Shiga
  Create an account
Gidan Ku
Yi Fita
 
 
 
Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


Babban Labari Yau

Babu Wani Babban Ma Labari A Nan Ka A Yanzu, Domin Ba Su Yi Rajista Ko Da Ya Zama Dan Maabuci Ba Tukuna. Shiga Yanzu!.

Mahadin Kafada Kissoshin


Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai
[ Labari, Da Kayayyakin Aiki Kanun Labarai ]

·Siyasa da matsayin malamai a Musulunci (1)
·Matsayin sada zumunta a Musulunci
·Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
·Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
·Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
·Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
·Adabin Gargajiya
·Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
·Matsara Wasu Yan Bidi'ah Da Wasu Kafurai Ta Yi Matukar Kama Game Da Khawaar

Wa Ya Ke A Dandali

Wannan Lokaci, Akwai A Wani Hali Da Kanka 2 Bako, Ko Baki, Da 3 Dan (Yan), Wadanda Suka Hada da 'Yan awqaf. Ga Da Sauran Kasashe Membobin (Yan), A Kan Wani Hali Da Danna Here

Ba Kuka Je Maabuci. Ka Iya Diwani Kyauta Da Matsarka Da Nan

Cagiya
Luggogi

Tsina Sarke Harshe:


Babobi Kafa Hanya


Iya Yin

Lakani

Muku Magana

Ba Ni Da Lissafin Duk Da Haka? Ka iya Halitce A. Kamar Yadda Suka Yi Rajista Maabuci Akwai Wakansu A Cikinku Amfania Fagen Siyasa Kamar Taken Manajar Lafiyata, Da Tungume Kafa Lafiyata Gidan Da Sunanka.

Da Makalolin

Monday, September 09
· Kwadaitarwa kan yin azumi a cikin watan Sha'aban
· Mu rika nuna juriya da hakuri kan jarrabawar da ke samunmu
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla (2)
· Hukuncin daga hannu sama a yi addu'a bayan an gama sallar farilla
· Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya (3)
· Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (4)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (3)
· Duk wanda ya gode wa ni'imar Allah zai samu kari (2)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (3)
· Kyauta da kyauta yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)
· Kyauta da kyauta-yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (3)
· Manuniya kan ladubban yin addu'a (2)
Sunday, September 08
· Manuniya kan ladubban yin addu'a
· Matsayi da muhimmancin addu'a ga Musulmi
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (5)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (4)
· Ma'ana da illolin zina da luwadi da madigo da kuma hukuncinsu (3)
· Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
· Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (7)
· Idan za ku fadi magana ku yi adalci
· Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu
· Na rubuta littafin Almajirai Ko Attajirai? ne don ceto yara daga kangin bara da
· Binciken tarihin Hausa: Labaran da bishiyoyin kuka ke sanar mana
· Malam Usman Dan Is'haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakk
· Adabin Gargajiya
· Asalin Hausa (3)
· Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
· Asalin Hausa (2)

Babban Makaloli

Hause

- Gaban Shafin
- Samiya Goma
- Batutuwa
- Takardun Labari
- Cagiya Hausa
- Muhawara Hausa
- Ƙungiyar Hausa
- Yakan Yi Bitar
- Saƙonninku Na Sirri
- Bincike
- Mujallan
- Ma\'ajiyar Takardu
- Ciki
- Shafin Yanar Gizo
- Saukewa
- Tambayoyi Masu Yawa
- Shawarce Mu
- Ajiye Bayanai


TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.
 
 
Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi SHEIKH ABDULWAHHAB ABDULLAH

TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S.A.W)?

Amsa:

Kafin mu amsa wannan tambayar ya na da kyau muyi wa kanmu wadannan tambayoyin:

-Mece ce soyayya?

-Mene ne yake sa a so mutum?

-Mene ne rabe- raben so?

-Mece ce alamar so?

Daga nan kuma sai musan mece ce hakikanin soyayyar Manzon Allah (S.A.W)?

Mece ce soyayya?

Hafiz Ibin hajar babban malamin hadisin nan da yayi sharhin sahihul bukhari yace:

haqiqanin soyayya awajen masana; wata aba ce da ba'a iya bayyanata,mai yinta kawai shi ne ya san yadda yake jinta,amma baya yiwuwa ya furta yadda take.

Mallam ibnul Qayyim yace:

Ba'a bayyana soyayya da wani bayani fiye da ace mata soyayya. Duk abin da za'a bayyana game da ita ba zai kara mata komai ba sai buya,bayaninta kawai shi ne samuwarta, ba kuma a sifantata da wata siffa fiye da soyyya.

Mutane kawai suna yin maganane game da abinda yake jawota,da abinda yake wajabta ta, da alamominta da shaidunta da abinda ake samu idan anyi ta.

Mene ne yake sa aso mutum a dabi'ance?

Akan so mutum a dabi'ance saboda abubuwa masu yawa. Kadan daga ciki sune kamar haka:

– Akan so mutum don yawan kyautatawarsa, -ko don kyawun surarsa wadda take burge mutane, – ko don cikar kamalarsa, -ko baiwar ilmi, ko mulki, ko dukiya, ko wani abu wanda yake burge mutane.

Haka kuma akan so mutum don kyawawan halayensa na gari ko kuma saboda amfanarwarsa ga al'umma.

Manzon Allah (S.A.W) kuwa ya tattare dukkan wadannan sababbai da ninkin-ba- ninkinsu wadanda suke sa a so mutum.

Don haka ya zama wajibi a so shi fiye da kowane irin mahluki.

Tambaya; Menene rabe raben so?

Amsa; Imam ibn bazzar da alkali Iyadh da wasunsu sunce soyayya ta kasu kaso uku:

1)- Soyayya don girmamawa da taimakawa; kamar soyayyar 'ya 'ya ga iyayensu.

2)- soyayyar tausayi da jin kai; kamar soyayyar iyaye ga 'ya'yansu 3- Soyayyar bani in baka; ita ce ke sanya kyautatawa wanda ya kyautata maka; kamar soyayyar da sauran al'umma suke wa junansu.

Idan muka kalli wadannan rabe-rabe da sababbai da suke sa a so mutum zamu ga cewa Manzon Allah (S.A.W)
ya tattare dukkaninsu.

Don haka ibn Bazzar yace:

''wanda yake da cikakken imani ya san Manzon Allah (S.A.W) ya fi girman hakki akansa fiye da hakkin kansa akan kansa, haka zalika hakkin iyayensa da na 'ya'yansa da na mutanen duniya baki daya.

Domin da imani da kaunar Manzon Allah (S.A.W) ne Allah ya tserar da mu daga wuta kuma ya shiryar da mu daga bata.

Mece ce alamar son Manzon Allah (S.A.W)?

Imam alkali Iyadh yace:

''kusani, lallai duk wanda ya so abu dole zai fifita shi akan komai ,kuma zai fifita binsa kwabo da kwabo.

Idan kuwa bai zama haka ba to sonsa ba na gaskiya ba ne,da'awar son kawai yake yi.

Mai son Manzon Allah (S.A.W) da gaske shine wanda alamomin soyayya suke bayyana a gare shi kamar haka:

-Na farkon su shi ne koyi da shi.

-Aiki da sunnar sa.

-Bibiyar zantukansa da aiyukansa.

-Kwatanta umarninsa.

-Nisantar hane- hanensa.

-Ladabtuwa da ladabansa, a halin wahala da yalwa,da nishaxi da damuwa.

Abinda yake karfafa wannan shine fadin Allah (S.W.T):

ma'ana:

ka fada musu ya kai wannan annabi mai girma, idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni sai Allah ya so ku, kuma ya gafarta zunubanku.

lallai Allah mai yawan gafara ne mai yawan jinkai''{al- imrana:31} Wannan ayar ta nuna cewa biyayya ita ce matakin farko na soyayya.

Sannan alkali ya ci gaba da cewa:

Da fifita abin da ya shar'anta ko yakwadaitar da yinsa fiye da son zuciyarka da sha'awarka.saboda fadin Allah s.w.t:

Ma'ana:

''Wadanda suka riki Madina wurin zamansu(al- ansar) da imani kafin su (muhajirun)
suna kaunar wadanda suka yi hijira zuwa garesu, (wato manzon Allah da muhajirun)kuma basa jin wani kyashi a zuciyarsu game da abinda Allah ya bawa (muhajirai na falala da matsayi da daukaka da gabata a cikin Ambato da matsayi), kuma suna fifita su (muhajirai)
akan kansu ko da kuwa suna da matsananciyar bukata.'' Imam addabari da imam assuyidi kuwa sun fassara ayar da cewa:

''Wadanda suka riki madina wurin zamansu(al- ansar) da imani kafin su (muhajirun)
suna kaunar wadanda suka yi hijira zuwa garesu, (wato manzon Allah da muhajirun)kuma basa jin wani kyashi a zuciyarsu game da abinda Manzon Allah (S.A.W) ya bawa (muhajirai da shi na ganima da fai'i)
kuma suna fifita su (muhajirai)
akan kansu ko da kuwa suna da matsananciyar bu tata.'' Sannan alkali iyadh ya ambaci hadisi da isnadinsa zuwa anas bn malik (r.a) yace:

Ma'ana:

ya kai Dan qaramin Dana, idan ka sami iko ka wayi gari ko ka yammata ba tare da wani kulli a zuciyar ka game da wani ba to ka aikata:

wannan yana daga sunnata,wanda ya raya sunnata haqiqa ya soni.wanda ya soni zai kasance tare da ni a cikin aljana.

Sai alqali iyadh yace:wanda ya siffantu da waxannan sifofi da suka gabata to shi ne mai cikakkiyar soyayya ga allah da manzonsa.wanda kuma yasa va musu a xaya daga cikin abubuwan da aka ambata to wannan soyayyarsa tauyayyiya ce,duk da ba za'a kore musu soyayyar gaba daya ba.

Haka dai. yayi ta kawo alamomin da su ke nuna kaunar Manzon Allah (S.A.W) ga wanda ya siffantu da su.

Acikin wannan littafi na sa mai albarka (asshifa). Ya rage wa mai hankali da tunani ya kalle su da idon basira don ya ga a da'awar da yake yita son Manzon A awane aji yake?

Kuma ya yi wa kansa adalci wajen gane cewa anya kuwa ba yaudararsa ake yi ba wajen nuna masa abin da Manzon Allah (S.) bai yi ba a ce masa shi ne qaunar Manzon Allah (a) ? Allah ka bamu ganewa amin.

Wa sallallahu wa sallama ala nabiyina Muhammad wa ala a'lihi wa sahbihi ajma'in'.
 
 
 Posted By Aka Sanya A Tuesday, May 09 @ 05:59:31 PDT Da MediaHausaTeam
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 
 
 
Comments & Debates :-: التعليقات والمحاورات

 
 
For Your Membership Comments And Registered Debates Please, See Below Or Register Here :-: للحصول على تعليقات عضويتك و مناقشات الأعضاء انظر من فضلك أدناه أو سجّل هنا
 
 
:-: Go Home :-: Go Top :-:
 

Wace Alaka

· Fiye Da Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi
· Labari Da MediaHausaTeam


Mai Karanta Labari A Kan Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi:
Bayyanar mata masu neman mata a kasar Hausa


Mataki Na Rating

Average Score: 5
Kurioi: 1


Don Allah Ku Kai Ta Biyu, Da Wannan Mataki Na:

Excellent Very Good Good Regular Bad

Hanyoyin


 Firinta Zumunci Firinta Zumunci


Ya Danganta Kanun Labarai

Janar Kan Labarin Wasu Fasahohi

"TAMBAYOYI DA AMSA, SHEIK ABDULWAHAB ABDULLAH MECE CE ALAMAR SON MANZON ALLAH (S." | Iya Yin/Halitta Lissafin | 0 Lafiyata
Maganar Na Mallakar Takardar Mannawa Ba Ma Da Ke Kula Da Su Natsu.

Lafiyata Wanda Ya Ba Da Yarji Da Kuka Je Ka Diwani
 

 
EsinIslam The Muslim World Portal For Islamics, News, Fatwas, Audios, Videos, Muslim News, Quranic Islamic Articles, Radio, Audio Quran, TV Channels, Fatwa Rulings, Muslim News Newspapers Magazines Headlines Articles Forums Schools, Universities, Colleges, Mosques, Qur'an, Hadith, Sunnah, Fiqh, Prayers, Salat, Fasting Ramadan, Vidoes, Books On EsinIslam.Com And Muxlima.Com

  :-: Go Home :-: Go Top :-: