Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Al'Adun Musulmi Da Darajoji
[ Al'Adun Musulmi Da Darajoji ]

·Falalar Darare Goma na Zul-Hajji
·Dabbobin Layya da kwanakin 10 na farkon Zul-Hajji
·Azumi da abubuwan da yake koyarwa (4)
·Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
·Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
·Buhari Da Muslim: Babi Na Hudu 140 - 142 & 148
·Buhari da Muslim: Babi na Talatin da Biyu 114 - 124

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR

An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace ''Kada ku rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna. Muslim dan uwan muslim ne, kada ya zalunce shi, kada ya kuntatar da shi, kada ka yi masa karya, kada ya wulakantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku).!! Yana nuna kirjinsa,'' Ya ishi mutum sharri, ya rika tozartar dad an uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi.(1) Muslim ne ya rawaito shi (# 2564).

SHARHI; Abin da ake nufi da hassada shi ne ka rika burin ina ma ni'imar da wane yake cikinta taho ta barshi ina ma dukiyar wane ta ragu jarinsa ya lalace ka rinka jin ina ma mukamin da ka baiwa wane yazo ya rasa to wannan itace hassad kuma siffa ce ta yahudu sun fi kowa sanin Annabi da siffofinsa amma hassada ta hana su yin imani dashi don haka, kayi kokarin ka wanke zuciyarka daga yi wa dan'uwanka musulmi hassada. Ko da mutum yana kokarin yin takara da kai kan wasu al'amura na duniya kai kar kayi takara dashi lallai mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa da haka.

Dangane da cewa,''.....kada ku yi cinikin zure .....''kai ne kana da rumfa a kasuwa kana sayar da jakunkuna sai nazo zan sayi jaka muna ciki ciniki kace naira dari biyu ni kuma inacewa naira tamanin kawai sai wani dan kore yazo ya dauki irin wannan jakar yace don Allah ka sayar min da wannan jakar dari da hamsin, '' Shi wanda yazo yayi hakan din yayi ne fa don saboda ni yace Dari da hamsin ka sayar ? yace 'aa' to dari da sittin da biyar wai dole sai ya zurma ni na shiga a yi dakyar a sayar masa dari da saba'in bayan kuwa ciniki ne na bogi na karya ba gaskiya bane, don kawai ni in kai dari da saba'in, farashinta kuwa naira tamanin towannan shi ne kore, kuma duk malamai sunyi ittifakin haramcinsa dangane da yiwuwar cinikin kuwa, wadansu suka ce yayiwu wadansu kuma suka ce bai yiwu ba sai dai mafi ingancin magana, cinikin ya yiwu don shi wanda yazo wanna tayi ai ba da shi muka yi ciniki ba wannan shi ne abin da imamu Malik Bin Anas yace. Amma idan daga baya ka gane cewa wancan dan kore ne to kana da dama ka fiot ka mayar kace baka so a baka kudinka kuma dole ne a baka. In kuma ka ce shi kenan kai ka hakura kana son abin haka, ba komai ya halatta.

Abu na uku Annabi yace, kada ku zamanto masu kiyayya da juna kaje kana fushi da wani shi ma yana fushi da kai, wannan ma ba'a so abin fushi idan ya faru, to ayi hakuri a rarrashi zuiciya s ta hakura da manzon Allah yace kada ku juya wa juna bayanku yana nufin kar ku kaurace wa junanaku, ku yanke mu'amala da juna in dai an fara mu'amala kar ayanke ta a ci gaba sai in an riga an cuce ka ne to idan akazo za sake zaunawa sai kace aa ai rannan ka cuce ni ba zan yarda ba. Sallah dai muyi tare, da Azumi komai ma muyi tare sai kuma Manzon Allah yace kada sashenku yayi ciniki acikin dan uwansa abin nufi idan mu biyu muna da haja ta kasuwani da muke sayarwa idan kwastoma ya shigo rumfata muna tsaye munacinikayya na sa masa suna yana tayi, to bai halatta ba kazo ka juye kwastoma nan kace, zo mana in sayar maka kasa da yadda ya baka. Bangare na biyu idan ni saye nake a wani wuri, nazo ina sayen kaya, an sami suna ina yin tayi bai halatta ba wani shi ma ya shigo yace shi ma zai sayi wannan kayan sai har ni na bari ba'a daidaita ba Daga kashe manzon Allah yace, ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna musulmi dan uwam musulmi ne kada ya zalunce shi kada yayi masa karya kada ya kunyatar dashi ko kaki taimakonsa in ya nemi taimakon ka ka taimaka masa, kada ka wulakantar da shi wai don talaka ne ka bashi matsayinsa da ya dace dashi Aisha (R.A) tana cewa an umarce mu sauke kowanne mutum a matsayinsa. Manzon Allah ya karasa cewa '' ya ishi mutum sharrin ya rinka tozarta da dan uwanka musulmi don talaucinsa ko don karamin ma'aikaci ne ko don dan makaranta ne kauda nba ko komai bane.

Snnan sai yace,''.....Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne a kan musulmi.'' ma'ana, kowne musulmi game da musulmi dan uwansa, haramunne ya zubar da jininsa, ko ya cinye dukiyarsa, ko ya zubar da mutuncinsa. Shi ne, ko ka zge shi ko ka la'anceshi ko ka jefe shi da laifin da bai yi ba ka yi gini bisa ga zato haka kawai. To wannan duk dai bai haltta ba.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA'AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 04:51:05 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: