Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16
 
 
Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi DR MANSUR SOKOTO

MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16

MEYA FARU A KARBALA? 16 Matsayin Malaman Sunnah a kan Wadannan Fitinu Game da tawayen mutanen Madina malamai magada Annabawa ba su ja bakinsu ba suka yi shiru.

Sun bayyana ma mutane abinda Allah ya wajabta na da'ar shugaba ko da fasiki ne.

Maslahar da ke cikin wannan ita ce, kauce ma abinda zai zubar da jinainan jama'a da kawo tashin hankalin da ba a san karshe ko iyakarsa ba. Littafan Sunnah na hadisi da na Akida a cike suke da wadannan hadisan. Sheikh Abdus Salam Bin Barjis ya tattara su tare da maganganun magabata a cikin littafinsa MU'AMALATUL HUKKAM FI DAU'IL KITAB WAS SUNNAH, bugun Riyadh 1415H.

Misalai biyu kawai zamu kawo don bayyana matsayin malaman Sunnah a wancan lokaci.

1. Matsayin Abdullahi bin Umar:

Kamar yadda muka gani a baya, Abdullahi bin Umar Radiyallahu Anhuma na daga cikin wadanda ba su yi na'am da nadin Yazidu ba.

Amma da ya ga jama'a sun yi masa mubaya'a sai ya kyamaci ya ware daga mutane. To, a lokacin da wannan fitinar ta taso ta yin tawaye ga Yazid, Ibnu Umar ya tara dukkan iyalansa ya gargade su game da sa hannu cikin abinda ke gudana. Ya ce musu, ku sani mun bada mubaya'armu ga wannan mutum ne bisa ga amincin Allah da sunnar Manzonsa. Kuma na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana cewa:

''Duk wanda ya yi yaudara za a kafa masa tuta a ranar alkiyama ace ga yaudarar da wane ya yi. Babu kuwa wata yaudara – in dai ba shirka ce ba – da ta kai kwance mubaya'ar da aka yi bisa ga Sunnah. Don haka kada ku yi ma Yazid tawaye.

Kada dayanku ya sanya hannunsa cikin wannan tashin hankali. Wanda kuwa duk ya yi haka zai zama rabuwata da shi kenan. Duba Sharhin Sahihu Muslim tare da sharhin Imam An Nawawi, Hadisi na 58 da na 1851 (2/1478).

Sayyidina Ibnu Umar bai tsaya kawai ga gargadin iyalinsa ba sai da ya je wajen jagoran wannan yunkuri Abdullahi bin Muti'u.

Abdullahi ya yi wuf ya dauko masa majingini, sai Ibnu Umar ya ce masa dakata. Ni ban zo don in zauna ba. Na zo ne in sanar da kai wani Hadisi da na ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.

Na ji shi yana cewa:

''Duk wanda ya zare hannunsa daga biyayya (ga shugaba) zai gamu da Allah ba ya da hujja.

Wanda kuwa duk ya mutu yana mai rabuwa da jama'ar musulmi to, zai yi mutuwa irin ta jahiliyyah''. Duba Sahihu Muslim a wurin da muka fadi a dazu.

2. Matsayin Muhammad Bin Ali Bin Abi Talib A cikin yawon da suka yi na neman goyon bayan jama'a, wadanda suka shirya tawayen a Madina sun je wurin kanen Husaini; Muhammad Wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah. Muhammad ya tambaye su, mene ne dalilinku na yi wa Yazidu tawaye? Sai jagoransu Abdullahi bin Muti'u ya kada baki ya ce masa, saboda Yazidu na shan giya, kuma ba ya sallah, sannan yana tsallake hukuncin Alkur'ani. Muhammad ya ce masu, to amma ni na je wajen Yazid ban ga abinda kuka fadi ba. Na zauna tare da shi na wani lokaci, na lura da yana tsayar da sallah, yana kamanta yin alheri, yana tambayar ilimi kuma yana lazimtar Sunnah. Sai suka ce, ai zai iya yin haka don riya!

Ibnul Hanafiyyah ya ce, to me yake so a gurina ko yake tsoro da zai mani riyar abinda bai saba ba? Ya sha giyar ne a gabanku? In dai har kun ga ya sha giya, to tare kuka sha kenan. In ba haka ba to bai halalta ku shedi abinda ba ku gani ba. Sai suka ce, ba mu gani ba kam amma wallahi mun yarda da wannan magana, kuma tabbas gaskiya ce. Sai ya ce, to, Allah Ta'ala ya soke wannan shaida taku, don cewa ya yi:

( ﺍﻻ ﻣﻦ ﺷﻬﺪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ :

٨٦ ''Face wadanda suka yi shaida da gaskiya, kuma suna sane (da abinda suka yi shaida a kansa). Suratuz Zukhruf: 86 Da Ibnul Hanafiyyah ya tabbata masu ba shi tare da su, sai suka ce kamar dai kana ganin kai ka fi cancanta mu sa gaba! Sai ya ce, sam. Ba na halalta ma kaina yin wannan al'amari a kowane matsayi, ina jagora ko ina mabiyi.

Suka ce, to, amma ai ka yi yaki tare da babanka.

Ya ce, ku kawo min wani irinsa in taya shi yaki.

Suka ce, to ka sa 'ya'yanka Al Qasim da Abul Qasim su biyo mu.

Ya ce, in har zan sa 'ya'yana me zai hana ni ma in je?

Suka ce, to ka zo mu je ba sai ka yi yaki ba.

Iyaka kawai ka yi mana kamfe ga mutane. Ya ce, tsarki ya tabbatar ma Allah! In ce mutane su yi abinda ba na yi?

Suka ce, to lalle ko kana so ko ba ka so sai mun fitar da kai ka shiga cikin wannan lamari. Ya ce, ba zai maku dadi ba don zan rinka ce ma mutane su ji tsoron Allah, kada su yardar da wani mahaluki a cikin fushin ubangiji. Daga karshe dai Muhammad ya fice ya bar Madina zuwa Makka don gudun wannan fitina. Duba AL BIDAYA WAN NIHAYA na Ibnu Kathir (8/604)
da kuma MUKHTASAR TARIKH DIMASH na Ibnu Manzhoor (8/256).

Zamu dawo magana kan Yazid in Allah ya so.

Ku dakace mu.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:29:18 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi:
Son Maso Wani Koshin Yunwa!: Gidan Annabi Mohammad (SAW)


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Tarihi Addinin Musulunci Da Kissoshi

"MEYA FARU A KARBALA? ME YA FARU A KARBALA? 16" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: