Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12

ME YA FARU A KARBALA? 12 Wa ya kashe sayyidina HUSAINI?

Bayan duk bayanin da ya gabata na abinda ya faru, muna son amsa wannan tambaya. WA YA KASHE SAYYIDINA HUSAINI? Amma a wannan karon littafan Shi'ah kadai muke son su bada amsa.

1. Ga abinda Allamah As Sayyid Muhsin Al Amin ya fada a cikin A'yanus Shi'ah (1/34):

ﺑﺎﻳﻊ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺃﻟﻔﺎ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ، ﻏﺪﺭﻭﺍ ﺑﻪ ﻭﺧﺮﺟﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺑﻴﻌﺘﻪ ﻓﻲ ﺃﻋﻨﺎﻗﻬﻢ ﻭﻗﺘﻠﻮﻩ '''Mutane 20,000 daga 'yan Iraqi sun yi ma Husaini mubaya'a, sun YAUDARE shi kuma suka fito a kansa, alhali mubaya'arsa na ga wuyansu, kuma suka kashe shi''.

2. Ga kuma abinda Hurru bin Yazid – daya daga cikin 'yan rakiyar Husain -ya ce ma rundunar da take kokarin kashe HUSAINI a Karbala:

ﺍﺩﻋﻮﺗﻢ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ، ﺣﺘﻰ ﺍﺫﺍ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﺍﺳﻠﻤﺘﻤﻮﻩ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺗﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﻟﺘﻘﺘﻠﻮﻩ، ﻓﺼﺎﺭ ﻛﺎﻻﺳﻴﺮ ﻓﻲ ﺃﻳﺪﻳﻜﻢ؟ ﻻ ﺳﻘﺎﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻈﻤﺎ .


''Yanzu zaku kira wannan bawan Allah na kirki, sai da ya zo maku sannan ku mika shi, Sannan ku yi tsalle a kansa don ku kashe shi, har ya zama kamar wani fursuna a hannunku?! Kada Allah ya shayar da ku ranar kishirwa''. Duba AL IRSHAD na Al Mufid, shafi na 234 da I'LAMUL WARA BI A'LAMIL HUDA na Tabarsi, shafi na 242.

3. Sai kuma abinda Tabrasi ya hikaito cewa shi kansa sayyidina Husaini yana cewa:

'' ﺃﻟﻢ ﺗﻜﺘﺒﻮﺍ ﺇﻟﻲ ﺃﻥ ﻗﺪ ﺃﻳﻨﻌﺖ ﺍﻟﺜﻤﺎﺭ ، ﻭ ﺃﻧﻤﺎ ﺗﻘﺪﻡ ﻋﻠﻰ ﺟﻨﺪ ﻣﺠﻨﺪﺓ؟ ﺗﺒﺎً ﻟﻜﻢ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﺣﻴﻦ ﺍﺳﺘﺼﺮﺧﺘﻤﻮﻧﺎ ﻭﺍﻟﻬﻴﻦ ، ﻓﺸﺤﺬﺗﻢ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺳﻴﻔﺎً ﻛﺎﻥ ﺑﺄﻳﺪﻳﻨﺎ ، ﻭﺣﺸﺸﺘﻢ ﻧﺎﺭﺍً ﺃﺿﺮﻣﻨﺎﻫﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﺪﻭﻛﻢ ﻭﻋﺪﻭﻧﺎ ، ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺃﻟﺒﺎً ﻋﻠﻰ ﺃﻭﻟﻴﺎﺋﻜﻢ ﻭ ﺳﺤﻘﺎً ، ﻭ ﻳﺪﺍً ﻋﻠﻰ ﺃﻋﺪﺍﺋﻜﻢ . ﺍﺳﺘﺴﺮﻋﺘﻢ ﺇﻟﻰ ﺑﻴﻌﺘﻨﺎ ﻛﻄﻴﺮﺓ ﺍﻟﺬﺑﺎﺏ ، ﻭ ﺗﻬﺎﻓﺘﻢ ﺇﻟﻴﻨﺎ ﻛﺘﻬﺎﻓﺖ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ﺛﻢ ﻧﻘﻀﺘﻤﻮﻫﺎ ﺳﻔﻬﺎً ، ﺑﻌﺪﺍً ﻟﻄﻮﺍﻏﻴﺖ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻣﺔ ''
''Wai kam ba ku ne kuka rubuto mana cewa, 'ya'yan itace sun nuna ba, kawai zamu zo mu sami hadaddiyar runduna? Allah ya abkar da halaka a gare ku ya ku wannan taron wofi!

Tunda kun kwala mana kira a haukace, sannan kuka daga mana takobin da muke ganin a hannunmu yake (Zaku kashe mu da shi), Sannan kuka hura wutar da mun hasa ta ne don makiyanmu kuma makiyanku. A yanzu kun zama masu fada da masoyanku, masu hada kai da makiyanku. Kaico! A Lokacin da kuke bamu mubaya'a kun yo sulu kamar fari amma a yanzu kun kakkabe hannayenku kamar ba ku ne ba. Kai, Allah dai ya nisantar da ku ya ku dawagitan wannan al'umma'' Duba I'LAMUL WARA na Tabarsi, shafi na 949.

4. A nan ne kuma – in ji Mufid – sayyidina Husaini ya yi masu bakar addu'a yana cewa:

''ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻣﺘﻌﺘﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﺣﻴﻦ ﻓﻔﺮﻗﻬﻢ ﻓﺮﻗﺎً ﻭﺍﺟﻌﻠﻬﻢ ﻃﺮﺍﺋﻖ ﻗﺪﺩﺍ ، ﻭ ﻻ ﺗﺮﺽ ﺍﻟﻮﻻﺓ ﻋﻨﻬﻢ ﺃﺑﺪﺍ ، ﻓﺈﻧﻬﻢ ﺩﻋﻮﻧﺎ ﻟﻴﻨﺼﺮﻭﻧﺎ ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺍ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻘﺘﻠﻮﻧﺎ ''
''Ya Allah! In har ka tsawaita rayuwarsu to, ka tarwatsa su, ka hahhargitsa su, kada ka bari su ji dadin mai mulki ko wane ne sam. Hakika sun kira mu da sunan taimakonmu amma sai suka zabura a kanmu zasu kashe mu''. Duba AL'IRSHAD na Al Mufid, shafi na 241 da Kashful Gummah na Arbili (2/18 da kuma 2/38).

5. Al Ya'qubi a cikin Tarihinsa (1/235) shi kuma cewa ya yi, Zainul Abidin dan sayyidina HUSAINI wanda Allah ya kaddari ya kubuta ba a kashe shi ba a Karbala shi ma ya jingina kisan Husaini da iyalansa ga 'yan Shi'ah, mutanen Kufa duk kuwa da kukan munafurci da ya tarar suna yi. Ga maganarsa nan da nassinta:

ﻟﻤﺎ ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺍﻟﻜﻮﻓﺔ ﺭﺃﻯ ﻧﺴﺎﺀﻫﺎ ﻳﺒﻜﻴﻦ ﻭﻳﺼﺮﺧﻦ ﻓﻘﺎﻝ '' : ﻫﺆﻻﺀ ﻳﺒﻜﻴﻦ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻤﻦ ﻗﺘﻠﻨﺎ ؟ ''
''A lokacin da Ali bin Al Husain ya shiga Kufa – yana nufin bayan rikicin Karbala – sai ya tarar da matan garin na ta kuka da hargowa, sai ya ce, ''Af! Dubi wadannan wai mu suke wa kuka. To, wa ya kashe mu ne?

Zamu takaita a haka, sai gobe mu garzaya birnin Sham wurin Yazidu mu ji abinda yake faruwa a can. Amma muna son mu jefa tambaya ga masu adalci: Don girman Allah, wa ya kashe sayyidina HUSAINI?
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:24:36 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 12" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: