Muhawara Hausa
 



ARBA'UNA HADITH {2} HADISI NA BIYU
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji ARBA'UNA HADITH {2} HADISI NA BIYU

An karbo daga sarkin muminai baban hafs umar bin khaddabi yace na ji manzon allah (SAW) yana cewa lallai kadai ayyuka suna tare da niyyoyinsu kuma lallai kawane mutum yana samun sakamakon abin da yayi niyya (a zuciyarsa). Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda allah ga manzon sa to hijirar sa ta ga allah da manzon sa waanda yai hijira saboda duniya da zai sameta ko dan wata mace da zai aure ta to hijirarsa tada ga abin da yai hijira saboda shi.

Shugabannin masu hadisai ne suka rawaito shi. Sune Muhammad dan isma'ila dan Ibrahim dan magirata da bardizah al- bukhari al-ju'ufy(1,54) da abul hussain muslimu dan hajjaju dan muslimu alkushairiy annaisaburiy (1907) a cikin ingantatun littattafansu wadan da sune mafi ingancin littattafai da aka rubuta.

SHARHI; Wannan hadisi yana daya daga cikin hadisai mafiya shahara daga cikin hadisian annabi (SAW) mutum day ne ya ji wannan hadisi daga bakin annabi(SAW) shi ne umar dan khaddab mutum daya ne yaji shi ga umar dan khaddab shi ne alkama bin wakkas allaisiyyi haka ma mutum daya ne yaji shi daga wajen alkawama shi ne Muhammad bin Ibrahim attaimiyyi mutum daya ne taka ya ji shi daga wajen Muhammad bin Ibrahim attaimiyyi, shine yahaya bin sa'id al- ansariyyi daga kan wanna bawan allah yahay bin said al-ansariryyi ne wanna hadisi ya shahara.

Domin shi daya sama mutum dari biyu ne suka rawaito hadisin a wajen sa wannan it ace hanyar da ta inganta cikin hanyoyin wanna hadis. Wasu malamai sukan rawaioto shi daga sa'ad bin abi wakkas, amma bai inganta ba wanna it ace (kadai)
hanya ingantataciya da ta tabbata. Daga cikin mutanen da suka ji wanna hadisi a wurinsa akkwai imamu malik bin anas da ishak bin rahawaihi da ahamd bin hambali da shu'ub da safyan bin said assuriy da sfyan bi uyayna.

Imamul buikhari ya mayar da wanna hadisin ya zamanto shi ne gabatarwar littafinsa sahihul bukharri. Bayan busmillah sai ya kawo wanna hadisin don ya mayar da shi gabatarwa ta littafin sa domin ya nuna wa mutane cewa a wajen allah sai in ya zamanto ka yi shi da kyakkyawar niyya, kuma domin ya nuna mana tsadar iklasi a cikin ayyuka. Malamai da dama sun yi Magana kan matsayin wanna hadisi har abdurahaman bin mahdi ya ke cewa d azan sami dammar wallafa littafi mai babi –babi ba hukunce hukunce to da sai na mayar da wanna hadisi ya zamanto shi ne gabatarwar kowane babi,'' imamush shafi'I yana cewa shi wanna hadisi shi ne sulusin illimi gaba daya. Abin da ake nufi sa sulusi illim kashi daya bias uku illimi sannan ya ci gaba da cewa zai iya shi ga babi har guda saba'in daga cikin babiN fikhu.

Lafazin hafs day a zo awanna hadisi, a larebce daya na daga cikin sunayen zaki sukan ce masa hafs sukan ce asad sukan ce masa aglab sukan ce hizabr. Zaki yana da sunaye daidai har guda dari idan ka duba kamus an ace wa umar dan khaddab abu hafs saboda jaruntakarsa, kuma yana alfahari da wannan da cewa abu hafsin.

Dangane kuwa da lakabin amirul mu'umina umar dan khaddab shi ne mutum na farko daga cikin sahabbai wanda suka yi shugabanci a bayan annabi (SAW) da ake yi wa lakabi da amirul mu'uminina(RA).

Dangane da fadinsa (SAW) cewa ''Lallai kadai ayyuka suna tare da niyyoyinsu......'' a nan wurin duk aiki ne ake yi wa niyya ko kuma akwai wadanda ba ayi musu niya?

wadansu malamai msun ce akwai wadanda ake yi masu niyya akwai wadanda ba ayi nmusu niya abinda ake nufi da ayyuka a nan kuwa shi ne ayyukan da suka shafi shari'a kai tsaye kamar alwala da sallah da zakka da azumi da dukkan aikin da yake ibada ne tsantsa. To irin wadannan ayyuka sune suka bukatar niyya. Amma akwai ayyukan da suka shafi dabi'arka tad an adam ta yau da gobe kamar zama da tashi da kwanciya da kishingida da cin abinci da shan ruwa da yin wanda da sanya tafafi da dai sauransu. Wadanna duk sunansu ayyuka amma bas a bakatar niyya. Don za ka zama ba wani bukatar niyyar zama don sa ka tashi ba bukatar sai kayi niyyar tashi.

Ashe lafazin ayyuka a nan ba ayyuka gaba daya ake nufi ba, abin da ake nufi shi ne dukkan ayyukan da suke shar'ia ce t ace a yi su. To irin wadannan ayyuka sune suke dbukatar niyya.

Hadisi yayi maganar hijira abin da ake nufi da hijira shi ne mutum ya yi kaura daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Wanna shi ne aslain hijira wannan hijir wajibi ce kuma abu ne mai falalar gasket shi ya sa ko cikin alkur'ani ubangiji ta'ala bayani bai inganta ba daga annabi(SAW) wanna hadisi ne da'ifi.

A nan wrurin da annabi(SAW) ya fadi ayyuka sai ya buga misali a kan daya daga cikin ayyuka da kae yi masu niyya. Sai ya kawo hijira don kai kuma ka yi ta kawo saurna ayyukan da za su iya shiga karkashin kalmar ayyuka baga misali ne annabi(SAW) ya yi abin ya faru ko bai faru bva ya buga misali ne da she. Duk wanda yayi hijira don allah to ga sakamankun sa dukk wanda ya yi hijira don wani abu sai fadi dangogin abubuwan da mutane ke bukata a rayuwarsu.

Niyya tana da bangarori guda biyu bagaren farko shi ne bangaren day a shafi fifiku zall.

Anan wurin ana kawo niyya ne saboda rarrabe tsakanin ibada da ibada, kamar rarrabe tsakanin azahar da la'asar. Idan muka yi lakari game da wadannan salloli biyu zamu ga raka'o'I hudu ake yi tsarin karatu.

Sai babinta na biyu shine alakar niyya din da wanda aka yi aiki dominsa shi ne allah (SAW) idan ka yi niyyar sallar azahar a irin tsarin da ake niyya ka sallaci raka'a hudu salla ta inganta yanzu sai ka yi niyya kashi kashi ta biyu kafin maganar lada ta zo it ace kyakkyawar niyya tsakaninka da allah. Ya zamanto kayi wanna salla don neman kasuncin allah ta'ala. To wanna niyya a wanna bangarenta na biyu bat a shiga babukan fikihu tana shiga babukan tauhidi ne.

Idon kuma ya zamanto aiki ba ka fare shi ba kana zaune ba ka da niyyar yinsa sai kawai ka tashi ka yi shi domin wani to wannan an yi ittifaki ba ka da ladan komai a ciki kuma malamai da dama sun ce musulmi ba she da wanna dabi'a duk wanda kuwa ya yi wanna to ana jin tsoron wannan ya fitar da shi daga ne yi sa kamar salla. Mutum bay a sallah kwata kwata sai ya ga wasu abokansa sun zo ko ya ga wani mutum da yake jin nauyinsa ya zo ko wanda yake jin kunyarsa ya zao sai ya tashi ya yi sallah amm a zuciyarsa ba uwan sa daita to wannan mutum ba musulmi ban e akwai jin tsoron ya shiga karkashin fadin allah ta'ala.

( ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺍﻟﺤﻴﻮﺓ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﺯﻳﻨﺘﻬﺎ ﻧﻮﻑ ﺇﻟﻴﻬﻢ ﺃﻋﻤﻠﻬﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻫﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻻ ﻳﺒﺨﺴﻮﻥ 15 ﺃﻭﻟﺌﻚ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻟﻴﺲ ﻟﻬﻢ ﻓﻰ ﺍﻷﺧﺮﺯﺓ ﺇﻻ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﻭﺣﺒﻂ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﻮﺍﻓﻴﻬﺎ ﻭﺑﻄﻞ ﻣﺎ ﻛﻨﻮ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ 16 ).


(Duk wadanda suke nufin duniya (da ayyukansu) da kayan adonta, to za mu cika musu ayyukansu a cikinta, ba za a tauye musu ba. Su ne wadandada bas u da komai a lahira sai wuta, abin da duk suka aikata ya rushe, haka abin da suka aikata ya lalace {Hudu: 15-16}.

Ba ya hallata ga mutum y ace zai yi lafazi da naiyya. Naiyya abu ne a zuci, har ma da dama a cikin malamai sun bad a fatawar cewa yin lafazi da niyya bidi'a ne. {Duba:

Jami'ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/63}. Don haka da zarar ka zo sallah ko azumi abin da ake bukata, shi ne kudurcewa a cikin zuviyark, irin sallar da za ka yi. Azahar ce ko la'asar ce, za ka yi tan e kai kadai ko jam'i ne, Wannan duk za ka halarta wa ziciyarka ne, ba sai bakin ka ya furta haka ba. Da niyyar azumi da niyyar aikin hajji, da niyyar sallah da kowacce niyya ba a furta ta da baka, ana kudurcewa ne a zuci. Da ka kudurce a zuci shi kenan, ka shiga sallah! Sai Mukaranatun niyya. Wato ya zamanto da inbadar da niyya.

Misali, lokacin da ka zo za ka yi azahar, ka fuskanci gabas bakinka na cewa Allahu Akbar! Zuciyarka na kudurce irin sallar da za ka yi, azahar ce ko la'asar ce. Wannan shi ne ka yi kababra, sallarka ta yi. Abin da ba zai yiwu ba, shi ka yi kabbara, sannan kuma daga baya ka shigar da niyya, wannan ba zai yiwu ba.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN MARIGAYI SHEIK JA'AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

 Posted By Aka Sanya A Sunday, February 26 @ 05:11:10 PST Da MediaHausaTeam



Comments 💬 التعليقات
 

For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا

Hanyoyin da ke da alaƙa

· Ƙari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labarai By MediaHausaTeam


Mafi Karanta Labari Game da Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Matsalar Magana

Matsakaicin Maki: 0
Kurioi: 0

Don Allah a Ɗauki Na Biyu Ka Zabi Wannan Labarin:

Madalla
Mai kyau sosai
Mai kyau
Na yau da kullum
Bad


Zabuka


 Mawallafin Aboki Mawallafin Aboki





Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji



"ARBA'UNA HADITH {2} HADISI NA BIYU" | Shiga/ Ƙirƙiri Asusu | 0 Lafiyata


Malakacin Bayanan na Mai aikawa. Ba Mu Da Alhaki Don Abubuwan da Suke ciki. A halin yanzu, Muna gayyatar masu karatu su ba da rahoton duk wani abu na cin zarafi, rashin dacewa da / ko abun ciki na Islama



Babu Sharhi Ta da Aka Bada izini Don Marasa Suna, Da fatan za a Yi rijista
 

Muhawara Hausa
Asusu Gare Ku
Babban Shafi  | Labarun Hausa  | Muhawara Hausa  | Ƙungiyar Hausa  | Saƙonninku Na Sirri  | Samiya Goma  | Batutuwa  | Takardun Labari  | Cagiya  | Yakan Yi Bitar  | Bincike  | Mujallan  | Ma\'ajiyar Takardu  | Shafin Yanar Gizo  | Saukewa  | Shawarce Mu


Ẹsin Islam الدين الإسلامي Religion of Islam Addinin Musulunci Agama Islam Religión del Islam 伊斯兰教 Dini ya Kiislamu Религия Ислам Religião do Islã イスラム教 Esin Islam 이슬람의 종교 Portal African Muslim Website - Arabic English African Islamic Website For World News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Articles, Radio, Audio, Video, Quran, Hadith, TV Channels, Fatwas, Muslim News, Newspapers, Magazines Headlines, Forums, College, Schools, Universities, Mosques, Quranic, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Ramadan, Vidoes, Books, Fasting, PDFs On EsinIslam.Com And IslamAfrica.Com