Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
[ Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi ]

·Muhimman sharuddan da ya kamata a lura da su kafin a kafirta wani
·Wani abu kan Sallar Idi
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (5)
·Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji (4)
·Sallar Idi da ladubbanta
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
·Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
·Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
·Babu Masu Kashe Masu Jefa Kuri'a A Ranar Zabe Sai Azzalumai

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13

ME YA FARU A KARBALA? 13 Labarin Kisan Husaini Ya Game Duniya Da sauri kuma ba da bata lokaci ba wannan mugun labari ya game duniya. Ana mamaki ya aka yi musulmi mai neman ceton Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya iya kashe jikansa, farin cikin rayuwarsa?! Wannan labari ya mantar da musulmi sauran musibu da fitinun da suka gabata. Daman an ce, ba a jin warin bera in ana babbakar giwa.

A hedikwatar halifanci Sham, Yazidu ya samu wannan labari mai ban mamaki. Sai dai kamar yadda muka fadi a baya, ruwayoyi sun sha banban game da irin tarbon da Yazidu ya yi ma wannan labari.

Riwayoyi mafi kusa da gaskiya sune wadanda suka ce, Yazidu ya firgita da jin wannan labari, ya yi taslima.

Sannan ya yi rantsuwa shi bai ce a kashe Husaini ba, kuma bai ji dadin kisan ba. Ya la'anci gwamnansa Ubaidullahi, ya ce bai kiyaye alfarmar Manzon Allah ba.

Wannan magana ba a cikin littattafan Sunnah kawai ba har a cikin na Shi'ah akwai ta. Misali, a cikin KITABUL IHTIJAJ na Tabarsi cewa ya yi:

A lokacin da aka zo da Ali bin Al Husain wajen Yazid ya ce ma sa, na samu labarin cewa zaka kashe ni. Idan har haka ne, ina son wadannan 'yan mata (yana nufin kannensa da aka zo da su) ka nemi wanda zai kai su Madina. Sai Yazidu ya ce masa, ai ba wanda zai kai su in ba kai ba. Allah ya la'anci Ibnu Murjanah – Ubaidullahi bin Ziyad kenan – wallahi ban sa shi kashe babanka ba.

Kuma da ni ne a wurin wallahi ba zan kashe shi ba. Sannan ya yi masa kyauta mai yawa, ya mutunta shi, ya hada shi da 'yan rakiya tare da sauran matan suka wuce Madina.

Kisan Husaini ya yi kama da kisan Zubair bin Al Awwam Dan gwaggon Manzon Allah Safiyyah bint Abdil Muttalib wanda ya kasance tare da su Nana Aisha a cikin yakin rakumi. Yakin da makasan sayyidina Usman, wadanda suka yi masa juyin mulki suka hasa wutarsa tsakanin sarkin musulmi Ali da talakawansa da suka fito don daukar fansar Usman. Yaki ya koma ba ji ba gani tsakanin 'yan uwa – Su Zubairu, Dalha da Aisha a daya bangare, da kuma Ali, Ammar bin Yasir da sauransu a bangare daya. Da Ibnu Jarmuz ya kashe Zubair sai ya zo yana murna da bushara ga sayyidina Ali. Sai Ali Radiyallahu Anhu ya ce masa: Tabbas na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana cewa: ''Ka yi bushara ga wanda zai kashe Dan Safiyyah da shiga wuta''. Duba BIHARUL ANWAR (32/336).

Babu shakka tambaya ta farko da mutum zai yi a nan ita ce, to in haka ne don me da Yazid bai yi wa Ubaidullahi hukunci ba?.

Alal akalla ai ya kamata ya cire shi daga gwamna. Haka ne.

Amma dai wannan mas'ala ce ta siyasa. Ai ka ga ko sayyidina Ali ba wani hukuncin da ya yi wa Ibnu Jarmuz wanda ya kashe Zubair. Daga karshe ma shi Ibnu Jarmuz na cikin wadanda suka yi ma Alin tawaye har suka yi yunkurin kashe shi, kai ma suka kashe shi din.

Dalilin kasancewar lamarin na siyasa shi ne, duban yanayin Kufa ita kanta da yake babu salihin mutum da ke iya zama gwamna a garin.

Sahabbai da dama suka sa aka dauke masu har da wanda suka tuhumta da rashin iya sallah, alhalin tun zamanin Manzon Allah yake gwamna! Don haka, a zamanin daular Bani Umayyah zaka ga duk wani fasikin gwamna maras imani – irin su Hajjaj – a can ne aka tura shi. Na tattauna wannan matsala a mukalar da aka buga a fitowa ta 3 ta mujallar Degel, June 2000 (FAIS, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto) mai taken ''The Umayyad Dynasty Between Facts and Fiction: A Study of the Genesis of the Dynasty and Critical Analysis of it's Historical Sources''.

Husaini dai ba shi kadai Allah ya azurta da shahada ba a Karbala.

Akwai da dama daga cikin 'yan uwansa da ya fito da su wadanda suka hada da kannensa Ja'afar da Abbas da Muhammad da Abubakar da Umar da Usman duk 'ya'yan sayyidina Ali. Akwai kuma 'ya'yan wansa Al Hasan: Abdullahi da Qasim da Abubakar. Sai 'ya'yansa shi kansa Husaini: Ali babba da Abdullahi. Karamin dansa kam Ali Zainul Abidin – Wanda ake ma lakabi da Abubakar – bai samu wannan daraja da danginsa suka samu ba, saboda ba shi da lafiya a wannan rana, don haka bai yi yaki ba, su kuma arnan ba su taba shi ba. Mun bada cikakken tarihinsa a cikin littafin MAI RABON GANIN BADI: ALI ZAINUL ABIDIN, wanda aka buga a shekara 2004.

Daga cikin wadanda Allah ya karrama da shahada a tare da Husaini har wayau akwai 'ya'yan baffansa Akilu. Su ne, Ja'far da Abdullahi da Abdurrahman. Sai kuma Muhammad bin Muslim wanda aka kashe mahaifinsa tun kafin isowar Husaini. Daga cikin 'ya'yan Abdullahi bin Ja'far kuwa akwai Aunu da Abdullahi. In ka hada da Husaini mutane 18 kenan dukansu 'yan gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Wannan kuma shi ya sa musibar ta kara tsananta a kan musulmi.

Amma ko me ya sa su 'yan Shi'ah suke maganar Husaini, suna makokinsa shi kadai, ba sa ko nuni da sunayen sauran abokan shahadarsa? Wannan su ya kamata su bada amsa da kansu.

A gaba zamu yi maganar abinda ya biyo bayan wannan fitina, sannan mu yi sharhi a kan matsayinmu game da Yazidu da hukuncin la'antarsa.

Allah ya yi mana kariya daga fitinu na zahiri da na boye.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:25:37 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 13" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: