Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#
 
 
Al'Adun Musulmi Da Darajoji DR MANSUR SOKOTO

AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH''?

Bismillahir Rahmanir Rahim Abinda muka sani ne cewa, daga cikin manyan ginshikan Shi'a da suka dogara gare su kuma suka gina akidarsu a kai shi ne, cewa Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi wasici da abi Alkurani da ''ITRA'' wato iyalan gidansa. Sa'annan kuma sai suka dauka cewa, bin jikokin sayyidina Husaini shi ake nufi domin su ne magadan ilimin annabta. (mutum tara ne daga cikin zuri'ar Husaini suka sa a cikin imamansu goma sha biyu amma babu na Hasan ko guda!). A kan wannan fahimta tasu sun hakikance cewa an saba ma umurnin Manzon Allah tun da farko, don haka tafiya ta gurbace tun daga asalinta, musulmin farko – almajiran Annabi da masu bi masu – duk sun bar tafarkin shiriya, a fahimtar 'yan Shi'ah.

Muna so mu tattauna a tsanake dangane da wannan Hadisi da ruwayoyinsa, domin mu gano ingancinsa ko rashin haka. Sannan mu yi tsokaci game da ma'anarsa wadda ta yi daidai da abinda aka sani na koyarwar ma'aiki Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam.

Kafin mu shiga wannan bayani, zai yi kyau muyi nuni ga matsalar da take shiga a cikin rubuce-rubucen malaman Shi'a idan suka zo magana a kan hadisai. Wannan bayani a hakikaninsa na masanan Hadisi ne, yana yiwuwa ya dan yi nauyi ga wasu daga cikin masu karatu.

Amma na ga ya zama dole ne a matsayin shimfida ga wannan bayani da muke son yi.

Da farko dai malaman Shi'ah sukan zo su dauko hadisai nagartattu ingantattu wadanda a duniyar Sunnah an gama sallama masu, an amince da su. Amma sai su ba wadannan hadisai wata ma'ana wadda ta yi daidai da tasu fahimta. Kamar wasu hadisai da ke nuna falalar sayyidina Ali da darajojinsa. Ba ma musun hadisan, kuma ba ma rage ma sayyidina Ali girmansa, amma su sai su ce wadannan hadisan hujja ne a kan an zalunce shi tunda ba a ba shi halifanci ba tun da farko. Sai su manta – ko su yi gangancin mantawa – cewa, halifofi na gaba da shi su ma suna da irin nasu darajoji.

Kashi na biyu shi ne hadisan da suke masu rauni ne a wurin ma'abota ilimi, an bayyana illolin da ke tattare da su, sai su dauko wadannan hadisan su rinka hujja da su a kan mu, suna cewa to, ga su nan ma daga littafanku! Idan aka yi sa'a hadisin mashahuri ne da ake iya samu a littafai da yawa sai su yi ta cika takarda da sunayen wadanda suka kawo shi. Wanda bai sani ba bai iya gane cewa magana guda ce ake maimaitawa, kuma Hadisin daga mafita guda yake. A wurin malaman Sunnah kuwa Hadisi ba ya zama hujja sai an ruwaito shi ta hanya gangariya wadda babu sofane a cikin maruwaitanta, kuma an samu saduwar su dukansu da juna, sannan ba a samu wata tangarda da ke iya kawo suka abar dubawa ba ga ita kanta hanyar ko abinda shi Hadisin ya kunsa. Irin wadannan hadisan zaka tarar da malaman Sunnah da suka kawo su sun fade su ne don bayyana aibinsu, amma sai su kuma wadannan su cire maganar wannan aibi su ce, to gasu nan a cikin littafanku muka dauko su. Wannan kuwa wani nau'i ne na boye ilimi daidai yadda Yahudawa suka so su yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam – ganin bai iya karatu ba – sai Allah ya ba shi ikon da ya ce, to ku dage yatsanku daga nan ku karanta mana sauran.

Sai ga su sun yi tsuru tsuru! Hadisin da ya ce ''Ni ne birnin ilimi, Ali ne kofarsa'' ya shahara kwarai, ga kuma yawan hanyoyi, amma da an bi su za a gan su wayau, don ba nagartacciyar hanya guda daya da aka samo shi da ita.

A wata sa'ar kuma malaman Shi'ah sukan tsallake littafan hadisi da aka sani gaba daya su dauko wani labari ko wata almara daga littafan mawaka ko na tarihi ko na adabi ko ma wani mawallafi kawai da yake wallafa tatsuniya. Misali irin su SUBHUL A'SHA na Qalqashandi ko AL AGANI na Abul Faraj Al Asfahani ko littafan Ahmad Shauqi ko na Abbas Mahmud Al Aqqad. Idan aka kawo hadisan irin wadannan littafan wani lokaci a fadi littafin, wani lokaci kuma a ce RAWAHUL BUKHARI!!!

Akwai kuma littafan da aka rubuta da sunan Sunnah amma a hakikanin gaskiya mawallafansu 'yan Shi'ah ne. Kamar su Ibnu Abil Hadid da Ibnus Sabbag da Qanduri da makamantansu wadanda masana sun dade da tantance labarinsu.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:31:24 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Al'Adun Musulmi Da Darajoji
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Al'Adun Musulmi Da Darajoji:
Sahabban Manzon Allah (SAW) Kamar Yadda Hadisai Suka Bayyana Su


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Al'Adun Musulmi Da Darajoji

"AL KITABU WAL ''ITRA'' KO AL KITABU WAS ''SUNNAH&#" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: