Hause
- Gaban Shafin    - Samiya Goma    - Batutuwa    - Takardun Labari    - Cagiya Hausa    - Muhawara Hausa    - Ƙungiyar Hausa    - Yakan Yi Bitar    - Saƙonninku Na Sirri    - Bincike    - Mujallan    - Ma\'ajiyar Takardu    - Ciki    - Shafin Yanar Gizo    - Saukewa    - Tambayoyi Masu Yawa    - Shawarce Mu    - Ajiye Bayanai   

 

 
MARABA DA WATAN RAMADAN [12]
 
 
Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen FALALAR CIYAR DA MAI AZUMI !!!

MARABA DA WATAN RAMADAN [12]

Haqiqa ayoyin alqur'ani mai girma sun zo da kwadaitar da Musulmi akan ciyarwa saboda ALLAH a lokacin Azumi da lokacin da bana Azumi ba, da taimakawa matalauta da mabuqata domin yaqar talauci a tsakanin al'ummar musulmai, kuma yin haka na qara tabbatar da 'yan uwantakar musulunci a tsakanin musulmai.

Daga cikin wadannan ayoyi akwai fadar ALLAH (SWT) cewa:

"wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana , 6oye da bayyane, suna da sakamakon lada a wurin Ubangijinsu kuma basu tare da kowane irin tsoro ko baqin ciki (a ranar alqiyama) (Surah ta 2 aya ta 274)
"(Ku ciyar) daga Abunda muka fitar muku na (tsirrai) daga qasa, kada ku nufi maras kyau acikinsa kuna ciyar dashi, alhali ku baku kar6arsa, sai in (kun daure) kun runtse ido, ku sani ALLAH (SWT)
mawadaci ne ga abinda duk zaku ciyar kuma wanda ya cancanci yabo ne acikin ko wani hali" .

(Surah ta 2 aya ta 267)
"Ba zaku samu cikakkiyar lada, har sai kun ciyar da abunda kuke so, abunda duk kuka ciyar na alkhayri, to ALLAH Masani ne game dashi" .

(Surah ta 3 aya ta 92)
"Misalin masu ciyar da dukiyoyinsu saboda ALLAH, kamar qwayar hatsi ce wadda ta fitar da zangarniya bakwai, acikin kowace zangarniya akwai qwaya dari, kuma ALLAH yana lullunkawa ga wanda yaso, ALLAH Mayalwaci ne, kuma mai sani akan duk abunda kuka ciyar" .

(Surah ta 2 aya ta 261)
Wadannan ayoyi duk suna nuni akan falalar ciyarwa saboda ALLAH acikin dukkan yanayi da lokuta. Ciyarwa saboda ALLAH bata ke6anta ga wani lokaci ba, sai dai ciyarwa a wannan mafificiyar watan yafi falala.

Kamar yadda ayoyi suka gabata suna kwadaitarwa akan ciyarwa a lokacin azumi da lokacin da bana azumi ba. Haka ma Hadithan Manzon ALLAH (SAW) sunzo da yawa suna kwadaitarwa akan haka, daga cikinsu akwai wadanda suka zo akan siffar ciyarwa gaba daya, akwai kuma wadanda suka ke6anta ga watan Ramadan kawai, wanda shine muke magana a halin yanzu.

Manzon ALLAH (SAW)
Yace:" Duk wanda ya ciyar da mai azumi ga budin baki, yana da kwatankwacin ladarsa, ba tare da an tauye wani abu ba daga ladar mai Azumin ba" .

(Ahmad 4/114, Tirmizi, Ibn Majah 1746)
•WASU DAGA CIKIN ADDU'O'IN WANDA AKA CIYAR GA WANDA YA CIYAR DASHI !!!

Yana da kyau ga wanda aka ciyar yayi Addu'a ga wanda ya ciyar dashi bayan qare cin abincin, kamar yadda yazo daga Manzon ALLAH (SAW)
Addu'o'in suna da yawa amma ga kadan daga ciki:

"ﺃﻓﻄﺮ ﻋﻨﺪﻛﻢ ﺍﻟﺼﺎﺋﻤﻮﻥ ﻭﺃﻛﻞ ﻃﻌﻤﻜﻢ ﺍﻷﺑﺮﺍﺭ ﻭ ﺻﻠﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ " .


Ma'ana: "ALLAH Yasa masu azumi sunyi buda baki a wajenku, kuma ALLAH Yasa nagartattun bayi sunci abincinku, kuma ALLAH yasa Mala'iku sunyi muku addu'a" .

(Abu-dawud 3/367 da Ibn Majah 1/556, da Nasa'i a cikin Amalul Yaum wal Laila Hadith na 296-298. Albani ya inganta shi acikin Sahih Abu-dawud 2/730.

"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻃﻌﻢ ﻣﻦ ﺃﻃﻌﻤﻨﻲ ﻭﺳﻖ ﻣﻦ ﺳﻘﺎﻧﻲ" .


Ma'ana: "Ya ALLAH! ka ciyar da wanda ya ciyar dani, ka shayar da wanda ya shayar dani" .

(Muslim 3/1626)
" ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻬﻢ ﻓﻴﻤﺎ ﺭﺯﻗﺘﻬﻢ ﻭﻏﻔﺮ ﻟﻬﻢ ﻭﺭﺣﻤﻬﻢ " .

Ma'ana: "Ya ALLAH! Ka albarkace su acikin abunda ka azurta su dashi, kuma ka gafarta musu, kaji qansu" .

(Muslim 3/1615).

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Yace: "Aiki wanda yafi falala shine ka shigar da murna acikin (zuciyar) dan uwanka mumini ko ka biya masa bashi ko kaciyar dashi " .

(Silsilatus sahiha 1494)
• A LURA CEWA:

Annabi (sallallahu alaihi wasallam) Yace: "kada ku ciyar da talakawa daga abunda Ku Baku cinsa" .

(Sisilatus sahiha 2426)
Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Yace: "lallai Bawa ya ta6e kuma yayi hasara idan ALLAH (SWT) bai saka masa tausayin yan Adam acikin zuciyarsa ba" .

(Silsilatus sahiha 456)
YA ALLAH DUK WANDA YA TAIMAKI WANI YA ALLAH KA TAIMAKE SHI KA SANYA LADARSA TA ZAMA SANADIN SHIGARSA ALJANNAH.

ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU (Ameen)
-Faridah Bintu Salis.

(Bintus-sunnah)
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:44:42 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen:
Sako daga marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa


Mataki Na Rating

Average Score: 0
Kurioi: 0

Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Kacici-ka-cicin Addini, Hukunce-hukuncen

"MARABA DA WATAN RAMADAN [12]" | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: