neman wata baiwar Allah cikin muminai da aure, sai ta yi hijira ta tafi Madina, shi ko da bai da niyyar zuwa Madina, da ta yi hijira shima sai ya naxe kayan sa ya yi hijira, ya taho Madina. To wai sanadiyyar sa ne sai Annabi (SAW) ya faxi wannan hadisi. Wannan bayani bai inganta ba daga Annabi (SAW), wannan hadisi ne da'ifi.[Don qarin bayani duba: Fathul-Bari 1/10 A nan wurin da Annabi (SAW) ya faxi ayyuka, sai ya buga misali a kan xaya daga cikin ayyukan da ake yi musu niyya, sai ya kaho hijira, don kai kuma, ka yi ta kawo sauran ayyukan da za su iya shiga qarqashin kalmar ''ayyuka''. Buga misali ne Annabi (SAW) ya yi, abin ya faru, ko bai faru ba, ya buga misali ne dashi. Duk wanda ya yi hijira don Allah, to ga sakamakonsa, duk wanda ya yi hijira don wani abu, sai ya faxi dangogin abubuwan da mutane ke buqata a rayuwarsu.

Niyya tana da vangarori guda biyu:

Vangaren farko, Shi ne vangaren da ya shafi fiqihu zallah. A nan wajen ana kawo niyya ne saboda rarrabe tsakanin ibada da ibada, kamar rarrabe tsakanin azahar da la'asar.

Idan mukayi la'akari game da waxannan salloli biyu, zamuga raka'o'I huxu akeyi, tsarin karatu xaya akeyi, suffer da ake yin su duk iri xaya ce, abin da ake bamban ce wannan azahar ce, wannan la'asar ce, shi ne niya! Sabo da haka ana zuwa da niya sabo da a bamban ce tsakanin ibada da ibada; tsakanin farilla da lafila; tsakanin kaffara da bakance, duk niya ce take banbance waxannan. Sannan ana zuwa da ita don bambance tsakanin Ibada da al'ada.

Wani yana iya qin cin abinci sabo da yana yajin cin abinci, kamar yadda ''yan kurkuku suke yi awani gari, yace yau wannan wunin gaba-xaya, ba zai ci abinci ba, awa goma shabiyu, cur. Kai kuma katashi da niyar yin azumi ka yi awa goma shabiyu cur, bambancin da ke tsakanin ka das hi anan, shi ne ta fuskar niyya. Sai babin tan a biyu, shi ne alaqar niyya xin da wanda aka yi aiki domin sa, shi ne Allah (SWA). Idan akayi niyyar sallar azzahar a irin tsarin da ake yin niyya, ka sallaci raka'a huxu, sallah ta ingan ta, yan zu sai akai niyya kasha ta biyu kafin maganar lada ya zo itace kyakkyawar niyya stakanin ka da Allah. Yazamto ka yi wannan sallah don ne man kusancin Allah Ta'ala. To wannan niyya a wannan vangaren ta na biyu, ba ta shiga babukan fiqihu, tana shiga babin tauhidi ne. Malamai da dama sun yi wallafe-wallafe a kan niyya ta vangaren tauhidi kuma dukkanninsu suna kafa hujja da faxin Annabi (SAW) a cikin wannan hadisin, ''Lallai kaxai aiyuka suna tare da niyyoyin su''........Kuma lallai ko wanne mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya (azuciya) ......'' wannan vangaren day a shafi tauhidi kenan. {Duba: Jami'ul Ulum Wal-hikam Na Ibnu Rajab 1/28} Faxin Manzon Allah (SAW)ce wa, ''.....kuma lallai kowanne mutum yana samun sakamakon abin da yayi niyya (azuciyar sa)
...... ''yana nufin abin da ka niyyata, shine abin da za ka samu. Idan kayi tagari tsakanin ka da Ubangiji,, to Allah zai baka lada, idan kuma baka da niyya tagari to baka da lada awajen Allah. Rashin bambance wannan zai haifar maka da matsala da dama. Sai ace mutum ya yi sallah ta isar masa, amma ba lada, sai kayi mamaki, to sabo da yayi niyyar da ta shafi wanda ake yin aikin domin sa, bata yi kyau ba.

Malamai na cewa idan mutum ya yi aiki, ya nufi wani a cikin aikin (wato ya yi riya), wannan bas hi da lada awajen Allah. To amma abin na iya zama kasha biyu: Ta iya yuwa, farkon lokacin da za ka yi aikin, ka yi shi domin Allah. Ka ta shi niyyar yin sallah domin Allah, kana cikin yi kafin ka qarasa, sai riya ta shigo. Wannan riyar da ta shigo a tsakiyar sallarka kafin ka qarasa, bayan afarko kayi niyyarka ka yi domin Allah, domin samun kusancin Allah bat a isa ta rusa maka aikinka ba, aikin ka na nan da cikakken ladanka a wajen Allah.

Don haka sai wasu malamai sukace, ayyuka iri biyu ne: Ko dai aikin da yake farkonsa da qarshen sa suna haxe da juna kamar sallah, raka'ar qarshe tana haxe da ta farko.

Sukace aiki irin wannan, wanda qarshen sa yake haxe da farkon sa, to in ka yi kyakkyawar niyya da farko to ko riya ta shigo, bata isa ta rusa maka shi ba, saboda in farkon ya ingan ta, to qarshema zai tafi ahaka. Amma aikin da qarshensa baya haxe da farkonsa, kamar karatun Al-qur'ani; misali kana cikin karatun Al-qur'ani da kyakkyawar niyya, kayi izifi biyu da kyakkyawan karatun ka don Allah, sai wani yazo karatun yaburgeshi yana sauraro, sai ka qara koxa muryar ka don ka burge shi, to wannan hizifi biyun da ka yi, ka samu wannan amma daga ayar da kafara koxa muryar ka, aikin ka ya rushe saboda qira'ar farko bata da alaqa da qarshen ta, inda kayi da kyakkyawar niyya kana da lada inda ka yi mummunar niyya kuma, baka da lada.

Idan kuma ya zamto aikin baka fare shiba kana zaune baka da niyyar yinsa, sai kawai katashi ka yi shi domin wani, to wannan anyi ittifaqin ba ka da ladan komai aciki, kuma malamai da dama sunce musulmi ba shi da wannan xabi'a duk wanda ya yi wannan to ana jin tsoron wannan yafitar das hi daga cikin musulunci, musamman idan wannan aikin ya zamto wajibi ne yinsa, kamar sallah. Mutum baya sallah kwata-kwata, sai yaga wasu abokan sa sunzo, ko yaga wani mutum da yake jin kunyarsa yazo, sai yatashi ya yi sallah, kawai domin waxannan kada su tuhumce shi da cewa baya sallah, amma a zuciyarsa ba ruwnsa da ita, to wannan mutum ba musulmi bane, akwai jin tsoran ya shiga qarqashin faxin Allah Ta'ala, { } [Duk waxanda suke nufin duniya (da ayyukansu) da kayan adonta, to za mu cika musu ayyukansu acikinta, ba za'a tauye musu ba. Su ne waxanda ba su da komai a lahira sai wuta, abin da duk suka aikata ya rushe, haka abinda suka aikata ya lalace] (Hudu: 15-16).

Bai halalta ga mutum yace zai yi lafazi da niyya. Niyya abu ne a zuci, har ma da dama daga cikan malamai sun bada fatawar cewa yin lafazi da niyya bidi'a ne. [Duba: Jami'ul Ulum wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/63]. Don haka da zarar kazo sallah ko azumi, abin da ake buqata shine qudur cewa a cikin zuciyar ka, irin sallar da zaka yi. Azahar ce ko la'asar ce, za ka yi ta ne kai kaxai ko jam'I ne wannan duk zaka halarta wa zuciyar kane,ba sai bakinka ya furta haka ba. Da niyyar azumi da niyyar aikin hajji, da niyyar sallah da ko wacce niyya ba a furtata da baka, ana qudurcewa ne a zuci. Da ka qudur ce a zuci shike nan, ka shiga sallah!

Sai muqaranatun niyya; wato ya zamto da ibadar da niyyar sun haxu da juna, lokacin da zaka shiga cikin ibdar. Misali, lokacin da zakazo ka yi azahar ka fuskanci alqibla, bakin ka nacewa Allahu Akbar! Zuciyar ka na qudurce niyyar sallar da zaka yi, azahr ce ko la'asar ce. Wannan shine muqaranatun niyya! Haqiqanin al'amrin shine, in ka gabatar da niyya azuci, sannan ka yi, kabbara, sallar ka ta yi idan ka cuxanya niyya da kabbara, sallarka ta yi. Abin da ba zai yiwu ba shine ka yi kabbara, sannan kuma daga baya ka shigar da niyya, wannan ba zai yiwu ba.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 04:26:36 PST Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"ARBA'UNA HADITH ARBA'UNA HADITH {1} HADISI NA FARKO" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: